Leadership Hausa

Sana'a Ce Rufin Asirin Mace —Hindatu

- ADON GARI Tare Da

Da farko za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki

Sunana Hindatu Sulaiman amma anfi kirana da Ummi. Na yi makarantar primary a Aonullah Model School, IjebuOde Ogun State knn. Na yi ‘Secondary school’ guda biya a nan Jihar Ogun mai suna ‘Oke-Eri Comprehens­ive High School’. Ina karatun Jami'a a jihar Sakkwaro wato ‘Sokoto State University’ ina karanta ilimin qwayoyin halittu wato (Microbiolo­gy).

Shin Hindatu matar aure ce?

A, a ni ba matar aure bace

Malam Hindatu 'yar kasuwa ce ko kuwa karatu kaxe tasa a gaba?

Eh to ana iya cewa ‘yar kasuwa nake, saboda gaskiya ina xan tava kasuwanci kaxan kaxan haka de ba lefi.

Wannen irin kasuwaci kike yi?

‘Company Business’ nake yi ma'ana zaka yi ‘Ordering’ wato abin da ake nufi da ‘order’ shi ne za a tura maka kaya a hoto ka gani idan ya myi aka sai ka biya kuxinsa sannan na cire ribata sai na tura kamfani aiko maka da kayanka wato ni zan saro maka daga kamfani.

Ina sayar da kayan kwalliya na mata (Cosmetics), Turare na mata da maza sai kuma ‘Skincare Creams for both Ladies and Gentlemen’, wato man gyaran fata na maza da mata.

Me ya je hankalinki har kika shiga wannan kasuwanci?

Abin da ya ja hankali na shi ne ni mutum ce da ban son ina yawan tambayar Babana abu, shi yasa na ce nima ya kamata na fara Kasuwanci.

Hindatu baki faxa mana matakin karatunki ba?

Ina Jami'a ne yanzu aji na biyu wato ‘200 level’.

Wanne irin qalubale kika tava fuskanta a cikin sana'arki?

Da yawa, misali kayan da muke sayarwa gaskiya suna da tsada, idan ba wanda ya tava ko yana jin ana maganar ‘Products’ xin ba ba zai iya saya ba. Shi yasa wani lokaci ake kashe maka qwarin gwiwa.

Zuwa nasarori sana’ar? yanzu waxanne irin kika cimma a harkar

Ban cimma ba amman InshaAllah na san ina kan hanya nan bada jumawa ba.

burinki?

Burina shi ne na zama Likita

Wanne abu ne yafi faranta miki rai game da sana'arki?

Yadda nake ganin anawa wasu yadda nake gani ana bawa mutane kyaututtua wanda ya shafi (Awards) a kana bin da suke sayarwa, ina jin daxin hakan, shi ya sa nake sa a raina nima lokaci zai zo da za a karrama ni a kan wannan sana’ar.

Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana'arki?

Hanyar da dama, ina tallata sana'ata

Bilkisu Tijjani Kassim.

HINDATU SULAIMAN,

ta yanar gizo wato (By posting in all my social handles).

Dame kike so mutane su rinqa tunawa dake?

So nake su gwada sayan kayana wato ‘Pproducts’ xina nasan za su ji daxin shi, to daga nan na san kuma za su rinqa tunawa dani.

Ga karatu ga kuma hidimar sana'a shin, ta yaya kike haxasu?

Na riga na saba da wahalar makaranta don haka wahalar kasuwanci ba komai ba ne a gare ni

Wanne irin addu'a ne idan aka yi miki kike jin daxin?

Allah yasa ki ci amfanin wahalar ki, ina yawan jin wannan addu’ar ina jin xaxin addu'ar nan.

Wanne irin goyon baya samu daga wajen iyayanki? Qawaye fa? kike

Gaskiya ina samun goyon baya musamman ma daga wajen Umma na, amman gaskiya dukkan su biyun na ba ni goyon baya xari bisa xari.

Gaskiya ba ni da aminiya sai dai ina da qawaye da yawa kowa nawa ne

Me kika fi so cikin kayan sawa da kayan kwalliya?

Na fi son dogowar riga ko riga da siket da hijab. Ni bana kwalliya.

A qarshe wanne irin shawara za ki ba 'yanuwanki mata?

Shawarata shi ne mu tashi tsaye su nemi sana'a don sana'a shi ne rufin asirin mace.

 ?? ?? •Hindatu Sulaiman
•Hindatu Sulaiman

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria