Leadership Hausa

Kotu Ta Ɗaure ‘Yan Ƙungiyar Asiri 4 Bisa Zargin Kisan Kai

- Tare da

An tasa qeyyar wani matashi xan shekara 21, John Junior, zuwa gidan yari na Ikoyi bisa zargin kashe wani Kehinde Sule da ke zaune a kan titin Apapa, a unguwar Ebute Metta na Jihar Legas.

An gurfanar da Junior a gaban Majistare O. Y. Adefope na wata kotun Majistare ta Yaba a kan laifuka biyar da suka haxa da kisan kai, zama xaya daga cikin mambobin haramtacci­yar qungiyar asiri da kuma fashi da makami.

A cewar mai gabatar da qara, Haruna Magaji, wanda ya yi wa Chekwube Okeh taqaitacce­n bayani, wanda ake qara, xan qungiyar Aiye Confratern­ity ne wanda ‘yan qungiyarsa suka kai hari gidan Sule, wanda aka fi sani da ‘Seigo’, inda suka kashe shi ta hanyar amfani da gatari wajen saransa da caka masa wuqa a kansa da ciki.

A wani vangare na tuhumetuhu­men da aka yi an karanto cewa “Cewa kai, John Junior da sauran jama’arka a ranar 17 ga Maris, 2023, da misalin qarfe 9:30 na dare, a kan titin Apapa, Ebute Metta Legas, a gundumar majistare da aka ambata, kun kai hari kuma da gangan inda kuka kashe wani Kehinde Sule, da fi sani da Seigo ta hanyar amfani da gatari wajen saransa da kuma dava masa wuka a kai da cikinsa sannan ka aikata laifin da ya sava wa sashe na 222 (1)a) (b) kuma hukuncin da ke qarqashin sashe na 223 na dokar laifuka ta Jihar Legas, 2015.”

Mai gabatar da qara ya shaida wa kotun cewa ta ci gaba da tsare wanda ake qara har sai an kammala karvar bayanai daga hukumar kula da qararrakin jama’a.

Bayan gabatar da wannan buqata, Mai Shari’a Adefope ya sa an tasa qeyar wanda ake qara zuwa gidan yari na Ikoyi sannan ya xage sauraron qarar zuwa ranar 28 ga watan Satumba, 2023.

Har ila yau, an tasa qeyar wasu mutum da ake zargin ‘yan qungiyar asiri ne zuwa cibiyar cibiyar na Qirqiri bisa zargin mallakar makamai.

Waxanda ake zargin, Solomon Samuel, Ibrahim Mohammed da Moses Ogundepo, an gurfanar da su ne a gaban wata kotun Majistare da ke Unguwar Yaba bisa laifin mallakar makamai ba bisa qa’ida ba da kuma zama mambobin haramtattu­n qungiyoyin Aiye da Alora Fraterniti­es.

Xansanda mai shigar da qara, Thomas Nurudeen, ya shaida wa kotun cewa, an kama waxanda ake zargin ne a titin Ojumola, Shomolu, da Ajegunle, inda ya qara da cewa an samu bindiga gargajiya guda xaya da kuma harsashi daga wurinsu.

Mai Shari’a Adefope, wanda ya saurari taqaitacce­n bayani ga Patrick Nwaka, ya bayar

Rabiu Ali Indabawa 0803433694­9 da umarnin a ci gaba da tsare waxanda ake zargin na tsawon kwanaki 30 sannan a aika da su ofishin DPP domin kammala bincike, sannan ya xage sauraron qarar zuwa ranar 28 ga Satumba, 2023.

 ?? ?? •'Yan Qungiyar
•'Yan Qungiyar

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria