Leadership Hausa

Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Wani Limami A Abuja Da Sanata Ndume 6 Ga Satumba

- Daga Sani A. Anwar

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta xage shari’ar da ta ke sauraro har zuwa 6 ga watan Satumbar wannan shekara da muke ciki, wadda wani Limamin Masallacin Juma’a mai suna Imam Ibrahim Lawan ya shigar gabanta, inda yake zargin Sanata Ali Ndume da Mansur Jarkasa, a matsayin waxanda ke da hannu wajen tura guggun matasa ‘yan ta’adda su ci zarafinsa tare da yi masa mummunan rauni. Kazalika, ya zargi waxanda yake qarar da cewa, sun haxa ayarin ‘yan ta’addan ne da nufin hallaka shi, a masallacin da yake gabatar da Limanci na ‘Yan Majalisu a Apo da ke Zone B cikin Birnin Tarayya Abuja.

Kafin mai shari’a M. Muazu ya kai ga tsayar da ranar yanke hukuncin, ya baiwa Lauyan da ke kare waxanda ake zargin, wato Sanata da Mansir Jarqasa da kuma Jami’in ‘Yansanda (CSP) Ibeh Chukwudi, damar qalubalant­ar qarar da aka shigar a gaban Kotun.

Kafin nan, an gabatar da shaidar da matar Limamin ta bayar mai suna Shamsiyya, inda ta bayyana cewa a ranar 16 ga watan Yunin 2023, Ndume ya yi sallah a wannan masallaci, ana kuma idarwa ne sai ya tashi ya fice daga masallacin a fusace, bisa zargin nasihar da Liman zai gabatar, ta shafe shi ne kai tsaye.

Ta qara da cewa, “wanda a wannan lokaci, Liman ya yi kira kai tsaye ne tare da nusasshe da mutane a kan muhimmanci­n neman ilmi tare da aiki da shi, bisa koyarwar Alqur’ani da bin sunnar Annabi Muhammad SAW. Amma sai ga shi daga bisani Sanata ya dawo wannan masallaci yana kumfar baki da zage-zage tare da cin zarafinsa.”

Kamar yadda yake a rubuce a Kotu, wannan Uwargidan Liman ta haqiqance cewa, ranar Lahadi wadda ta yi daidai da 18 ga watan Yunin wannan shekara, Maigidan nata (Liman) yana haramar tayar da Sallar La’asar a matsayinsa na Babban Limamin Masallacin, sai Ndume da Jarkasa tare da rakiyar guggun wasu mutane, suka fizge lasifiqar da ke hannunsa suna kuma yi masa gargaxi cewa, an dakatar da shi a matsayinsa na Babban Limamin wannan masallaci.

“Ganin faruwar hakan ya yi matuqar ba shi mamaki da al’ajabi, inda ya dage sai ya aiwatar sallar abinsa kamar yadda ya saba, amma sai wani daga cikin dattawan masallacin ya ba shi shawara tare da jan hankalinsa nacewan ya yi haquri ya fice daga masallacin don gudun tashin hankali, nan take ya xauki wannan shawara ya kuma fice daga masallacin,” in ji ta.

A cewar tata, ganin haka ne yasa Maigidan nata ya garzaya Ofishin ‘Yansanda na Apo, don shaida musu abin da ke faruwa domin gudun abin da ka je ya zo. Dawowar sa ke da wuya, “kafin ya ankara, gungun wasu matasa ‘yan ta’adda qarqashin jagorancin Sanata Ndume da Jarkasa, suka far masa tare da dukan sa babu ji babu gani, wanda hakan ya yi sanadiyar samun mummunan rauni a kansa.”

Wannan dalili ne ya sa, Lauyan mai qara (Liman), Al-bashir Lawal Likko, ya nemi wannan Kotu da ta dubi irin wannan cin zarafi da keta haddi da zalinci da kuma mummunan raunin da aka yi wa wannan mai qara, wanda ko shakka bau ya sava wa doka da kuma kundirin tsarin mulkin wannan qasa, a yi masa adalci tare da qwato masa ‘yanci na wannan mummunan zalinci da aka yi masa.

Lauyan ya qara da cewa, lokacin da aka shigar da rahoto a Ofishin ‘Yansanda na Apo, wanda yake karewa (Liman) da wasu waxanda ke tare da shi, sai aka bi su duka aka kame wai da sunan masu qoqarin tayar da tarzoma a tsakanin al’umma, aka kuma gurfanar da su a Kotun Magistiri da ke Abuja.

Sai kuma a vangaren waxanda ake qarar, ma’ana Sanata Ndume da Jarkasa, Lauyansu Ben Jones Akpan, ya nemi Kotun ta yi watsi da qara a matsayin wani batu mara tushe da kan gado.

Har wa yau, ya bayyana wa Kotun cewa tuni kwamatin wannan masallaci ya dakatar Limamin, sakamakon zargin sa da ake yi da rashin gudanar da al’amuran masallacin yadda ya kamata da kuma barin waxanda ba su dace ba, marasa kuma alaqa da masallacin su riqa kwana a ciki, wanda hakan ya sava wa dokar masallacin.

Yanzu haka dai, Kotun ta xage shari’ar tare da tsayar da ranar 6 ga watan Satumbar wannan shekara a matsayin ranar yanke hukuncin. Inda mai qarar ke ci gaba da ikrarin cewa, yana nan a kan bakarsa na qoqarin neman haqqinsa, babu gudu babu ja da baya.

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria