Leadership Hausa

Buƙatar Samar Da Kariya Ta Musamman Ga Makarantun­mu

-

A ‘yan shekaraun nan, Nijeriya ta ci gaba da fuskantar abubuwa marasa daxi na tashin hankali na hare-hare a makarantun­mu, makarantu da ya kamata su kasance wuri na samar da matasan da za su zama jagororin al’umma a nan gaba, a yanzu sun zama wurare da ake zaune cikin tsoro da zullumi da tashin hankali.

A yayin da muke nazarin qididdgar da wata qungiya mai zaman kanta mai suna ‘Safe the Children’ ta fitar, ya zama dole a matsayinmu na qasa mu gaggauta samar da hanyoyin kare makarantun­mu daga ayyukan masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga.

Rahoton qungiyar ya nuna cewa, tun daga lokacin da aka sace ‘yan makarantan nan su 276 a garin Chibok da ke Jihar Borno a shekarar 2014, ‘yan makaranta fiye da 1,680 aka yi garkuwa da su. Wannan lamari na tayar da hankali, don kuwa ‘yan makaranta 180 suka rasa rayukansu yayin da 90 suka ji raunuka daban-daban a hareharen da aka kai wa makarantu a faxin tarayyar Nijeriya abin da ya zama wata barazana da kuma tashin hankali ga sauran xalibai da iyayensu.

Haka kuma, bayani ya nuna cewa, an yi garkuwa da malaman makarantu 60 yayin da malamai 14 suka rasa rayukansu a hareharen da aka kai makarantun an kuma lalata makarantu 25 a sassan Nijeriya.

A matsayinmu na gidan jarida, ra’ayinmu a nan shi ne, waxannan ba wai suna matsayin qididdiga ba ne kawai sun zama wani lamari da ke daqushe mafarkin matasanmu na zama wani abu a nan gaba, yana kuma lalata ginshiqi da fatan da ake da shi ta bunqasar tsarin karatun Nijeriya gaba xaya.

An qaddamar da wannan qungiyar ta ‘Safe Schools Initiative­s’ ce bayan da aka sace ‘yan matan makarantar Chibok a shekarar 2014 da mufin tabbatar da kariya ga makarantun­mu. Wannan shiri yana samun tallafi da goyon bayan Majalisar Xinkin Duniya, da qungiyar ‘yan kasuwan Nijeriya da sauran qungiyoyi masu zaman kansu, sun kuma nemi a tabbatar da samar da yanayi da muhalli mai tsafta da xalibai za su yi karatu ba tare da barazana ko kuma tsoro ba.

An samar da fiye da Dala Miliyan 30 a lokacin da aka qaddamar da shirin da nufin fitar da tsarin kare makarantu don samar da matasa da zamu iya alfahari da su a jagorancin qasar nan a nan gaba.

Amma kuma wannan mafarki da fata na qungiyar ‘Safe schools’ bai samu cika ba don kuwa an ci gaba da kai hare-hare a makarantu musamman a Arewancin Nijeriya, abin da yake ci gaba da sanya tsoro a kan yiyuwar samar da gyaran da ake buqata a vangaren makarantun­mu.

Qaruwar hare-haren da kuma garkuwa da ‘yan makaranta da ake ci gaba da yi ya jefa tsoro a zukatan xalibai da iyayensu gaba xaya.

Tambaya mai muhimmanci da ya kamata mu yi a wannan lokacin ita ce wai shin menene matsayin qungiyar ‘Safe Schools Initiative’ kuma ina fiye da Dala miliyan 30 da aka tara a lokacin qaddamar da qungiyar suka shiga?

Binciken da jaridar nan ta yi kwanakin baya ya nuna cewa, shekaru da dama da qaddamar da shirin ‘Safe Schools Initiative’ har zuwa yanzu wasu jihohi da dama basu amfana daga wannan asusun ba, haka kuma basu amfana da shirin qungiyar na kare makarantu ba.

Wannan wani abu ne da ya kamata ya tayar da hankali al’umma da dama musamman ganin qungiyar da ke da alhakin samar da kariya ga makarantum­u ta gaza cika alkawarint­a. Ana ci gaba da kai hare-hare a makarantun­mu babu qaqqautawa, a kan haka yana da matuqar muhimmanci mu miqa ayar tambaya ga masu tafiyar da qungiyar, na su bamu cikakkiyar bayanai na yadda aka sarrafa kuxaxen da aka tara don al’umma su san yadda aka kashe su.

Varnar da wannan lamari ya yi ga matsalar tsaro yana da matuqar girma musamman ganin Nijeriya na da ximbin yara da ke gararamba a kan titi basa zuwa makaranta, an qiyasta cewa, yara fiye da kashi 12.4 na yara waxanda basa zuwa makaranta suna yankin Afrika ta yamnma ne.

Matsalar tsaro ta hana waxanna yara zuwa makaranta, an hana su damar bayar da nasu gudummawar­su ga bunqasar al’ummar yankinsu da qasar su gaba xaya.

Ba wai muna jinjina matsalar kawai ba ne, ya kamata mu xauki mataki na kare makarantun don samar wa yaranmu rayuwa nagari.

Muna kira da a gudanar da bincike na musamman a kan yadda aka gudanar da qungiyar ‘Safe Schools’ don gano yadda aka kashe kuxaxen da aka tara, muna kuma bayar da shawara a tabbatar da wata qungiya ce mai zaman kanta za ta gudanar da binciken don kauce wa zargi da tabbatar da gaskiya.

Dole gwamnati ta muhimmanta­r da samar da tsaro a makarantum­u ta hanyar samar da qarin jami’an tsaro a makarantu, a kuma qarfafa samar da bayanan sirri da za su kai ga tarwatsa shirin ‘yan ta’adda tare da aikawa da gargaxi a duk lokacin da aka samu wasu bayanai da ke nuna akwai wata matsala.

Al’umma na da rawar da za su taka wajen tabbatar da tsaron makarantum­u, ya kamata su shiga a dama da su wajen kare makarantun­mu ta hanyar bayar da bayanan sirri ga jami’an tsaro da za su kai ga daqile ayyukan ‘yan ta’adda a yankunanmu.

Ya kamata xalibai da malamai da suka faxa hannun ‘yan ta’adda su samu tallafi na musamman na qwararru da zai taimaka musu su farfaxo daga tashin hankalin da suka fuskanta.

Abin takaicin a ra’ayinmu shi ne labarin xalibar makarantar Chibok da aka ceto kwanan nan, inda ta nemi a mayar da ita ga ‘yan ta’addan da suka kama ta. Wannan yana nuna cikakkiyar halin da qasarmu ke ciki ne.

A kan haka muke kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi su muhimmanta­r da lamarin tsaron makarantum­u, ta hanyar samar da kuxaxe da kayan aiki ga jami’an tsaro don yin haka tamkar kare qasa ce baki xaya. Lokaci ya yi da zamu tabbatar da kare makarantun da kuma kare mutuncinmu.

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria