Leadership Hausa

Jami'in LASTMA Na Bogi Da Ya Sato Mota Ya Shiga Hannu

-

An kama wani mutum mai suna Adejumo, da ake zargi da yin sojan gona na jami’in Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa Ta Jihar Legas, da laifin janyo mota a Legas.

PUNCH Metro ta gano a wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa wanda ake zargin ya tuqo wata mota mai fentin LASTMA a jikinta kuma ana zarginsa da sato motar gami da janyo ta da sanyin safiya a unguwar Somolu da ke Legas.

A cikin faifan bidiyon, an ji wata mata da har yanzu ba a bayyana sunanta ba, mai yiwuwa ita ce mamallakiy­ar motar qirar Acura MDX, tana ihun cewa an sace motar ta ne ta hanyar amfani da motar jawo motoci ta LASTMA.

Ta ce, sandar da aka maqala a jikin motar domin janyo ta ce ta karye, sannan direban motar ya fita ya gudu bayan da mazauna garin suka yi masa ihun varawo.

“Ban taba tsammanin cewa za a yi amfani da motar janyo motoci a sace mota ba. Alhamdu lillah, kawai sai jama’ armu suka tashi suka fara ihu, yayin da mutane suka yi ta ihu sai varayin suka ruga da gudu suka bar komai nasu a wurin,” in ji matar.

An ga motar da aka janyo ta kakare a bayan sandar da aka maqala sarqar janyo motar ya ta karye.

Da yake bayani a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya, Daraktan hulxa da wayar da kan jama’a na LASTMA, Adebayo Taofiq, ya ce an kama direban motar.

Adebayo ya ce, “Direban motar da ya tuqo motar janyo motocin ba jami’in LASTMA ba ne. Yana da kyau a sanar da jama’a, musamman masu ababen hawa cewa an kama direban, Adejumo, kuma a yanzu haka yana ofishin ‘yansanda na Pedro domin ci gaba da bincike.”

Ya qara da cewa bincike ya nuna cewa “Direban motar da aka kama ya yi kama da xaya daga cikin masu safarar motocin LASTMA da katin shaida na bogi da tambarin LASTMA na jabu.”

Ya qara da cewa Babban Manajan Hukumar LASTMA, Mista Bolaji Oreagba, ya roqi jama’a da su yi hattara da miyagu masu qoqarin vata sunan hukumar.

 ?? ?? •Wanda ake zargi
•Wanda ake zargi

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria