Leadership Hausa

Hukuncin Zaven Gwamnan Kano: Magoya Bayan NNPP Da APC Sun Duqufa Addu'o'i

- Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

A gabanin yanke hukuncin da kotun sauraron qorafe-qorafen zaven da ke zaman ta a Kano, magoya bayan jam'iyyar APC sun bayyana cewa addu'ar da suke ba ta riya ba ce, don haka suka ce ta su ba irin ta sauran ba ce.

Mashawarci na musamman kan harkokin gyaran motoci, Alhaji Idris Hassan ne ya bayyana haka a lokacin taron addu'ar da aka gudanar a unguwar Gwagwarwa da ke yankin qaramar hukumar Nasarawa, inda ya ce magoya bayan jam'iyyar APC suna cikin nutsuwa kuma a wajen Allah suke neman nasara ba wurin kowa ba.

Ya qara da cewa jama'ar Jihar Kano na nadamar abin da ya faru a lokacin zaven da ya gabata, musamman ganin yadda wannan gwamnatin ke yi wa harkokin ci gaban Kano xibar karan mahaukaciy­a.

“Babu shakka mu muna da cikakkiyar tarbiyar da muke mutunta na gaba da mu, muna kira da goya bayan Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakin­sa Alhaji Murtala Sule Garo su ci gaba da haquri.”

Shi ma da yake gabatar da nasa jawabin a wurin taron addu'ar, tsohon daraktan hukuma Zakka da Khubusi na Jihar Kano, Alhaji Safiyanu Ibrahim Abubakar Gwagwarwa (Tafidan Gwagwarwa), ya bayyana cewa, “Muna tawassili da sunayen Allah mai tsarki da alqur'aninsa, muna kuma da yaqin cewa wanda muke neman a wurinsa wadataccen sarki ne, yana amasa tsarkakkiy­ar addu'ar da ba riya a cikinta, wannan ta sa mu idan za mu yi addu'a tsakaninmu da mahaliccin muke yi, ba wai tallata abubuwan da ya kamata ba.”

Tafidan na Gwagwarwa ya kuma yi tsokaci kan Sallar Alqunut da Gwamnatin Kwankwasiy­ya ta gudanar, inda ya ce wannan ba haka

Allah ya ce a yi sallatul hajati ba, "A ina aka ce limamin irin wannan sallah ya yi huxuba, sannan ya kama banbaxanci tare da aibata wasu jama'a, don haka muna da yaqinin sun ruguza kansu a wurin wanda ya kamata a ce an kyautatawa ayyuka ba a yi domin riya ba.”

 ?? ?? •Taron addu'ar da aka gudanar a Unguwar Gwagwarwa ta Jihar Kano
•Taron addu'ar da aka gudanar a Unguwar Gwagwarwa ta Jihar Kano

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria