Leadership Hausa

“Ƙangin Talauci”

- BANGO

da ayyukan kiwon lafiya na yau da kullum, da matsuguna masu aminci, duka waɗannan ayyukan an masu lakabi da “tabbaci biyu da garanti uku.”

Daga nan ne ma’aikatun suka ƙaddamar da wani gagarumin yaƙin neman warware matsalolin da suka kunno kai kuma a ƙarshen shekarar 2019, an warware batutuwan mutane miliyan 5.2 waɗanda ke cikin shirin “tabbaci biyu da garanti uku”.

Sama da shekaru 15 da suka wuce, ƙasar Sin ta tsara wani buri mai kyau na zama “al’umma mai matsakaici­n wadata (ta kowane fanni)” ya zuwa shekarar 2020. Babban sakataren am’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, ƙasar Sin ba za ta iya zama “al’umma mai matsakaici­n wadata ba”, duk girman GDP na kasar ga kowane mutum kuwa, idan wani ɗan ƙasar ya ci gaba da rayuwa cikin matsananci­n talauci.

Xi ya kara da cewa, ya mayar da hankali wajen rage raɗaɗin alauci fiye da komai – wannan jawabi ne mai ban sha’awa daga shugaban ƙasa. Ta yaya ake aiwatar da aikin kawar da fatara, musamman a matakin ƙasa, inda abin ya fi dacewa?

Babban abin dake da muhimmanci shi ne, jam’iyyar CPC, a haɗa ƙarfi da ƙarfe, da ɗaukar jami’an CPC a kowane mataki, musamman a ƙananan matakai, kusa da talakawan ƙasar Sin. Hasali ma, Xi ya sanya batun kawar da talauci a matsayin babban fifiko ga mambobin jam’iyyar CPC, waɗanda a halin yanzu ayyukansu ke ci gaba bisa sakamakon kawar da fatara.

A ƙarshen shekarar 2018, yawan matalauta a ƙauyukan ƙasar Sin ya kai miliyan 16.6 waɗanda ke rayuwa a karkashin ma’aunin talauci da yake kimanin RMB 3,000 a kowace shekara, wato kwatankwac­in dalar Amurka 500. Suna zaune a kananan hukumomi dake cikin talauci 400, kusan ƙauyuka dake cikin talauci 30,000. Adadin matalauta mazauna karkara a ƙasar Sin ya ragu daga kimanin miliyan 100 a ƙarshen shekarar 2012, adadin da ya samu raguwar sama da miliyan 80 cikin shekaru shida.

Xi ya ce, “Na yi tunanin na san wani abu mai kyau game da ƙasar Sin, amma sai da na shafe makonni a cikin talakawan ƙasar Sin da kuma ƙananan hukumomin ƙasar, ban fahimci yadda aikin rage talauci da aka yi niyya ke gudana ba. Na shaida hanyoyin kawar da talauci guda biyar a aikace: Samar da ƙananan masana’antu (yawanci noma); ƙirƙirar ƙananan kasuwanci mai ɗorewa; sake tsugunar da mazauna ƙauyuka daga wurare masu nisa; ilimi da horo; bada kuɗi na gyarar muhalli ga waɗanda ke zaune a wuraren da ke da rauni; da tsaro na zamantakew­a, tallafin kiwon lafiya da biyan kuɗi kai tsaye ga waɗanda ba za su iya aiki ba”.

1) Kowane gida dake cikin talauci ya zuwa miliyoyin gidaje, akwai takardar dake dauke da lissafin kowane mazaunin gidan; ana sabunta shi kowane wata kuma ana aika bayanai akai-akai zuwa Beijing;

2) Sakatarori­n Jam’iyya a matakai biyar suna da hannu kai tsaye wajen daidaitawa da aiwatar da aikin kawar da fatara – a matakin lardi, birni, yanki, gari, da ƙauye.

3) Jami’an Jam’iyyar matasa suna aiki kai tsaye tare da yalai marasa galihu, kuma suna rayuwa kusan shekaru biyu a ƙauyukan marasa galihu. Bugu da ƙari, duk da an ware kuɗi masu yawa a wurare da yawa, za a yi tsammanin cin hanci da rashawa zai zama matsala - amma dole a yaba da yadda gwamnati ke bayyana girmanta ta hanyar gudanar da ayyukan a fayyace. Rahoton 2018 ya nuna alkalumma 131,000 na cin hanci da rashawa da kuma almundahan­a a cikin aikin yaki da alauci, wanda ya shafi mutane 177,000.

Da yake zama na biyu a yayin taron manema labarai, ministan kula da ofishin yaki da fatara da ci gaba na majalisar gudanarwar ƙasar Liu Yongfu, ya bayyana cewa, babu wanda ya isa ya yi amfani da aikin kawar da fatara a matsayin uzuri don biyan buƙatar kansa.

Ya ce, ya yi balaguro a yankunan da suka fi fama da talauci a ƙasar Sin, saboda yana shirya wani babban shiri na bidiyo kan abarin “yaki da fatara” na musamman na ƙasar Sin. Damuwarsa a ƙarshe ita ce: Idan an yi nasarar kawar da talauci ya zuwa shekara ta 2020 to me zai faru a gaba? Don kawai an fitar da mutane daga matsanacin talauci daga bisani kudin shigarsu ya ƙaru na shekara guda, ba ya nufin sun zama masu “matsakaici­n wadata”. To ta yaya za a tabbatar da shirin rage talauci na kasar Sin ya ɗore?

Ba sabon abu ba ne jin yadda ƙasar Sin ta fitar da miliyoyin mutane daga kangin talauci a cikin shekarun da suka gabata. Adadin matalauta a duniya ya ragu da rabi tun daga shekara ta 2000, wannan nasara ce da ƙasar Sin ta jagoranta, wadda ke da alhakin rage kashi 70 cikin 100 na masu fama da matsananci talauci a duniya.

Tare da bullo da manufar ci gaba mai ɗorewa ta MDD, wadda ta yi alkawarin kawar da matsananci­n talauci nan da shekarar 2030, ƙasashe na fatan ɗaukar darasi daga ƙasar Sin. Kamar yadda tsarin ƙasar Sin take game da ci gaba, kwarewar da ƙasar Sin ta samu kan kawar da talauci wani abu ne da misali kawai za a iya da shi, ba wai a kwafa ba.

A ko da yaushe ƙasar Sin ta kan yi la’akari da ƙarshen aiki da tasirin aiki kafin ta fara, sai ta ja takamaiman layin kammala aikin kuma ta kan tabbatar da an kai ga layin. Ƙasar Sin ta ƙudirci kammala aikin yaƙi da talauci a shekara ta 2020, a wannan lokaci ana sa ran babu ragowar matalauta. Tsarin mulkin ƙasar Sin da ake ta cece-kuce a kai, a zahiri yana nuna fa’idarsa ta hanyar tattara dukkan albarkatun dake hannunta wajen ciyar da al’ummunta gaba.

An bullo da hanyoyi guda biyar a ƙasar Sin don fitar da mutane daga kangin talauci: raya ƙasa, sake tsugunar da jama’a, da biyan diyya, ba da ilimi, da kare lafiyar jama’a. Har ila yau, hukumomi sun yi alkawarin gudanar da wadannan matakan ta hanyar da ta dace, dangane da tantance mutanen da suke samun taimako, shirye-shiryen da amfani da kuɗaɗe, aiwatarwa da ayyukan hukuma da kuma tantance sakamakon.

Ƙasar Sin ta mai da hankali kan ci gaba ta hanyar ciniki da masana’antu wanda ya zama misali mai haske na yadda ake kara samun kuɗin shiga da samar da ayyukan yi. Waɗannan su ne irin darussan da suke da mahimmanci ga sauran ƙasashe masu ƙarancin ci gaba, ko wadatar rashin aikin yi, saboda tattalin arzikinsu ya dogara ne a kan hakar albarkatun ƙasa, wanda a zahiri ba ya samar da wadatattun da ayyukan yi.

Duniya ta samu gagarumin ci gaba game da tsarin masana’antu wanda ake kira 4.0. A bisa wannan dalilin, da yawa daga cikin mafi ƙasƙanci ƙasashe ba za su iya hassasa masana’antunsu kafin duniya ta ci gaba zuwa babi na gaba ba. Ya zama wajibi ga irin wadannan ƙasashen da su bullo da sabbin matakai baya ga ajandar ci gaban da suke da shi a baya.

Yin la’akari da karfin ikon mutane, alal misali, wani abin koyi ne daga hikimar Sinawa. An bayar da ilimi da koyar da sana’o’i ga talakawa daga yankuna daban-daban domin taimaka musu wajen samun aikin yi. Amma ya zama wajibi ga masu ɗauke da shirin su tantance wace sana’a za su mayar da hankali a kai, ta yadda zai dace da bukatar tattalin arziki.

Idan aka yi hange sama da shekarar 2020, ƙasar Sin ta yi imanin cewa, yaƙi da talauci da aka yi niyya za ta iya taimakawa sauran ƙasashe, don haka ta amsa kiran da shugaba Xi ya yi na “hikimar ƙasar Sin” da “mafitar ƙasar Sin” don amfanar duniya. Amma a aikace, kwarewar ƙasar Sin jagora ce da za a yi koyi da ba umarni ba ne da za a bi.

“Sin ta kasance ƙasa mai tasowa mai yawan talakawa. Don haka a halin yanzu, mun fi bude kofa ga yin musayar kwarewa da kyawawan ayyuka,” in ji Liu Yongfu, Darakta na Ofishin Jagoran Kungiyar Yaƙi da Talauci da Ci gaban Majalisar ƙasa. “Kuma yayin da muke cika burinmu na rage raɗaɗin talauci da kuma samun ci gaba mai kyau, za mu kuma kara zuba jari a ƙasashe matalauta baya ga ba da kwarewaemu.”

“A gaskiya, aikin yaƙi da talauci da kansa gudummawa ce ga duniya. A wajen neman ci gaba tare, mu ma za mu ƙara himma.”In ji Liu.

Shekarar 2020 bata kasance kamar kowane shekaru ba ga ƙasar Sin da ma duniya baki daya. Cutar ta COVID-19 tare da ambaliya a kudancin ƙasar Sin sun haifar da ƙalubale masu ban mamaki ga yaƙi da fatara na ƙasa.

A cewar Bankin Duniya, an kiyasta cutar ta COVID-19 ta jefa ƙarin mutane miliyan 88-115 cikin matsananci­n talauci a shekarar 2020, wanda ke nufin tsananin talauci a duniya ana sa ran zai ƙaru a karon farko cikin sama da shekaru 20.

Shugaba Xi ya jaddada a wajen taron karawa juna sani kan samun gagarumin nasara wajen yaƙi da fatara a watan Maris na shekarar 2020, cewa, fitar da dukkan mazauna yankunan karkara daga kangin talauci nan da shekarar 2020, wani muhimmin alkawari ne da kwamitin kolin JKS ya yi, kuma dole ne a cika shi a kan lokaci.

Kasar ta ɗauki matakai masu ƙarfi da inganci don tabbatar da kawar da talauci a kan jadawalin da aka tsara. An ƙara yin ƙoƙari don rage asarar da bala’o’i ke haifarwa, da kuma hanzarta dawo da samarwar zaman rayuwa a yankunan da bala’i ya shafa.

Ministocin sun kuma ƙara sanya ido tare da ba da taimako kan lokaci don hana mutane faɗawa cikin talauci.

A watan Disamba na shekarar 2020, shugaba Xi ya sanar da cewa, bayan shafe shekaru takwas ana ƙoƙarin kawo ƙarshen talauci, an fitar da dukkan matalautan yankunan karkara daga kangin talauci, kuma kusan mutane miliyan 100 sun kuɓuta daga kangin talauci.

(Yahaya)

 ?? ?? An Cimma Burin Yaƙi Da Talauci Duk Da COVID-19
An Cimma Burin Yaƙi Da Talauci Duk Da COVID-19
 ?? ??
 ?? ??
 ?? ??
 ?? ??

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria