Leadership Hausa

Wasu 'Yan APC Sun Koka Da Rashin Naxa Masari Minista A Gwamnatin Tinubu

- Daga Yusuf Shuaibu

Wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a shiyyar kudu maso yamma sun nuna damuwarsu kan yadda aka yi watsi da tsohon gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari a cikin gwamnatin Shugaban Qasa Bola Tinubu.

Masu ruwa da tsaki na yankin kudu maso yamma a qarqashin qungiyar ‘4th Tribe Global Movement’ sun yi zargin cewa waxanda ake kira kabal a gwamnatin Tinubu ne suka yi wa Masari makirci duk da biyayya da kuma gudunmuwar kuxaxe da ya bayar na tallafa wa wannan gwamnati a lokacin zaven da ya gabata.

A cikin wata sanarwa da qungiyar ta fitar mai xauke da sa hannun shugabanta, Abayomi Mighty, wanda ta raba wa manema labarai a Legas ta bayyana cewa Masari na xaya daga cikin tsofaffin gwamnonin arewa da suka yi ruwa da tsaki wajen ganin an miqa mulki ga yankin kudu, tare da tsayin daka na ganin an zavi Tinubu a matsayin xan takarar shugaban qasa.

“A rubuce yake cewa Masari na xaya daga cikin tsofaffin gwamnonin arewa da suka goyon bayan miqa mulki ga sashin kudu da kuma mara wa Tinubu baya.

“Ya kuma jagoranci tattaunawa da takwarorin­sa na arewa don mara wa takarar Tinubu baya. Ya raunata ‘yan adawa a Jihar Katsina ta hanyar gudanar da mulki nagari,” in ji Mighty.

Mighty ya bayyana Masari a matsayin cikakken magoyin bayan Tinubu wanda ya yi amfani da dabarar siyasarsa da kuma tasirinsa wajen mayar da Katsina tudun mun tsira ga APC.

Ya qara da cewa ba za a iya lissafa irin gudunmawar da Jihar Katsina ta bai wa Tinubu ba.

A cewarsa, duk da irin qalubalen tsaro da qarancin kuxaxe da ya haifar da ruxani a yayin gudanar da zaven, jam’iyyar APC a Jihar Katsina ta nuna bajinta a zaven 2023.

Masu ruwa da tsakin sun ce, “A sakamakon zaven shugaban qasa, bayanai da hukumar zave mai zaman kanta ta qasa (INEC) ta fitar sun nuna cewa APC ta samu quri’u 482,283, yayin da jam’iyyar PDP ta samu quri’u 489,045.

“Duk da jam’iyyar APC ta yi rashin nasara a zaven shugaban qasa sakamakon ayyukan zagon qasa, amma sai da Masari ya jagoranci jam’iyyar ta lashe dukkan kujerun majalisar dattawa guda uku da kuma majalisar wakilai guda tara cikin kujeru 15.

“A matsayinsa na xan siyasa na asali, ya yi amfani da tasirinsa da kuma dacewarsa wajen haxa ximbin magoya baya domin lashe zaven gwamnan Jihar Katsina.”

Mighty ya jaddada cewa da irin gudunmawar da Masari ya bayar ga nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a zavukan da ya gabata, ya cancanci a ba shi muqamin siyasa a cikin qasar nan.

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria