Leadership Hausa

Kwana 100 A Karagar Mulki: Kamun Ludayin Sabbin Gwamnoni

-

A wannan makon ne galibin zavavvun gwamnonin jihohin qasar nan ke cika kwana 100 a kan karagar mulki, ciki har da sabbin da suka shigo a karon farko da kuma waxanda suke a kan wa’adi na biyu.

Ganin muhimmanci­n kwana 100 a kowacce gwamnatin dimokraxiy­ya, musamman a yanzu da al’umnma ke fama da matsaloli a vangaren tsaro, tattalin arziqi da zamantakew­ar rayuwa gaba xaya, ana iya fahimtar inda gwamnatin kowace jiha ta nufa bisa irin ayyukan ci gaba da ta gabatar ko ta aza tubalin yi cikin kwana 100.

Wakilanmu sun yi nazarin halin da ake ciki a wasu Jihohin Arewacin Nijeriya, musamman sabbin gwamnonin da aka samu waxanda suka hau karagar mulki, saboda xokin da jama’a suke yi a kansu da kuma irin kamun ludayinsu.

Sakkwato

Gwamna Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC, wanda ya yi galaba a kan Sa'idu Umar na jam'iyyar PDP bayan qarewar wa'adin zangon mulki biyu na Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya gaji gawurtacci­yar matsalar tsaro wadda ta addabi al'ummar Gabacin Sakkwato ba tare da hovvasar qwazon Gwamnatin Tarayya na shawo kan matsalar ba.

Jim kaxan da shigar sa ofis, Gwamna Aliyu ya gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan sha'anin tsaro tare da alwashin xaukar qwararan matakan da suka wajaba, domin ganin al'ummar yankin sun ci gaba da bacci da idanu biyu; akasin halin hare- hare, garkuwa da mutane da kisan gillar da 'yan ta'adda ke yi musu ba qaqqautawa. Daga bisani, Gwamnan ya yi ganawar musamman da Shugaban Rundunar Tsaro, Manjo Janar Chirstophe­r Musa da zummar kakkave ayyukan ta'addanci a faxin Jihar baki-xaya.

A cikin kwana 100, Gwamnan ya magance matsalolin da jami'an tsaron ke fuskanta da suka haxa da biyan bashin alawus na wata biyar da alqawarin duba matsalar rashin ingantattu­n motoci da suke fama da shi da kuma aminta da dukkanin buqatar da suka gabatar, wanda hakan zai inganta ayyukansu.

Gwamnatin Sakkwato, wadda tuni ta naxa 'Yan Majalisar Zartaswar Gwamnatin Jiha da Mashawarta­n Gwamna na Musamman da Kantomomin Qananan Hukumomi tare da wasu muhimman muqamai, baya ga biyan albashi a cikin lokaci, tuni ta fara aiwatar da ayyukan raya qasa da ci gaban al'umma ta hanyar shimfixa hanyoyin motoci a wasu zavavvun unguwanni tare da ci gaba da qoqarin kammala gadar sama a Rijiyar Xoruwa, wadda Gwamnatin Tambuwal ta bayar da kwangilar ginawa a kan naira biliyan 3.5.

Haka zalika, gwamnatin ta aiwatar da qawata tagwayen babbar hanyar Fadar Gwamnati da ado na musamman. Sai dai tuni jam'iyyar PDP a Jihar ta nuna rashin dacewar bayar da kwangiloli­n hanyoyin ba tare da amincewar Majalisar Zartaswar Jihar ba, wadda a lokacin ba a kafa ba. Jam'iyyar ta ce ko kaxan ba a bi doka da qa'ida ba; wajen bayar da ayyukan waxanda kuma ta ce ba a bayyana adadin kuxin aikin da kuma 'yan kwangila ba.

Jihar Sakkwato, wadda ke fama da yawaitar shara a mafi yawan wurare, ta kafa kwamiti na musamman a qarqashin jagorancin fitaccen xan siyasa, Alhaji Ummarun Kwabo (Jarman Sakkwato) domin tsaftace Birnin Sakkwaton, aikin da tuni kwalliya ta fara biyan kuxin sabulu.

Bugu da qari, matakan da gwamnati ta xauka na magance matsalar wuta a Asibitin Qwararru ta jiha da qoqarin magance matsalar ruwan sha da dawowa da kuma biyan tallafin wata- wata na marasa galihu; duka al'ummar jihar sun yaba.

A siyasance kuma, tuni sabuwar Gwamnatin Sakkwato ta fara binciken Gwamnatin Tambuwal, wadda suke da zazzafar adawa ta hanyar kafa hukumar bincike da zummar alhakin binciken gwanjon motoci da gidaje da Tambuwal ya yi kafin ya bar mulki tare da filayen da gwamnatins­a ta raba kyauta da kuma gidajen da aka sayar. Haka nan kuma, gwamnatin ta soke dukkanin muqaman da Tambuwal ya naxa bayan zave tare da dakatar da dukkanin Sarakunan Gargajiya da tsohuwar gwamnatin ta naxa a qarshen mulkinta.

Har wa yau, tuni Jam'iyyar PDP ta bayyana wannan bincike a matsayin bita- da –qulli, don tozarta jami'anta. A cewar Kakakin Jam'iyyar, Hassan Sahabi Sanyinnawa­l, an gudanar da gwanjon ne a bisa qa'ida ba tare da sava wa doka ba, sannan su kansu jigogin APC a jihar sun amfana da wannan gwanjo a baya. Sai dai Kakakin Gwamnatin ta Sakkwato, Abubakar Bawa ya ce babu nufin tozartawa a wannan bincike, illa a bincika idan an bi qa'ida kamar yadda doka ta tanada ko kuma akasin hakan.

Kano

Siyasar Jihar Kano ta sha banban da siyasar sauran Jihohin Qasar nan, musamman ganin irin salon siyasar bai wuce hannun karva hannun mayarwa ba. Domin idan za a iya tuna Shekarar 1979 da Gwamna Abubakar Rimi ya xare mulkin Kano, wa’adin Shekara huxu kawai ya samu, daga nan abokin adawarsa Sabo Bakin Zuwo ya karve kujerar, hakan ce ta faru a shekara ta 1999, inda Kwankwaso ya lashe zaven Gwamna, amma shi ma shekara huxu kacal ya samu a kan mulki, sai abokin hamayyarsa na Jam'iyyar ANPP; Malam Ibrahim Shekarau ya kwace mulkin, wanda shi ne gwamna na farko da ya yi nasarar sake cin zango na biyu a kan karagar mulki, amma shi ma daga qarshe Kwankwason ya sake dawowa a shekara ta 2011 ya karve mulkin daga hannun jam’iyya mai mulki, a wancan lokaci ta ANPP.

Bayan da Kwankwaso ya qarasa, cikin shekaru huxunsa da kundin tsarin mulki ya ba shi, sai ya miqa wa Mataimakin­sa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda shi ma ya yi sa'ar yin zango biyu a kan karagar mulkin, daga nan kuma sai NNPP wadda Abba Kabir Yusif ya tsaya wa takara ya kayar da jam'iyya mai mulki ta APC, wanda yanzu haka yake cika Kwana 100 a kan karagar mulkin Jihar Kano.

Tun bayan rantsar da shi, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana manufofin gwamnatins­a na cika alqawuran da suka xauka a lokacin yaqin nemnan zave, waxanda suka haxa da qwato dukkanin wasu filaye ko kadarar da gwamnatin da ta gabata da ake zargin yin watandarsa. Sai kuma shirin gwamnatin tasa na sake dawo da tsarin tura 'ya'yan talakawa zuwa qasashen waje domin samun digiri har da digirgir, wanda yanzu haka xalibai 501 ke jiran tashinsu zuwa makarantu daban- daban, domin ci gaba da karatu a qasashen na waje, ga Kuma shirin nan nasa na Aurar da Zawarawa, wanda a halin yanzu aka sauya wa suna da Auren 'yar Gata.

Shi ma yanzu haka, aikin ya yi nisa na aurar da waxannan Zawarawa kimanin 1,800, waxanda aka warewa kuxin lakadan ba ajalan ba; Naira Miliyon 840,000,000.00, sai kuma sake farfaxo da Makarantun SAS a faxin Qananan Hukumomin Jihar Kano 44.

Gwamnatin Abba Kabir Yusif, ta bayyana tare da zartar da shirin dawo da ladabin Ma'aikatan Gwamnati, sake dawo da Asibitin Yara na Hasiya Bayero da a baya ake zargin sayar da shi.

Gwamna Abba Kabir, ya kuma ayyana biyan xaukacin kuxaxen 'yan fansho, komawa aikin matatar ruwa da ke Tamburawa domin wadata Kano da ruwan Sha, biya wa xaliban Jihar Kano kuxin Jarrabawar NECO da kuma sake ginin wasu shataletal­en da ke qwaryar birnin jihar.

Bugu da qari, babban abin da ke xaukar hankalin jama'a shi ne, barazanar da Gwamna Abba Kabir Yusif ya yi wa Kwamishino­ninsa a lokacin da yake rantsar da su, inda ya sanar da cewa zai sa wa ayyukan Kwamishino­nin ido cikin watanni shida na farko, wanda duk ya gaza cimma abin da ake buqata ya tabbatar da cewa sallamar sa gwamnan zai yi. Sai kuma sake fasalin yadda ake tattara harajin Jihar ta Kano, samun nasarar sulhunta savanin da ke wakana tsakanin Hukumar Al'adu ta Jihar Kano da kuma Hukumar Tace Finafinai. Dawo da ciyar da xaliban makarantun firamare tare da xinka musu kayan makaranta.

Ta fuskar tallafawa mata da matasa da hanyoyin dogaro da kai, Gwamnatin Abba cikin kwanakin 100 ta waiwayi shirin nan na CRC, wanda ake raba wa mata 100 daga kowacce Qaramar Hukuma jarin naira dubu goma-goma, sai kuma batun Makarantar Koyon Sana’o’u, ita ma tuni wannan gwamnati ta sake dawowa kanta gadangadan.

Babban qalubalen da Gwamnatin ta Injiniya Abba Kabir Yusif ke fuskanta, bai wuce rusau da ta gudanar ba, wanda ko shakka babu wannan ya tava zukatan ‘yan Kasuwar da suke ganin sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar gwamnatin tasa. Haka nan, batun korarar wasu ma’aikata da ake zargin gwamnatin da ta gabata ta xauke su ba bisa qa’ida ba. Amma dai kamar yadda kowa ya sani, dukkan abubuwan nan jama’a sun kwana da sanin su, domin tun yana yaqin neman zave ya yi iqrari tare da alqawarin farawa da su da zarar ya samu nasarar cin zave, sannan ba don Kotu ta dakatar da aikin ba; da tuni aikin gama ya riga ya gama.

Zamfara

Cikin manyan qalubalen da sabon Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal ya fuskanta a yayin da ya karvi ragamar jagorancin Jihar Zamfara ya haxa da matsalar tsaro, wadda ta qi ci ta qi cinyewa.

Cikin matakan da gwamnan ya xauka a cikin kwana 100 na farkon mulkinsa, sun haxa da ziyartar Shugabanni­n Rundunonin TSaro tare da qarfafa musu gwiwa ta hanyar samar musu da cikakken kayan aiki. Gwamna Dauda Lawal ya ziyarci mai ba wa shugaban qasa shawara a kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribado, ya kuma nemi haxin kan shugabanni­n al’umma da Sarakunan Gargajiya, saboda muhimmanci­nsu a tsarin tafiyar da al’umma da zamantakew­a, a cewarsa su ne suka fi kusa da al’umma, don haka dole a tafi tare da su.

A watan Agustan 2023 ne kuma ya qaddamar da fara aikin yin sabbin hanyoyi a Birnin Gusau, duk a cikin shirinsa na sabunta biranai.

 ?? ?? •Gwamna Dauda Lawal tare da Shugaban Hukumar Civil defence a ziyarar da ya kai masa a Abuja
•Gwamna Dauda Lawal tare da Shugaban Hukumar Civil defence a ziyarar da ya kai masa a Abuja

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria