Leadership Hausa

Fargabar Ambaliyar Ruwa A Jihohi 13 Ta Qaru

- Daga Yusuf Shuaibu

Akwai yiyuwar wasu jihohi a Nijeriya za su fuskanci ambaliyar ruwa nan da kwanaki masu zuwa, yayin da qasar Kamaru ke shirin buxe tekun Lagdo da ke gavar kogin Benuwai.

A cewar hukumar bada agajin gaggawa (NEMA), jihohin sun haxa da Adamawa, Taraba, Benuwai, Nasarawa, Kogi, Filato, Gombe da Bauchi da dai sauransu.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin waje ta fitar mai xauke da kwanan watan Agusta 25, 2023, ta sanar da hukumar NEMA kan wata sanarwa da ofishin jakadancin qasar Kamaru ya fitar a hukumance cewa jami’an sun yanke shawarar buxe mashigar madatsar ruwa tekun Lagdo a cikin kwanaki masu zuwa sakamakon ruwan sama kamar da bakin qwarya a magudanar ruwan da ke yankin Arewacin Kamaru.

“Yana da kyau a sani cewa lokacin fitar da ruwa ya zama dole, hukumomin madatsar ruwa na Lagdo za su fitar da ruwa kaxan ne kawai a lokaci guda don ragewa da kuma guje wa varnar da ruwan da aka saki zai iya haifarwa a bakin kogin Benuwai a Kamaru da Nijeriya

"Saboda haka, za a yaba idan hukuma ta xauki dukkan matakan da suka dace da kuma ayyukan da za su rage varnar tare da wayar da kan jama'ar da ke zaune a irin waxannan wuraren don yin taka tsantsan," in ji ma'aikatar.

Gwamnatin tarayya ta ce mutane 3,219,780 ne ambaliyar ruwan ta shafa a shekarar da ta gabata, wanda ya zuwa ranar 24 ga watan Oktoba, mutane 1,427,370 suka rasa matsugunan­su, 2,776 suka jikkata, yayin da 612 suka mutu.

Masu ruwa da tsaki a ko da yaushe suna danganta barazanar ambaliya daga madatsar ruwa ta Lagdo da gazawar hukumomin Nijeriya wajen qin gina madatsar ruwan Dasin Hausa, wanda ke daura da kogin Benuwai, kamar yadda aka yi yarjejeniy­a a 1982.

A shekarar da ta gabata ne dai tsohon ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu, ya yi zargin cewa Kamaru ba ta sanar da Nijeriya ba game da sakin ruwan tekun Lagdo.

“Ana sakin ruwa a wannan dam a kowani lokaci, kuma idan aka saki ruwan ba tare da sanarwa ba, yana shafar al'ummomin da ke qasar nan.

"Mun yi qoqari sosai mu da su don sanya hannu kan wata yarjejeniy­a na sanar da Nijeriya game da sakin ruwan tekun.

“An sanya hannun a shekarar 2016. Tun daga lokacin, duk shekara idan damina ta kama, duk shekara hukumar kula da ruwan ruwa ta Nijeriya ce ke kiran su don sanin yawan ruwansu.

“Ba za mu iya xora laifin ambaliya a wannan shekarar a kan Kamaru ba. Za mu xora musu laifin karya ka’idojin yarjejeniy­a ne kawai,” Adamu ya fada a lokacin da yake kare kasafin kuxi a majalisar dattawa.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa, a tsawon shekarun da suka gabata, an samu ambaliyar ruwa mai yawa a jihohin qasar nan da dama da ake dangantawa da sakin ruwa daga tekun Lagdo.

Haka kuma an samu varnar ambaliya a shekarar 2022 wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi na biliyoyin naira.

Mai magana da yawun hukumar NEMA, Manzo Ezekiel, ya bayyana cewa sako ruwan tekun Lagdo zai shafi jihohin Adamawa, Taraba, Benuwai, Nasarawa da Kogi da dai sauran su.

“Daga Kogi zuwa Jihar Delta idan aka samu qaruwar ruwa a Jihar Neja zai zama babban qalubale. Wadannan jihohi ne da ke kan kogin kai tsaye, akwai wasu jihohin da abin ya zai shafa saboda an rufe kogin kuma ba su da wurin da ruwa zai ci gaba da kwarara, irin waxannan wuraren ma za a iya ambaliya kamar wasu sassan Gombe, Filato, Bauchi.

"Jihohin farko su ne waxanda ke kan hanyoyin kogin, amma sauran na iya shafa ne sakamakon tasirin ruwan."

Ya ce fitar da ruwa da ya wuce gona da iri daga tekun Lagdo bai zo wa NEMA da mamaki ba kamar yadda hukumar ta yi a shirinta na ambaliyar ruwa na wannan shekara.

Ya ce hukumar NEMA ta sanar da gwamnonin jihohi yiwuwar afkuwar ambaliya, kuma galibinsu sun xauki matakai da suka dace ta hanyar share magudanan ruwa da suka toshe da sauran hanyoyin da ke haifar da ambaliya.

Ya ce hukumar ta kuma shawarci gwamnonin da su ware kuxaxe na musamman domin bala’o’i da suka haxa da ambaliyar ruwa.

Ezekiel ya ce a baya hukumar NEMA ta sha gaya wa jihohin da su kwashe mutanen da ke bakin ruwa zuwa wuraren da ba za su kai ga ambaliyar ruwa a bana ba.

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria