Leadership Hausa

‘Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu A Mulkin Tinubu — PDP

- Daga Yusuf Shuaibu

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya na xanxana kula luransu a qarqashin jagorancin Shugaban Qasa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.

A wata sanarwa da babban sakataren yaxa labarai na jam’iyyar na qasa, Debo Ologunagba ya fitar a ranar Litinin da ta gabata, cewa babbar jam’iyyar adawar ta koka kan yadda Nijeriya ta shiga tsaka mai wuya a qarqashin jam’iyyar APC da Tinubu yake jagoranta, wadda ba ta damu da ‘yan qasa ba, al’amarin da ya haifar da yanayi na rashin nagartacce­n shugabanci a qasar nan.

Sanarwar ta qara da cewa, “Jam’iyyar ta firgita da yadda aka samu rashin jituwa mai tsanani tsakanin gwamnati da ‘yan qasa sakamakon rashin tsari da kuma gaggawar aiwatar da manufofin da suka kawo wahalhalu mai tsanani, rashin tsaro da kuma fargabar da tuni ke barazana ga zaman lafiyar al’umma da haxin kai da wanzuwar qasar nan.

“Rashin wayo ne da sanin ya kamata da gwamnati ta yi wajen cire tallafin man fetur da karya darajar naira wanda ya janyo tsadar rayuwa da ya gurgunta mana tattalin arzikin qasa, sannan ya durqusar da miliyoyin ‘yan kasuwa tare da jawo asarar ayyuka masu dimbin yawa da qaruwar talauci da yunwa da rashin tsaro a fadin kasar nan.

“Lmarin ya janyo mummunar asarar ga masu saka hannun jari tare da ficewar kamfanonin tare da barin miliyoyin ‘yan Nijeriya neman aikin yi da gurgunta masu qanana da matsakaita­n masana’antu waxanda su ne ainihin ginshiqan tattalin arzikin qasarmu.

“Abin ban tsoro ne cewa a cikin watanni biyun da suka gabata, sama da ‘yan Nijeriya miliyan 150 ba za su iya ciyar da iyalansu abinci ba, inda suke kwana da yauwa.

“Abin takaici ne yadda gwamnatin APC ke ci gaba da yaudarar ‘yan

Nijeriya da bayar da tallafi na raba buhunan shinkafa 1,200 ga mutane a kowace jiha. Jam’iyyar APC ta faxaxa qarfinta na yaudara da damfarar ‘yan Nijeriya ta hanyar shirye-shiryen marasa amfani."

PDP ta bayyana damuwata game da abin da ta lura akwai rashin tausayi, damuwa da raba kan ‘yan qasa, idan ba a yi gaggawar magance lamarin ba zai iya harfar da mummunan rikici."

Ta kuma buqaci ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankalinsu su kasance masu bin doka da oda da kuma mara wa juna baya a qoqarinsu na samar da qasa mai tsaro da ci gaban tattalin arziki.

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria