Leadership Hausa

Abubuwa Takwas Da Gwamnatin Tinubu Za Ta Bai Wa Fifiko

- Edita: 0803921637­2 , abdulrazak.yahuza@leadership.ng Daga Yusuf Shuaibu RAHOTANNI SHARHI WAIWAYE TATTAUNAWA

Shugaban Qasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana abubuwa guda takwas da gwamnatins­a za ta fi bai wa fifiko wajen bunqasa tattalin arziki da zai inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

Ministan Kuxi kuma ministan da ke kula da harkokin tattalin arziki, Wale Edun, ya gabatar da tsarin taswirar tattalin arziki, wanda aka yi la'akari da shi a farkon babban taron majalisar zartarwa ta tarayya da ya gudana a wannan mako.

Edun wanda ya bayyana wa manema labarai na gidan gwamnati ajandar da suka haxa da samar da abinci, kawo qarshen talauci, bunqasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi, damar samun babban jari, inganta tsaro, inganta filin wasan da mutane da kamfanoni za su yi aiki, inganta tsarin dokokin qasa, da yaqi da cin hanci da rashawa.

Ya ce majalisar zartarwa ta yi nazari a kan abubuwa takwas da suka fi ba da fifiko tare da gano abubuwan da za a cimma a cikin shekaru uku masu zuwa.

Edun ya ce shugaban qasa ya bai wa ministoci umurnin kan su fitar da manufofi da shirye-shirye a cikin makonni don inganta tattalin arzikin qasa tare da kyautata al'amura ga dukkan 'yan Nijeriya.

Edun ya ce majalisar ta amince da cewa tattalin arzikin bai kai inda ya kamata ba.

Game da batun alqiblar majalisar zantarwar ta dosa kuwa, ministan ya ce, “Tun da farko Shugaba Tinubu ya taya kowa murna tare da jaddada babban abin da ‘yan Nijeriya suke buqata, sannan ya karfafa muna gwiwa wajen jajircewa da kuma gudanar da yin aiki cikin gaggawa wajen samar da ingantacci­yar rayuwa ga ‘yan Nijeriya. Tun da farko, mun gudanar da wani atisaye na duba inda al’amura suka tsaya dangane da tattalin arziki, hauhawar farashin kayayyaki, hauhawar farashin kuxaxin waje, rashin aikin yi da sauransu.

“Babban abin da ya dace shi ne, ba inda ya kamata mu kasance ba, mun kuma yi nazari a kan batutuwa takwas da shugaban qasa zai mayar da hankali a kansu, wato abubuwa takwas da za mu saka a gaba wajen ciyar da tattalin arzikin Nijeriya gaba waxanda suka haxa da samar da abinci, kawo qarshen talauci, bunqasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi, samun jari, musamman wajen samar da bashi, haxa kai ta kowane fanni, musamman matasa da mata, inganta tsaro, inganta wuraren zuba jari, bin doka da oda da kuma

yaqi da cin hanci da rashawa. Wannan shi ne ainihin abin da tattaunawa­r ta kasance.”

Edun ya ce gwamnatin Tinubu ta gamu da mummunan yanayin tattalin arziki tare da hauhawar farashin kayayyaki na kashi 24 cikin 100 da kuma matsananci­n rashin.

Tun da farko a wajen qaddamar da taron majalisar zartarwar, Tinubu ya hori ministocin da su duba girman muqamin da ofisoshins­u tare da mayar da hankali kan ayyukan da ke gabansu domin kawo sauyi ga tattalin arzikin qasar nan.

 ?? ?? •Shugaban Qasa Tinubu
•Shugaban Qasa Tinubu

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria