Leadership Hausa

An Qaddamar Da Shirin Baje Kolin Inganta Harkar Noma Da Sana'o’i A Kano

- Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

An bayyana shirin Gwamnati Na Kano CARRES da cewa shi ne shirin da yafi sauran shirye shiryen da ake bijiro dasu da sunan tallafin sauqaqawa jama'a raxaxin matsin rayuwa da jama'a ke fama da ita tun bayan faruwar Annobar Korona wadda tayi sanadin durqushewa­r tatalin jama'a. Shugaban Hukumar Kano CARES na Jihar Kano Alhaji Rufa'I ne yabayyana haka alokacin da yake zagawa da babban sakataren ma'aikatar gona na Jihar Kano Alhaji Salisu Tahir alokacin shirin da ake na qaddamar da tallafin kayan Noma ga xaruruwan matasa maza da mata a Jihar Kano.

Alhaji Rufa'I ya shaidawa Babban sakataren Ma'aikatar gonan na jIhar Kano cewar wannan hukuma ta himmatu kamar yadda aka bata cikin kudin tsare tsaren wannan hukuma na samar da tallafi kamar bayar da injunan niqa, injin malkaxe, injin ban ruwa mai amfani da hasken rana, kiwon Kaji, samar da hanyoyi a karkara da kuma gina wuraren kewayawa a kasuwanni da wuraren taruwar al'umma.

Hakazalika shugaban hukumar ta Kano CARES ya bayyanawa mahalarta taron irin yadda majalisar mahaddata alqur'ani suma suka shigo cikin tsarin, musamman ganin suna da kyakkyawan shirin rage kwararar almajirai daga kauyuka zuwa manyan birane tare da qoqarin magance matsalar barace barace wadda a halin ke neman zama wata barazana a jihar Kano, don haka sai ya tabbatar da cewa yanzu haka shirye shirye sunyi nisa na sake samar da wani rukunin al'umma da suma ake fatan zasu rabauta da wannan tallafi da Gwamnatin Kano ke saukewa al'ummarta.

Da yake jawabi alokacin da yake ganewa idonsa irin kayayyakin da hukumar ta samar domin rabawa al'umma musamman abinda ya shafi noma, kiwo da sana'o'in dogaro da kai, Dakta Farouk Kurawa ya bayyana farin cikinsa tare da jinjinawa qoqarin wannan hukuma wadda yace babu shakka ya fahimci yadda jama'a ke alfahari da ayyukan wannan hukuma ke nuni da kyakkyawan alhairan da ke qunshe cikin manufofi da aikace aikacen hukumar ta Kano CARES.

Shima da yake duba kayayyakin da hukumar Kano CARES ta tanada domin ci gaba da rabawa jama'a, babban sakataren ma'aikatar gona na Jihar Kano Alhaji Salisu Tahir ya nuna gamsuwa da irin kalaman da yaji daga bakin waxanda suka amfana da alhairan wannan hukuma ta Kano CARES, musamman kan batan smaar da hanyoyi a karkara, inda wasu da suka amfana daga Qananan Hukumomi Gazawa da

Kura suka bayyana farin cikin al'umarsu bis aaikin hanya da wannan hukuma ta shimfaxa masu a yankunansu.

Alhaji Salisu Tahir ya jinjinawa qoqarin shugabanni­n hukuma tare da roqonsu da su qara himma wajen sauke nauyin da aka xora masu, sannan kuma ya buqaci waxanda suka amfana da waxanann tallafi iri daban daban da suyi kyakkyawan amfani dashi, domin ganin nan gaba kaxan suma sun zama suna cikin waxanda da za su taimaka wa sauran al'umma. A qarshe ya yi addu'ar Allah ya sawa damunar mu albarka.

 ?? ??

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria