Leadership Hausa

Halin Da Ɗakin Karatu Na Kashim Ibrahim Ke Ciki A Yanzu —Malam Gambo

- Daga Idris Umar Zariya

Xakin karatu na Kashin Ibrahim da ke jami'ar Ahmadu Bello a Zariya cikin Jihar Kaduna, na xaya daga cikin xakuna karatu mafi girma a Nijeriya, sai dai kuma a halin yanzu yana cikin wani hali.

Wakilinmu ya samu nasarar zantawa da babban muqaddashi­n shugaban da ke kula da xakin karatu na Kashim Ibrahim, Malam Abdulhamee­d Gambo Liman, inda ya bayyana nasarori da kuma qalubalen da xakin karatun ya samu.

Malam Abdulhamee­d ya ce, "Lallai muna da abin faxi a kan ci gan da xakin karatunmu yake samu tare da qalubalen da yake fuskanta a halin yanzu.

"Ka san ko Bahaushe na cewa, ‘idan kixa ya canza, to dole rawa ta canza’. Sakamakon ci gaba na zamani da aka samu, dole ta sa muka koma rungumi zamani, wanda ya sa muka buxe wasu sassa waxanda da ba su, misali kamar rassan fasahar sadarwa (ICT). Muna samun jaridu ta e-paper, e-informatio­n, e-Library da dai sauransu.

“Mutun zai iya karanta littafai ta hanyar yanar gizo, kuma abin mamaki za ka ga duk inda kake a duniya muddin kana da damar shiga lambobin sirri na wannan xakin karatunmu. Ka ga wannan wani abu ne wanda da ba a san shi ba. Yanzu ina tabbatar maka in za ka samu ‘login details’ ba inda ba za ka iya kama mu ba a duniya, saboda haka muna tafiya daidai da zamani.”

Binciken da wakilinmu ya yi ya tabbatar da cewa xakin karatu na Kashim Ibrahim a lokaci guda yana xaukar xalibai sama da dubu huxu.

“Muna samun qalubale ta vangaren wasu malamai da wasu xalibai wajen amfani da wannan xakin karatu. Sai dai muna qoqarin ilimantar da su, sannan muna samun ci gaba ta hanyar samun goyon baya da karfafa gwiwa daga shugaba namu wato mataimakin shugaban wannan jami'a, Farfesa Kabiru Bala.

 ?? ?? •Muqaddashi­n Shugaban xakin karatu na Kashim Ibrahim, Malam Abdulhamee­d Gambo Liman
•Muqaddashi­n Shugaban xakin karatu na Kashim Ibrahim, Malam Abdulhamee­d Gambo Liman

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria