Leadership Hausa

Sojojin Ruwa Sun Cafke Mutum Bakwai Bisa Zargin Satar Mai A Jirgin Ruwa

-

Tawagar sojojin ruwan Nijeriya da ke sintiri ta Beecroft sun daqile wani yunqurin haramtacce­n aikin satar mai tare da kama wasu mutum bakwai da ake zargi da hannu a ciki.

An ce an kama su ne a kan wata motar daukar kaya mai suna VIRGO I.

Rahotanni sun ce an kama su ne da wasu jiragen ruwa guda biyu na katako a lokacin da suke xauke da Premium Motor Spirit daga cikin jirgin tare da xaruruwan jarkoki 200 mai xauke da lita 50.

Kwamandan, NNS Beecroft, Kolawale Oguntuga, yayin da yake gabatar da waxanda ake zargin a filin fareti na rundunar sojin ruwa da ke Apapa Legas, ya ce za a miqa su ga hukumomin da suka dace.

Oguntuga ya bayyana sunayen waxanda ake zargin da suka haxa da Freme Adio, Onore Akwaso, Isegbejii Deli, Kosi Pascal, Dao Sure, John Abel da Buga Noel.

Ya ce, “Tawagar sintiri ta rundunar sojojin ruwan Nijeriya NNS Beecroft ta sake nuna bajinta wajen yaqar baragurbin da suke xiban mai ba bisa qa’ida ba, tare da samun nasarar cafke wasu jiragen ruwa da dama da ke yin fasaqwauri waxanda hakan zai iya haifar da qarancin kayayyakin mai da za a raba.

"A farkon sa'o'i na 27 ga Agusta, 2023, fasahar zamani, Falcon Eye Maritime Domain Awareness Facility, ta lura da tarin jiragen ruwa a kusa da Motar Tankar VIRGO 1, mai rajista a Panama.

“Lokacin da aka isa wurin da lamarin ya faru mai nisan mil huxu daga Legas Fair-Way Buoy, tawagar ‘yan sintiri ta gano wata hanyar hada-hadar mai ba bisa qa’ida ba.

An samu wasu kwale-kwale na katako guda biyu, xauke da xaruruwan durum-durom masu nauyin lita 200 da jarkoki 50 masu xaukar PMS daga MT VIRGO 1."

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria