Leadership Hausa

Taron LEADERSHIP Da NDLEA Zai Gudana Ranar 7 Ga Nuwamba

- Daga Yusuf Shuaibu

Babban taron LEADERSHIP tare da haxin gwiwar hukumar yaqi da sha da fataucin miyagun qwayoyi ta qasa (NDLEA) kan yaqi da ta’ammuli da miyagun qwayoyi da aka xaga zai gudana a ranar 7 ga watan Nuwamba.

A cikin wata sanarwa da LEADERSHIP ta fitar, kamfanin ya ce a yanzu za a gudanar da taron ne a ranar Talata 7 ga watan Nuwamba, 2023 a cibiyar ‘Yar’Adua da ke Abuja.

Tun da farko dai an saka ranar 3 ga Agusta a matsayin ranar gudanar da taron, amma sakamakon wasu uzuri ya sa aka xage taron.

Sanarwar ta ce, "Muna matuqar godiya da goyon baya da fahimtar abokan aikinmu da waxanda za su kashe kuxaxensu da kuma mahalarta taron, waxanda suka himmatu wajen samun nasarar wannan muhimmin babban taro da zai kawo mafita kan ta’ammuli da miyagun qwayoyi.

“Mun yi farin ciki da cewa daga qarshe mun yanke ranar da za mu yi babban taron. An kuma inganta abubuwan da za su gudana a wurin taron sosai," in ji sanarwar.

Taron mai taken, "Shaye-shayen miyagun qwayoyi, laifuka, rashin tsaro da ci gaban qasa," abun yaba ne da shi a matsayin muhimmin matakin zamantakew­a a wannan lokaci.

LEADERSHIP ta yi haxin gwiwa da hukumar NDLEA da abokan hulxarta waxanda suka amince da xaukar nauyin gudanar da babban taro domin bayyana illolin shaye-shayen miyagun qwayoyi da tasirinsa kan aikata laifuka da ci gaban qasa tare da yin nazari kan hanyoyin magance lamarin.

A binciken da Majalisar Xinkin Duniya ta yi na ta’ammuli da qwayoyi a shekarar 2017, bisa kiyasin al’ummar Nijeriya miliyan 98, ‘yan Nijeriya miliyan 14.3 ne ke ta’ammuli da miyagun qwayoyi da ke illata qwaqwalwa.

Baya ga shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa, akwai mai ba shugaban qasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da kuma babban lauya mai fafutukar kare haqqin Bil’adama, Mista Femi Falana, da sauran su duk za su halarci babban taron.

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria