Leadership Hausa

Amfanin Gona Takwas Da Ake Saurin Girbewa Cikin Wata Shida

-

Ana samun amfanin gona da dama a Nijeriya waxanda ake shukawa su kuma girma a cikin ‘yan watanni. Kazalika, mun yi muku nazari kan amfanin gona guda takwas da ake girbewa cikin watanni shida ko qasa da haka.

Ga gonar jerin kamar amfanin haka:

Waken Suya: Waken Suya na xaya daga cikin amfanin gona masu gina jikin xan Adam, yana kuma xauke da sanadarin ‘protein’. Kamar yadda aka sani, ana dafa Waken Suya sannan ana sarrafa busashensa a yi Madara, Fulawa, Awara da sauran nau’ikan abinci.

Haka nan, ana kuma sarrafa shi zuwa Mai, sannan ana kuma ciyar da dabbobi da da shi. Bayan an shuka Irin sa, ana girbe shi daga wata uku zuwa biyar, amma ya danganta da irin yanayi da kuma nau’in Irin nasa da aka shuka.

Shinkafa: Irin Shinkafa da ake shukawa na kaiwa daga watanni Uku zuwa biyar kafin ta girma. Kazalika, tana da saurin yin girma tana kuma kaiwa tsawon qafa uku bayan kwanaki 120, wanda ya yi daidai da lokacin girbe ta, tana kuma samun karvuwa a kasuwannin Nijeriya yadda ya kamata.

Masara: Masara na xaya daga cikin amfanin gona da ake yin amfani da ita a matsayin abinci a Nijeriya, sannan ana kuma gasa ta domin ci tare da sarrafa ta zuwa Gurguru. Har wa yau, ana kuma sarrafa ta zuwa fulawa da sauran makamantan­su tare da sarrafa ta zuwa abincin dabbobi.

Akasari kafin a girbe ta, tana kaiwa kwanaki 60 zuwa 100 bayan an shuka ta. Kazalika, cikin sauqi ake mallakar gonar da ake shuka Masara a Nijeriya, ana kuma shuka Irinta sannan a sayar da ita ga maqwabta.

Dankali: Dankali na xauke da sinadarin ‘calories’ xan kaxan, sannan mutane da dama na qasar nan na sarrafa shi a matayin abinci tare da yin amfani da shi. Yana xaukar watanni biyu zuwa uku bayan an shuka shi. Bugu da qari, ana iya shuka shi a kowacce irin qasar noma.

Tumatir: Ana matuqar amfani da tumatir a Nijeriya, ko xanyensa ko kuma busasshe. Yana xauke da sanadarin ‘vitamin C’, yana kuma taimakawa wajen rage kamuwa da cututtuka kamar waxanda ke yi wa zuciya illa, ciwon siga da kuma cutar daji.

Ana son a shuka Irinsa a qasar noma mai kyau tare da yi masa ban ruwa. Bayan an shuka Irin nasa, ana fara girbe shi daga watanni 2 zuwa 3, ya danganta da nau’in Irin da aka yi amfani da shi wajen shukawa.

Kankana: Duk yayin da aka shuka Irin Kankana, cikin xan gajeren lokaci ake girbe ta. A Nijeriya, daga wata 3 ake fara girbe ta, sannan ana iya shuka Irinta a kowanne vangare na faxin wannan qasa. Wakazalika, kankana na xauke da sinadarin ‘vitamin A’ da kuma ‘vitamin C’ mai yawan gaske.

Tattasai: Bayan shuka Irin tattasai, ana girbe shi cikin watanni uku kacal. Kazalika, ana iya cewa kusan kowane gida a faxin Nijeriya na yin amfani da shi. Ana kuma sayar da tattasai a kasuwanni da dama a wannan qasa, sannan waxanda ke yin sana’arsa na matuqar samun rufin asiri ko kuxaxen shiga. Hatta a bayan xakin gidanka, za ka iya shuka Irin Tattasai ya girma ya kuma bayar da abin da ake so.

Kokumba: Kokumba na xaya daga cikin sanannin kayan marmari ko lambu, ana kuma yin noman sa a wurare da dama na faxin Nijeriya. Wasu na cin sa tsurarsa, domin alfanun da yake da shi musamman a fannin kiwon lafiya. A duk lokacin da aka shuka Irinsa yana da matuqar saurin yin girma, ana kuma girbe shi bayan aqalla watanni 3. Sannan yana da saurin tafiya a kasuwa, ma’ana mutane suna son sa qwarai da gaske sakamakon amfaninsa ga lafiyar xan Adam.

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria