Leadership Hausa

Kwana 100 A Karagar Mulki: Kamun Ludayin Sabbin Gwamnoni

- •Gwamna Bago a ziyarar da ya kai kasuwar Madalla

buqatar mu yi wasu tulin tambayoyi, saboda muna buqatar mu yi aiki tuquru mu kafa tarihi wajen kyautata mulkinmu,” ya shaida.

Bisa bayanan da qungiyar ci gaban qabilar Mwaghavul (MDA) da qungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta MACBAN suka gabatar, sama da mazauna qauyukan Mangu da wasu Fulani sama da 200 ne aka kashe a tsakanin watan Afrilu zuwa Yulin 2023, lamarin da ke qara jefa jama'a cikin zaman xar-xar.

Kodayake, a wata tattaunawa mai magana da yawun gwamnan jihar Filato Gyan Bere, ya ce har yanzu gwamnati ba ta samu rahoton yawan mutanen da aka kashe a rikicin na baya-bayan nan ba.

Shugaban qungiyar ci gaban Mwaghavul (MDA), Cif Joseph Gwankat, ya ce, “Mun fito ne domin mu shaida muku haqiqanin abubuwan da suke faruwa da muhallanmu. Wasu 'yan ta’adda na kai hare-hare a Mwaghavul da wasu sassan Qaramar Hukumar Mangu.”

“Hare-haren da Fulanin suke kawo mana ya fara ne tun a watan Afrilu har zuwa yanzu, da farko lamuran sun fara da garkuwa da mutane, lalata gonaki da wasu matsaloli daga baya lamarin ya zama qaddamar da hare-hare.”

Sai dai kuma, Shugaban Qungiyar Fulani ta Miyetti Allah Cattle Breeders Associatio­n of Nigeria (MACBAN), Nuru Abdullahi a jihar, ya qaryata cewa Fulani ne ke janyo waxanan matsaloli, inda ya yi zargin cewa, su ma ana kashe musu mambobi haka siddan.

A kwanakin nan, gwamnan ya sanar da shirin gwamnatins­a na yin haxaka da masu abokan jere, domin kyautata harkokin kiwon lafiya. Ya tabbatar da cewa gwamnatins­a ba za ta yi sake da kiwon lafiyar al’ummar jihar ba.

Daga cikin abubuwan da gwamnan ya samu cimmawa a wannan kwanaki, sun haxa da samun nasarar naxa sabbin kwamishino­nin da za su taimaka masa wajen gudanar da harkokin mulkin jihar. A kuma ranar 4 ga watan Agustan 2023 ne, gwamnan ya rantsar da kwamishino­nin nasa.

Kuma gwamnan na Filato, Barista Caleb Manasseh Mutfwan ya shirya wa jami’an gwamnatins­a taron qara wa juna sani, domin sanin makamar aiki da inda aka dosa, ba wai yin aiki ido a rufe ba.

A wani babban matakin shawo kan rikici a wasu yankunan Filato, gwamnan jihar, ya ba da umarnin samar da filin noma mai girman hekta 900, a sassan Qananan Hukumomi uku Mangu, Barkin Ladi da Riyom da ke jihar, domin daqile yawaitar faxace-faxacen da ake samu a yankunan.

Wannan mataki na ware filin noma, za a iya cewa wani qoqari ne sosai da gwamnan ya yi domin kawo qarshen rikice-rikicen da ake yawan samu a sassan wuraren.

A wani mataki na garanbawul ga harkar ilimi, Gwamnan Jihar Filato, ya sha alwashin cewa zai kafa hukumar kula da manyan makarantun sakandari, domin qara samar da kula ga sashin ilimi.

Dukkannins­u a cikin kwana 100, gwamnan ya yi alqawarin cewa zai samar da takin zamani masu tarin yawa da kayan noma da kuma tiraktoci a nan kusa, domin kyautata harkokin noma a faxin jihar.

Har-ila-yau, gwamna Caleb, ya yi alqawarin maida ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu na asali, waxanda suka yi qaura daga muhallansu sakamakon matsalolin tsaro.

Duk a cikin qoqarin gwamnatin tasa na kyautata alaqa da abokan jere, gwamnan ya qaddamar da sufurin jirgi daga Abuja zuwa Jos kai tsaye, domin kyautatawa da faxaxa harkokin sufuri. Kamfanin ValueJetAi­rline shi ne ya cimma yarjejeniy­a da Gwamnatin Jihar, domin fara jigilar.

A baya-bayan nan kuma, Gwamnan Filato Caleb, ya buqaci haxin kan Gwamnatin Qasar Kanada, a vangarorin gine-gine, harkokin noma, daidaiton jinsi da sauran vangarorin kyautata rayuwa.

Benuwai

A Jihar Benuwai kuwa, Gwamna Hyacinth Alia, a cikin kwanakinsa 100 a mulki ya samu nasarar naxa kwamishino­ni 17 da masu ba shi shawara 23. Domin bunqasa abinci, Gwamnan Benue ya nemi goyon bayan gwamnatin tarayya. Kana a wani matakin fara gwamnati da Bismilla a cikin kwanakinsa 100, ya qaddamar aikin shimfixa titina na sama da naira biliyan shida (6b), hanyoyin da za a gina xin guda 16 a cikin garin Makurdi za haura sama da kilomita 15.39.

A cewar gwamnan, aikin zai laqume sama da bilyan shida a yayin gudanar da shi cikin watanni 11 kacal.

Haka zalika, gwamnan cikin wannan kwanaki nasa, ya kafa kwamitin da za su sanya idanu a kan daqile yaxuwar cutuka a faxin jihar.

A qoqarin Gwamna na kyautata aikin gwamnati, cikin kwana 100, ya samu nasarar bankado ma'aikatan boge 2,500 da suke amsar albashi ta haramtatun hanyoyi. Haka zalika, an samu wannan nasarar ne a aikin bincike da tantance ma'aikatan karo na farko da gwamnatin ta yi.

Gwamnan ya sanar da aniyarsa ta tsarkake sashin biyan albashin ya na mai cewa, ba zai bari wasu na lalata tsarin aikin gwamnati ba. Matakin a cewar gwamnan, ya taimaka wajen samun rarar naira biliyan 1.2.

Bugu da qari Gwamna Alia, ya kafa kwamitin da zai binciki kuxaxe da kwangiloli­n Jami'ar Benue da ke Makurdi daga 2016 zuwa yanzu, duk hakan na cikin qoqarinsa na daqile qofofin fata ne.

Har ila yau, gwamnan ya amince da aiwatar da sabon tsarin kammala aiki na shekaru 65 da tsawon lokaci na shekara 40 ga dukkanin malaman da suke jihar, bisa shawarwari­n da TRCN ta bayar.

Za a iya cewa dai, kamun ludayin sabbin gwamnonin ya zama kadaran, kadahan musamman idan aka yi la’akari da tarin matsalolin da suka gada da kuma yadda cire tallafin mai ya haifar tun daga ranar da aka rantsar da su. Abin jira a gani dai shi ne, wane ne zai kai bantensa?

Katsina

A cikin kwana 100, abubuwan arziqin da Gwamnatin Jihar Katsina ta yi qarqashin jagorancin Malam Dikko Umar Raxxa, sun haxa da tunkarar matsalar tsaro, inda ya amince da kashe kuxaxe kimanin naira miliyan dubu 7.8.

Sannan Malam Raxxa, ya jagoranci samar da fili na wucin gadi wanda za a kafa Jami'an Kiwon Lafiya ta Gwamnatin Tarayya a Qaramar Hukumar Funtua ta Jihar Katsina.

Bayan haka, Gwamnan ya ba da umarnin sayen shinkafa, inda za a kashe naira miliyan dubu biyu da Gwamnatin Tarayya ta baiwa jihohi.

Raxxa, ya ba da aikin faxaxa gadar Qofar Qaura da ta fara zama barazana, musamman ambaliyar ruwa; inda yanzu haka an kusa kammala ayyukan wannan gada.

Haka kuma, gwamnan ya ba da umarnin a fitar da miliyoyin nairori, domin xaukar nauyin waxanda iftila'in 'yan bindiga ya shafa a Jihar Katsina.

Abu na farko da Gwamnan Jihar Katsinan, Malam Dikko Umar Raxxa ya fara shi ne, cire masu riqe da muqaman siyasa waxanda ya gada daga tsohon Gwamna Aminu Bello Masari.

Sai kuma, yadda Gwamna Raxxan ya dakatar da manyan sakatarori daga muqamansu kafin daga baya ya kafa wani kwamiti da zai shirya jarrabawa ga duk wanda ke san zama Babban Sakatare.

Da yawa daga cikinsu, sun faxi wannan jarrabawa da aka ce an xauko wani qwararre daga Jihar Barno, domin shiryawa.

Haka kuma, gwamnan ya yi tafiye-tafiye har sau goma sha xaya zuwa Abuja, sannan ya fita qasashen waje sau uku, inda yanzu haka ya bar qasar kusan kimanin kwana goma.

Har ila yau, Malam Dikko Raxxa ya ba da umarnin Qananan Hukumomin Jihar Katsina 34, su sayi masara domin raba wa jama'a, sai dai har gobe jama'a na tambayar nawa aka kashe wajen sayen wannan masara, batun da har gobe babu amsa daga vangaren gwamnatin

Bayan haka, Gwamnatin Raxxa ta dawo da dokar hana hawa babur a wasu garuruwa da ke fama da matsalar tsaro, batun da masana ke cewa, dokar ba ta haifar da xa mai ido ba.

Kebbi

Tun daga ranar 29 ga mayun shekarar 2023, da Gwamna Nasir Idris ya karvi karagar madafun iko a Jihar kebbi, wanda zuwa wannan wata na Satumba, yana qasa da kwanaki 100 a kan karagar mulkin jihar. Amma duk da haka, gwamnan ya mayar da hankalinsa wajen tabbatar shinfixa sababin hanyoyi a cikin qwaryar babban Birnin Jihar ta Kebbi.

Inda a ranar 25 ga watan Yuli, ya ba da kwangilar shinfixa sabbin hanyoyin motoci na cikin babban Birnin Jihar guda biyar, a kan naira bilyan 9.4, ga Kamfanin Habib Engineerin­g Nig. Limited, inda ake sa ran kammala aikin a cikin wata goma sha takwas masu zuwa. Aikin shinfixa sabbin hanyoyin, zai soma ne tun daga hanyar shigowa jihar, wato NNPC Mega har zuwa shataletal­en RIMA, har zuwa bakin Ofishin Hukumar NDLEA, ya kuma tashi zuwa shataletal­en gidan man AP 2, wato hanyar fita daga garin Birnin na Kebbi.

Haka zalika, abubuwan da za a sanya a manyan titunan sun haxa da, hasken wutar lantarki mai aiki da hasken rana (solar street lights), ga hanyoyin guda biyar da kuma shuke-shuke na zamani.

Haka nan kuma, gwamnan ya ba da umarnin biyan kuxaxen tallafin karatu ga xaliban da ke karatu a Jami'o'in Qasar nan, 'yan asalin Jihar Kebbi, waxanda aka tantance a jami'o'in daga shekarar 2023 zuwa 2024.

Kazalika, ya sanya hannu tare da amincewa da kashe kimanin naria milyan 92.2, domin sayo sinadaren kemikal; don inganta samar da ruwan sha ga al'ummar jihar baki-xaya. Har wa yau, an sake fito da wani shiri na tallafi tare da inganta rayuwar kasuwancin masu qaramin qarfi da kuma marasa qarfin baki-xaya, wato KBCARES; inda aka ba da tallafi ga mutane dubu ashirin a dukkanin faxin Qananan Hukumomi 21 na jihar, wanda mata da maza matasa suka samu cin gajiyarsa, inda aka baiwa marasa qarfi naira dubu xari, sai kuma masu qaramin jari naira dubu xari da hamsi kowannensu.

Shirin dai, an tsara shi ne domin tallafa wa mutane dubu ashirin da takwas, inda kashin farko na shirin kawo yanzu ya tallafa wa mutane dubu ashirin a Qananan Hukumomi 20. Kashi na biyu kuma zai tallafa wa mutane dubu takwas.

Har ila yau, Gwamnatin Gwamna Nasir Idris a ranar 19 ga watan Augusta 2023, ta ba da kwangilar kammala aikin Sakatariya­r Ma'aikatar da ke a Gwadangaji, kan kuxi naira biliyan 10 ga kamfani biyu, ana sa ran kammala aikin Sakatariya­r a cikin wata goma sha takwas kacal, kamfanunuw­an da aka baiwa aikin sun haxa da, ‘MTECH Universal Concept Limited’ da kuma ‘ZBCC Limited’, haka kuma an kasa aikin gida biyu; wato Lot A da Lot B.

Aikin ginin Sakatariya­r, tun a farkon Gwamnatin Tsohon Gwamna Saidu Usman Dakingari, aka ba da Kwangilar ga Kamfanin ‘Rockwell Nig. Limited’ a kan kuxi naira biliyan 3.8, daga baya aka koma bitar kwangilar, saboda tashin kayan aiki zuwa naira biliyan 7.7, a watan Disamba na shekarar 2015. Bisa ga haka ne Gwamna Nasir Idris, ta qara ba da wannan kwangila domin kammala aikin.

Yanzu haka, Gwamnatin Jihar tana kan bayar da tallafin rage raxaxin janye tallafin man fetur ga al'ummar jihar. Bugu da qari, a watan da ya gabata, Gwamna Nasir Idris ya qaddamar da rabon taki ga al'ummar jihar kyauta, wanda manoma a jihar suke ta yaba masa tare da sanya albarka.

 ?? ??

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria