Leadership Hausa

Kwana 100 A Karagar Mulki: Kamun Ludayin Sabbin Gwamnoni

-

Sashen farko na wannan aikin za a fara ne da yin hanyoyi guda huxu masu tsawon kilomita 3.1, wanda kuma za su haxa da manyan kwalbati da sauran makamantan­su.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta bayyana cewa, an yi bikin qaddamarwa ne a titin Gidan Sambo, daura da ofishin 'yansanda da ke Gusau.

Ya qara da cewa, wannan aiki na hanyoyi yana daga cikin alqawuran da Gwamna Dauda ya xauka a lokacin yaqin neman za ensa; cewa zai sabunta biranai ta hanyar gina ingantattu­n hanyoyi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, "A wurin bikin qaddamarwa­r, Gwamna Lawal ya jaddada aniyarsa ta sabunta biranai a faxin Jihar Zamfara, lamarin da aka rasa a gwamnatoci­n baya.

"Sashen farko na aikin, zai zagaya shatale-talen Bello Barau zuwa Hanyar Babban Ofishin 'yansanda zuwa gidan gwamnati, zuwa Kwanar 'Yan Keke, zuwa Fadar Sarki, zuwa Tankin Ruwa.

"Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi imanin cewa, idan aka samar da hanyoyi masu inganci tare da bunqasa biranai, ko shakka babu zai taimaka wajen kawo wa jihar masu zuba hannun jari.

"Haka nan kuma, Gwamna Dauda ya nemi alfarmar jama'ar Gusau da su yi haquri da duk wata takura da aikin zai haifar, saboda za a mori alfanunsa nan gaba kaxan masu yawa."

Kaduna:

A yayin da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani ke shafe kwana 100 a kan karagar Shugabanci­n Jihar, alamu sun nuna cewa, akwai ci gaba ta fuskar magance matsalar tsaro a jihar; duk kuwa da cewa akwai sauran rina a kaba.

Har ila yau, manyan abubuwan ci gaba da Gwamnatin Uba Sani ta aiwatar a cikin kwana 100, mafi jan hankali a cikinsu su ne qaddamar da aikin gina rukunin gidaje 5,000 ga talakawa da kuma rage kuxin karatu a manyan makarantun jihar.

Gwamnatin ta rage kuxin karatu a Jami’ar Jihar Kaduna daga 150,000 zuwa 105. Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli daga 100,000 zuwa 50,000, Kwalejin Ilimi ta Gidan Waya daga 75,000 zuwa 37,500, sai kuma Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya ta Shehu Idris da ke Makarfi da aka rage kuxin daga 100,000 zuwa 70,000, kana Kwalejin Horar da Malaman Jinya da aka rage kuxin karatunta daga 100,000 zuwa 70,000.

Dangane da sha’anin tsaro, wakilinmu ya ji ta bakin Mista Samson Auta, wanda ya fito daga Kudancin Kaduna; kuma har ila yau jagoran Qungiyar Daqile Tashin Hankali a Cikin Al’umma ta CMMRC, ya ce an samu raguwar kai wa al’umma hare-hare cikin watanni uku da suka wuce, musamman a Kudancin Kaduna.

Samson ya qara da cewa, maiyuwa an samu raguwar kai hare-haren ne, saboda qoqarin sojoji da sauran hukumomin tsaro da kuma qoqarin qungiyoyi masu zaman kansu na sasanta al’ummar da ke zaman doya da manja a tsakaninsu da juna.

Sai dai, ya ce, ana ci gaba da samun 'yan hare-haren, musamman na masu yin garkuwa da mutane, inda suke sace matafiyan da suka biyo babbar hanyar Qaramar Hukumar Kajuru tare da yin kisa a wasu lokutan.

Shi kuwa wani mai fashin baqi a kan al'amuran yau da kullum, Alhaji Musa Bala, ya shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, gwamnatin a watanni uku da suka wuce, ta yi qoqarin inganta tsaro da baiwa matasa damar komawa makaranta ta hanyar rage kuxin karatu, “domin duk wanda ba ya zuwa makaranta, Allah ne kaxai ya san irin halin da zai iya shiga na aikata ayyukan da ba su dace ba.”

Haka zalika ya ce, Gwamna Uba Sani ya yi qoqari wajen kawo masu zuba jari daga Qatar, domin gina gidaje da bunqasa fannin kiwon kaji, wanda hakan zai qara samar da ayyukan yi da kawar da tunanin matasa daga shiga halin rashin tsaro.

Shi ma mai fashin baqi a kan al’amuran yau da kullum, kuma Shugaban Qungiyar Manoman Masara na yankin Arewa maso yamma, Alhaji Adamu Mohammed Maqarfi ya ce, ya zuwa yanzu “mun godewa Allah domin kuwa ana samun sauqi sosai, musamman ta fuskar rage kai wa manoma hare-hare da ake yi a wasu guraren.”

A cewar ta Maqarfi, amma gaskiyar magana abin damuwa a wasu vangarorin guda biyu, musamman a Qananan Hukomomin Birinin Gwari da Giwa, har yanzu ana ci gaba da samun koke-koken kai wannan hare-hare.

Daga vangaren jami'yyar adawa kuwa, Shugaban Jami'yyar ADC reshen Jihar Hon. Ahmed Tijjani Mustapha, ya yaba da abubuwan da Gwamna Uba Sani ya yi a vangaren ilimi, domin yara su samu ingantacce­n ilimi kyauta tun daga matakin Firamare har zuwa Sakandire.

A wani vangaren kuma, Gwamna Uba Sani a kwanan baya ya amince da a keve ware 15 a cikin kasafin kuxi na shekara-shekara na jihar, domin qara bunqasa fannin kiwon lafiya.

Neja

A daidai lokacin da Gwamnatin Neja, qarqashin sabon gwamnan jihar, Rt. Hon. Umar Mohammed Bago ke cika kwana 100, jama’a da dama sun zura idanu don ganin kawo qarshen matsalar tsaron da ya kai ga al'ummomi da dama barin gidajensu da gonakinsu, sakamakon tsoron yawaitar hare-haren da 'yan bindiga ke kai musu, musamman a yankunan karkara da abin ya fi shafa a vangarorin yankin Neja ta gabas da Arewa.

Duk da qoqarin da take yin a matsalolin da ta gada daga gwamnatin da shuxe, an samu nasara a wasu yankunan kamar matsalar sara suka da aka yi tanadi na musamman na kafa Rundunar Tsaro, wadda ta himmatu musamman a kan qwaryar garin Minna; inda gwamnatin ta sayo motoci don qarfafa guiwar rundunar aqalla guda ashirin, wanda aka damqa su ga jami'an 'yansanda, Rundunar Yaqi da hana fatauci da shan miyagun qwayoyi, jami'an tsaron fararen hula da ‘yan sinitiri.

Lamarin ya yi wa al'ummar cikin garin Minnan daxi, musamman yadda rundunar da zage damtse ba dare ba rana, lungu da saqon qwaryar cikin garin na Minna na ganin bayan 'yan sara suka cikin qwaryar Minna da ya yi sanadin rasa rayuka da dukiyoyin jama'a da matasan kan aiwatar a lokacin hare-harensu.

Sai dai lokacin da ake ganin jami'an tsaron bisa goyon bayan gwamnatin, sun samu damar karya lagon sara sukar, a vangaren 'yan fashin daji da ke kai hare hare ga mutanen karkara kuwa, abin ya xauki sabon salo, inda 'yan bindigar ke kai sumame ga mutanen karkarar na xauki xaixai.

Yanayin noma ga mutanen karkara kuwa, duk da cewa 'yan bindigar ba su cika shiga garuruwan karkara ba, rahotanni sun tabbatar da cewa har yanzu 'yan bindigar na da iko da wasu yankunan, musamman duba da irin harajin da suke qaqaba wa mutanen karkarar manoma.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, tun a shekarun baya da 'yan bindigar suka fara sanya harajin; abin kullum gaba yake sake yi, misali qauyen Dusai da Gulbin Boka da ke Qaramar Hukumar Mariga, a bayan nan sun shiga sahun 'yan harajin da 'yan bindigar suka qaqabawa. Dusai dai ana neman naira miliyan tara a hannunsu kafin su samu damar mayar da hankali kan gonakinsu, Gulbin Boka kuwa, wani mazauni garin ya ce 'yan bindigar sun umarci su biya naira miliyan arba'in, wanda hakan ya tilasta wa manoma da dama yin hijira domin canja matsuguni, bayan mutanenmu da dama da ke hannun 'yan bindigar suna garkuwa da su.

Hon. Aminu Musa Bobi, Shugaban Jam'iyyar APC na riqo a Jihar Neja, wanda ya tava zama mamba a kwamitin tsaro da gwamnatin da ta shuxe ta kafa, musamman a yankin Masarautar Kontagora, wanda kuma ya tava faxawa komar 'yan bindigar, cewa ya yi; “maganar gaskiya gwamnati da jami'an tsaro na bakin qoqarinsu kan lamarin, wannan wani iftila'i ne da Allah ya jarabce mu da shi. Babban abin da ya kamata jama'a su sani shi ne, bai wa gwamnati da jami'an tsaro haxin kai tare da komawa ga Allah na neman mafita a kan wannan lamari.”

Tun bayan hawan gwamnatin kan wannan mulki, jama'a ke tsammanin kafin kwana xari na mulkin Bago, an yi nisa da wasu ayyukan raya qasa, musamman ma batun kammala aikin hanyar Minna zuwa Bida, hanyar Kontagora zuwa Bida da wasu ayyukan Gwamnatin Tarayya da ya shafi hanyar Bida-Agaie, Lapai zuwa Lambata da hanyar Suleja da aka fara tun mulkin Jonathan.

Zuwa yanzu dai, kusan waxannan da gwamnatin ta sha alwashin idan ta kammala daidaituwa za ta xora xan ba a kai, akwai alamar ayar tambaya a kai, musamman dangane da rahotanni da ke yawo na samun maqudan kuxaxen da aka ce gwamnatin ta yi da har yanzu ba ta kammala natsuwar da zai baiwa jama'a qwarin guiwa ba.

Wani abin farin ciki da kafa tarihin da gwamnatin ta yi cikin kwanakinta qalilan shi ne, bai wa mata xari da talatin da xaya muqaman siyasa, bisa iqirarinta na cika alqawarin da ta yi musu lokacin yaqin neman zave.

Haka nan gwamnatin ta yi rawar gani wajen kafa sabuwar Ma'aikatar kula da Harkokin Fulani, irin ta ta farko a tarihin Arewacin wannan qasa, wanda damqa Ma'aikatar a hannun qungiyoyin

Fulani, inda suka ba da kwamishina­n da zai jagoranci Ma'aikatar, wanda cikakken Bafilatani ne.

Dangane da muhimman ayyuka kuwa, Gwamna Umar Mohammed Bago, ya ce kwanakinsa xari a kan kujerar Gwamnatin Jihar, zai mayar da hankali ne a kan tsara qudurce-qudurcensa na shekaru huxu a kan mulkin jihar, inda zuwa yanzu Ma'aikatar Ayyuka ta himmatu wajen tsara taswirar ayyukan hanyoyi xari biya da hamsin da xaya da gwamnatin ke qudurin farawa da kammala su a qanqanin lokaci.

Hususan dai, a cikin kwanaki xarin na mulkin Bago, babu wani abin da jama'a suka fi shauqi kamar kawo qarshen matsalar tsaro, samar da guraben ayyuka ga matasa da gwamnatin ta ce za ta fi mayar da hankali a kansu, musamman vangaren noma da samar da ayyuka da abinci da kuma tsaron qasa.

Filato

A jihar Filato kuwa, kamar sauran sabbin gwamnoni, Gwamna Caleb Mutfwang na Jam’iyyar PDP, a gavar cika kwana 100 a kan qaragar mulki, bincike ya nuna cewa ya taka rawa a wasu vangarori. Kazalika, a wasu vangarorin kuma ya gaza. Tun lokacin da gwamnan ya hau kan mulki, bai yi fashin biyan albashin ma’aikata ba, sai dai wasu haqqoqi kamar kuxaxen hutu da na fansho har zuwa yanzu bai biya ba, kazalika an samu matsalar tsaro tun a farko-farkon gwamnatins­a.

Koda-yake a kwanakin baya, Gwamna Caleb ya ce, gwamnatin baya ta Simon Lalong ta gadar masa da bashin albashi na kimanin naira biliyan 11 da bai biya ma’aikata ba.

Shi dai sabon gwamnan, Caleb Mutfwang, a lokacin amsar mulki, ya yi alqawarin haxa kan al’ummar jihar ne, sannan kuma ya gargaxi masu kunna wutar rikici da raba kawukan jama’a da cewa, daga yanzu su daina domin shi kam ba zai lamunci hakan ba.

Sai dai za a iya cewa, gargaxin nasa bai yi tasiri ba, domin kuwa an samu kashekashe a cikin kwanaki 100 na mulkinsa. A faxin gwamnan, ya kamata ne kowa ya ba da gudunmawar­sa wajen kyautata zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ba tarwatsa kawuna ba.

Sannan, ya koka kan yadda gwamnatin da ya amshi mulki a hannunta ta gadar wa gwamnatins­a tulin basuka da suka haura sama da biliyan N200.

“Ba za mu tozarta kowa ba, kuma ba za mu zauna muna sukar juna ba, za mu yi zurfin tunani mu xauki matakin gyaran abubuwan da muka gada yau, amma muna

 ?? ?? •Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda a yayin da yake rantsuwar maka aiki
•Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda a yayin da yake rantsuwar maka aiki

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria