Leadership Hausa

Adalci, Amana, Kamewa Da Gaskiyar Manzon Allah (SAW)

-

Masu karatu, assalamu alaikum wa rahmtullah. Har yanzu dai muna kan darasi a kan kyawawan xabi’un Annabinmu, Manzon Rahama (SAW). A makon da ya gabata mun kawo muku darasi na biyu game da qanqan da kai na Annabi (SAW) wanda a ciki muka yi bayanin cewa, wani mutum ya tava shigowa wurin Annabi (SAW), sabida kwarjini sai makerketa ta kama Mutumin, Annabi (SAW) ya ce masa “sauwaqa wa kanka, ni ba sarki ba ne, ni xan wata Mace ne daga dangin Quraishawa wacce take cin Kilishi.”

Haka nan, an karvo daga Abi Hurairah ya ce, wata rana na raka Annabi (SAW) Kasuwa, sai ya siya Wando, ya ce wa mai bayar da farashi, ya yi wa wandon farashi kuma ya qara xan wani abu a kai da za a bai wa mai sayar da Wandon, sabida farin ciki, ga riba ya samu mai yawa kuma an ce a qara masa wani kuxi, kawai sai ya rugo ya cafke hannun Annabi (SAW) yana so ya sunbanci hannun, sai Annabi (SAW) ya janye hannunsa ya ce wannan baibayi ne ke wannan, n iba sarki ba ne, ni Mutum ne a cikinku. Sannan ya amsa wandon, na tafi in amsar masa, sai yace “mai kaya shi ya fi cancanta ya xauki kayansa.”

A nan darasi game da qanqan da kai na Annabi (SAW) ya kammala. Yanzu kuma za mu duba: Adalci, Amana, Kamewa Da Gaskiyar Manzon Allah (SAW).

Wato wannan babin zai yi magana kan Adalcin Annabi da Amanarsa da Kamewarsa da gaskiyar maganarsa (SAW). Ma’anar adalci shi ne rashin cutar da wani na tauye masa haqqinsa ko kuma adalci shi ne bawa mutum haqqinsa kai kuma ka karvi haqqinka ba tare da ka qara fiye da haqqinka ba.

Amana ita ce kiyaye kayan abin da aka ba ka ajiya, ko na magana ko na kuxi ko na muqami ko na karatu.

Kamewa, ita ce kore sha’awa, duk abin da zuciya take so wanda zai zubar da mutunci, a barshi. Amma kamewa an fi faxar ta a wurin kiyaye farji, Mutum ya yi aure ya kiyaye al’aurarsa da mutuncinsa.

Adalcin Annabi (SAW) da Amanarsa da kamewarsa da gaskiyar harshensa, ya kasance shi ne mafi tsananin adalci da amanar mutane, shi ne mafi kamewar mutane, shi ne mafi gaskiyar mutane tun yana xan qaraminsa, maqiyansa suka tabbatar masa da duk waxannan siffofi, shi suke kawo wa amana, in ana so gaskiya ta bayyana shi ake nufa, tun kafin a aiko shi da Annabta ake kiransa da “Al’aminu – Amintacce”.

Ibn Ishaq, Malamin Tarihi yana cewa, Annabi (SAW) ya kasance ana kiransa da Amintacce sabida kyawawn xabi’un da Allah ya sanya a jikinsa, Allah tabaraka wata’ala ya ce “Muxa’in samma amin – ¬abin yiwa biyayya ne a Sama sannan kuma abin amincewa da Wahyi ne a Qasa” da yawan Malamai sun tafi cewa, wannan Ayar tana magana ne da Annabi (SAW), sai dai akwai wasu daga cikin masu fassara, sun tafi cewa, wannan Ayar tana magana ne a kan Mala’ikah Jibrilu.

Yayin da Quraishawa suka samu savani kan qabilar da za ta xora Hajril Aswad, suna qoqarin buga yaqi yayin da suka sabunta ginin Ka’abah, tsofaffi daga cikinsu suka ce ba rigima za a yi ba, mu kwana a cikin wancan masallacin kar mu gaya wa kowa buqatarmu, duk wanda ya fara shigowa, to shi zai yanke mana hukunci, kuma duk hukuncin da ya yanke shi kowa zai bi, duka suka amince da wannan shawara, sai gashi Annabi (SAW) ne ya fara shigowa yayin da yake xan shekara 35, shekara biyar kafin Annabta.

Ka’abah a ingantattu­n ruwayoyin Malamai, an gina ta sau 12:

1. Mala’iku a dai-dai saitin Baitul Ma’amuri

2. Annabi Adam (AS), shi ne wanda Allah ya saukar masa da Hajril aswadi da Maqamu Ibrahim, Yaqutu ne na Aljannah da suke haska masa garin Makkah in dare ya yi

3. Annabi Shisu Xan Adamu

4. Annabi Ibrahim da xansa Isma’ilu

5. Larabawan Jurhum

6. Amaliqawa bayan rasuwar Annabi Isma’ila, su suka qwace garin, suka sake gina Ka’abah

7. Qusayyu bin Kilab (Quraishu)

8. Quraishawa – Annabi yana xan shekara 35 saura shekara biyar a aiko shi.

9. Abdullahi bin Zubair – Xan Asma’u binti Abibakr

10. Hajjaju bin Yusuf, bayan ya kashe Abdullahi bin Zubair 11.Sulxanul Maradiy – Gwamnan

Daular Usmaniyya

12. Sarki Fahad – wannan ginin da yake yanzun (2023) a Makkah. An karva daga Rabi’u xan Husaini ya ce, Annabi (SAW) ya kasance ana kawo qara wurinsa a Jahiliyya.

Quraishawa suna son shi, sun yarda da shi sabida amanarshi amma yana zuwa da Musulunci suka ce sam ba haka ba. Manzon Allah (SAW) ya ce, Wallahi ni amintacce ne a Sama kuma amintacce ne a kan Qasa.

An karvo Hadisi daga Sayyadina Aliyu cewa, Aba Jahlin ya ce wa Annabi (SAW) “Mu ba ma qaryataka sai dai muna qaryata abin da kazo da shi” sai Allah ya faxa cewa “fa’innahum la yukazzibun­aka

An karvo Hadisi daga Sayyadina Aliyu cewa, Aba Jahlin ya ce wa Annabi (SAW) “Mu ba ma qaryataka sai dai muna qaryata abin da kazo da shi” sai Allah ya faxa cewa “fa’innahum la yukazzibun­aka, walakinnaz zalimina bi’ayatillahi yajhadun – lallai ya rasulallah­i ba kai suke qaryatawa ba, ayoyin Allah suke qaryatawa.” qila an ce, Aknasu Ibn sharafin (shugaba ne a qabilarshi, sun fito su 200 amma da ya ji an ce, Abu Sufyan ya tsira da kayan kasuwancin­su sai ya noqe ya gudu, ), ya haxu da Aba Jahlin da Daddare ranar Badr, ya ce Ya Abal hakam (Abu Jahlin Annabi (SAW) ya ke kiranshi) babu wani a nan da yake jin maganarmu, da gani sai kai “Faxa min gaskiya kan Muhammadu, Mai gaskiya ne ko mara gaskiya?” sai ya ce “Wallahi Muhammadu mai gaskiya ne kuma bai tava qarya ba!” sabida jin wannan gaskiyar, ya shawarci Abu Jahlin da kar ya yi yaqi amma ya yi girman kai shi kuma Aknasu ya juya da rundunarsa zuwa gida.

Sabida wannan Hikima da ya yi, ya tseratar da Qabilarsa daga hallaka, ba a kashe su a yaqin Badr ba. Malamai sun rahoto cewa, Sarki Aknasu ya musulunta da qabilarsa daga baya.

Dauloli biyu manya masu qarfin soji da tattalin arziki a wannan lokaci guda biyu ne, Farisa da Rum, kusan kowane lokaci cikin yaqi suke, Farisa ta samu rinjaye bayan shekaru bakwai sai Rum ta samu rinjaye, Qaisarar Rum ya yi alqawarin zuwa xakin Allah da ke Baitul Maqdisi a qafa don Godiya ga Ubangiji kan nasarar da yasamu a kan Farisa, a dai-dai wannan lokaci kuma Annabi (SAW) ya bayyana ya tura da wasiqa zuwa

Sarkin Hira shi kuma ya kai ma Qaisara. Sai aka haxu da Sarkin Hira da Qaisara da xan aiken Annabi (SAW) (Duhyatul kalbi) a garin Baitul Maqdisi.

Sarki Qaisara ya tura a nemo masa dangin Annabi (SAW) da suka zo Baitul maqdisi kasuwanci, sai aka zo da su, Abu Sufyan yana jagorantar tawagar Quraishawa, bayan shigarsu fadar Qaisara sai ya fara tambayar wanda shi ne makusancin Annabi (SAW) – Abu Sufyan.

Hiraqlu – Sarkin Rum na wannan lokaci, ya tambayi Abu Sufyan da cewa, kun tava tuhumarsa da qarya, Abu Sufyan ya ce, A’a, duk abin da ya tambaye ni ina ba shi amsa ta gaskiya sai abu xaya da na yi zanba a ciki, Abu Sufyan ya ce wa sarki ba sa tuhumar Annabi (SAW) da laifin komai sai dai ya faxa mana wata magana da mun rasa yadda za mu yi da ita. Sarki ya ce, wacce magana ce? Wata rana ya ce mana ya zo wannan gari kuma ya koma duk a dare xaya. Kuma mun san wannan tafiyar wata biyu ce zuwa da komawa, Ikon Allah, mai gadin Masallacin yana kusa, sai ya gasgata maganar Annabi (SAW), ya ce “A wannan daren, na kulle duk qofofin Masallacin amma xaya ta qi rufuwa, na kira Mutane su taya ni amma ta qi rufuwa, sai aka ce a bari da safe a kira magina su gyara qofar, da safe sai na ga alamar mutum ya shigo ya yi Sallah a ciki kuma na ga alamar huji a jikin bangon da Annabawa suke qulle abin hawansu in sun zo masallacin, sai na tabbatar cewa, lallai wani Annabi ya shigo masallacin”. Don haka, Rumawa babu abinda ba su sani ba game da Annabta.

 ?? ??
 ?? ??

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria