Leadership Hausa

Kamfanin ‘Power Oil’ Ya Ƙulla Alaƙa Da Ali Nuhu Kan Wayar Da Kan Jama’a

- Shin me kasuwancin naki ya qunsa? Ma'ana kamar me da me kike sarowa? A da can da kike qarama mene ne

Kamfanin Man Girki na Power Oil ya sanar da qara faxaxa gangaminsa na inganta kiwon lafiya a Arewacin Nijeriya. Kamfanin wanda ya fara kaddamar da man girki mai kyau a Nijeriya kuma kwanan nan ya yi hadin gwiwa da Ali Nuhu Mohammed (dan wasan kwaikwayo na Nijeriya kuma darakta wanda aka fi sani da Sarkin Kannywood) ya bayyana cewa za su shiga wani gangami a kan wayar da kan jama'a game da salon rayuwa mai inganci.

Gangamin zai faxakar da mutane kan yadda ake amfani da man girki sahihi tare da kauce wa amfani da irin man da ba a san asalinsa ba ko sunan kamfanin da ya sarrafa ba a Nijeriya.

Tsawon shekaru, man girki marasa asali sun samu gindin zama a cikin rumfunan kasuwar Nijeriya tare da shiga gidaje daban-daban ta hanyoyin da ba za su qididdigu ba. Akwai irin wannan man girki a cikin kwantenoni, sannan abin takaici yana haifar da rashin lafiya saboda rashin inganci da tsaftar da ta kamata a kiyaye yayin sarrafawa.

Wani abin la'akari shi ne yanayin tattalin arziki da kuma tsadar rayuwa a cikin kasa babu shakka sun sa magidanta cikin tagumi, don haka ake da buqatar kowa ya rika lura da yadda yake kashe kudin aljihunsa. Shi ya sa talakan Nijeriya a koyaushe ya gwammace ya rika make kudinsa tare da sayen gurbatattu­n abubuwa maimakon wadanda za su kiyaye koshin lafiya.

Daya daga cikin irin wadannan abubuwa shi ne man girki; wanda ake amfani da su a kai a kai a cikin kicin. Domin samun biyan bukata, talakawan Nijeriya sun zabi man girki mara sinadari wanda ke da araha kuma yana kara hadari ga lafiyar zuciya.

Kwararrun likitoci da hukumomin da abin ya shafa kamar Gidauniyar Kula da Cututtukan Zuciya ta Nijeriya (NHF) da sauran su sun yi gargadi game da shan wadannan kayayyakin da ba su da asali wadanda ka iya dauke da sinadarin kara kitse mara amfani (cholestero­l) mai yawa. Kasuwar irin wannan gurbatacce­n mai na ci gaba da hauhawa yayin da kwayar kitsen cholestero­l da cututtukan zuciya ke haddasuwa a cikin rayuwar masu amfani da su. A cewar kwararrun likitocin, cholestero­l na da matukar hadari ga cututtukan zuciya a tsakanin mutane masu shekaru daban-daban.

Sakamakon kudirin fadakar da ‘Yan Nijeriya hanyoyin kiwon lafiya tare da Jarumi Ali Nuhu, Man Girki na Power Oil wanda ba ya dauke da ‘cholestero­l’ ko kadan da sauran sinadarai na gina jiki yana fatan ya leka lunguna da sako na arewacin Nijeriya domin wayar da kan a kan amfani da man girki mara suna da asali, kana da ilmantar da ‘Yan Nijeriya a kan yadda za su rika gudanar da rayuwa cikin koshin lafiya.

Ali Nuhu Mohammed wanda wasu suke masa la abi da “Sarki Ali” ana xaukarsa a matsayin wani jigo musamman a tsakanin matasan Arewa; ya samu lambobin yabo da karramawa daga sassa daban-daban, wanda hakan ne ya ba shi damar zama mafi dacewa wajen jagorantar gangamin. Zai yi amfani da shuhurarsa tare da tasirin da yake da shi wajen jagorantar da gangamin hana amfani da man girki maraasali.

Wakazalika, Man Girki na Power Oil yana shirya motsa jiki na musamman wanda kowa da kowa zai iya halarta. Tun daga 2015 aka kaddamar da shirin inda likitoci daga sassan kiwon lafiya da dama ke halarta domin wayar da kan jama’a a kan rayuwa mai inganci.

 ?? ??

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria