Leadership Hausa

Atiku Ga Tinubu: Faɗa Wa ‘Yan Nijeriya Yadda Ka Samu Digiri Ba Tare Da Firamare Da Sakandare Ba

Hadari Gabas…

- Daga Yusuf Shuaibu Daga Yusuf Shuaibu

Xan takarar shugaban qasa na jam’iyyar PDP a zaven 2023, Atiku Abubakar, ya sake caccaki takardun makarantar Shugaban Qasa Bola Ahmed Tinubu.

Atiku ya qalubalanc­i sahihancin takardar shaidar digirin Tinubu da jami’ar Chicago ta Amurka ta bayar, ya ce karatun shugaban qasar na ci gaba da zama babbar abun tantama.

A wani sako da ya wallafa ta shafinsa na Tuwita, Atiku ya zargi shugaban qasar da kaurace kawo takardun karatunsa na firamare da sakandare amma sai ya kawo na digiri daga jami’ar Chicago.

A cewar tsohon mataimakin shugaban qasar, a shekarar 1999, Tinubu ya yi iqirarin cewa ya halarci makarantar firamare ta St. John’s da ke Aroloya a Legas, kafin ya wuce makarantar ‘Children’s Home’ da ke Ibadan.

Ya yi zargin cewa shaidar karatun Shugaba Tinubu a 2023 ya sha bamban da wanda aka gabatar a shekarar 1999, inda ya qara da cewa shugaban qasar ya ce ya halarci jami’ar Chicago ba tare da karatun firamare da sakandare ba.

“Na farka da safiyar yau ina mamakin yadda muka sami wannan lamari. A cikin 1999, Tinubu ya yi iqirarin cewa ya halarci makarantar firamare ta St. John da ke Aroloya a Legas, kafin ya wuce zuwa makarantar ‘Children Home’ a Ibadan.”

“A cewarsa, ci gaba da karatu kwalejin gwamnati ta Ibadan da kwalejin Richard Daley da jami’ar Chicago ta Amurka.

"Abin mamakin shi ne, a 2023, Tinubu ya ce shi dai kwai ya halarci jami’ar Chicago kaxai. Ina ta mamakin ko ta yaya hakan zai yiwu? Yana tunanin cewa ’yan Nijeriya ba za su shiga ruxani ba kamar yadda na shiga cewa, Tinubu ba shi da takardar firamare da sakandare amma ya yi digiri a jami’a. Kuna iya tambayar Tinubu yadda ya samu wannan nasarar domin mu yi koyi da hazaqarsa," Atiku ya rubuta.

A watan Maris ne aka ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaven shugaban qasa na 2023. Amma Atiku ya ci gaba da qalubalant­ar sakamakon zaven a kotun sauraron qararrakin zaven shugaban qasa, inda ya qalubalanc­i sahihancin takardun makarantar shugaban qasa.

Ya kuma garzaya wata kotun Amurka da ke gundumar Arewacin Jihar Illinois a Chicago, domin neman tilastawa jami’ar Chicago sakin bayanan karatun Tinubu.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Abubakar ya buqaci malamai da su riqa shawartar masu mulki kan shugabanci nagari.

Sarkin Musulmin ya yi wannan kiran ne a Abuja wajen taron bitar ga malaman addini kan harkokin kiwon lafiya a matakin farko.

Kamfanin dillancin labara na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa ma’aikatar lafiya da jin daxin jama’a ta tarayya tare da haxin gwiwar hukumar kula da lafiya matakin farko ta qasa (NPHCDA) ne suka shirya taron.

Sarkin Musulmi ya ce yana da kyau malamai su kasance masu gaskiya da riqon amana a yayin da suke da kusanci da shugabanni­n siyasa.

“Shugabanni­n addini sukan riqe muqamai masu gwavi kuma suna iya kawo sauyi ga rayuwar al’umma.

“Ta hanyar ba da shawara ta gaskiya ne za a iya samun ingantacci­yar shugabanci da zai ba da gudummawa ga rayuwar al’ummarsu gaba xaya.

“Kyakkyawan sadarwa tsakanin malamai da shugabanni­n siyasa na iya haifar da fahimtar juna, haxin kai da kuma cimma manufofin da aka saka a gaba.

"A duk lokacin da malamai ke faxa wa masu mulki gaskiya, zai taimaka wajen yanke hukunci da manufofi waxanda suka dogara a kan ingantattu­n bayanai da suka dace da xabi’u da qa'idodi," in ji shi.

Shi ma shugaban qungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) Archbishop Daniel Okoh, ya buqaci qarin haxin kai da hukumar kula da lafiya matakin farko ta qasa domin inganta harkokin kiwon lafiya musamman a yankunan karkara.

Okoh, wanda ya bayyana muhimmiyar rawar da malaman addini suke takawa wajen bayar da shawarwari da wayar da kan jama’a, ya ce dole ne a haxa kai da shugabanni­n siyasa domin inganta harkar kiwon lafiyar qasar nan.

Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ya yaba wa gudunmawar da malamai ke bayarwa wajen samar da kiwon lafiya a qasar nan.

Ministan ya jaddada mahimmanci­n haxin gwiwa tsakanin gwamnati da malaman addini.

Pate ya ja hankali kan yadda fannin kiwon lafiya ke ci gaba da bunqasa, ya ce akwai buqatar yin haxin gwiwa a tsakanin ma'aikatan kiwon lafiya da malamai.

"Ta hanyar haxin kai ne za a samu damar ilimantar da juna da kuma sanar da jama'a game da abubuwan da ke faruwa, za mu tabbatar da cewa an samar da ayyuka masu inganci na kiwon lafiya ga 'yan Nijeriya," in ji shi.

Babban daraktan hukumar NPHCDA, Dakta Faisal Shuaib, ya yi kira ga malamai da su ba da himma gudunmuwa wajen inganta harkokin kiwon lafiya a matakin farko da kyautata jin daxin al’umma.

"Manufar wannan taro na musamman shi ne, rigakafin cutar kansa ta mahaifa ta hanyar allurer HPV," in ji shi.

Ya buqaci shugabanni­n addini da su bayar da shawarwari­n rigakafi a cibiyoyins­u.

Shugaban NPHCDA ya jaddada qarfin haxin kai da aiki tare wajen inganta lafiya da walwalan al’umma.

Ya ce ta hanyar haxa kai ne malamai da ma’aikatan kiwon lafiya za su bayar da gudummuwa ga harkokin lafiya da kuma ci gaban qasa.

NAN ta ruwaito cewa taron ya samu halartar malaman addini, ma’aikatan lafiya da masu ruwa da tsaki kan harkokin lafiya da manyan jami’an gudanarwa na ma’aikatar lafiya da NPHCDA.

Taron dai an yi shi ne domin qara inganta fahimtar malamai game da allurar rigakafi da sauran shiryeshir­yen kiwon lafiya tare da wayar da kan al’umma kan amfanin rigakafin.

 ?? ?? •Atiku Abubakar
•Atiku Abubakar
 ?? ?? •Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III
•Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria