Leadership Hausa

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Don Fara Rigakafin Kansar Mahaifa

-

Hukumar lafiya ta duniya ta qiyasta cewar ana iya maganin kansar mahaifa idan har aka samun yi ma kashi 90 na ‘yan mata allurar rigakafi ta qwayar cuta mai suna Human Papillo Virus.

Gwamanatin tarayya ta kammala shiryeshir­yen da suka kamata domin gabatar da allurar da zata ceci rayuwar mata matasa wajen yi masu allurar rigakafin kansar mahaifa allurar rigakafi mai suna Human Papillomav­irus (HPV) wadda zata kare ‘yan mata daga kamuwa da cutar kansar mahaifa da sauaran cututtuka masu ala qa da ita.

Darektan hukumar kula da lafiya matakin farko Dakta Faisal Shuaib, shi ya bayyana hakan ranar Litinin a Abuja lokacin da aka yi taro da Shugabanni­n addini kan halin da hukumar take ciki.

Mista Shuaib ya ce gwamnatin zata fara yin allurar ne ranar 25 ga watan Satumba ga ‘yan mata masu shekara 9 zuwa 15.

Ya ce kansar mahaifa tana shafar iyayenmu,’yan'uwanmu, ‘ya'yanmu mata da suke kamuwa da cutar ta hanyar qwara HPV".

“Ranar 25 ga watan Satumba wannan shekara za mu fara yi ma ‘ya’yanmu mata masu shekara 9 zuwa 15 allurar rigakafin kamuwa da kansar mahaifa.”

Qwayar Cutar HPV Da Kansar Mahaifa

Kansar mahaifa wata nau’in cutar kansa ce da take girma cikin mahaifar mace, ita ceta huxu da aka fi sani a tsakanin mata a duniya. Masana sun ce a shekarar 2008 kaxau cutar kansar mahaifa ta yi sanadiyar mutuwar kamar yadda aka qiyasta mutuwar mata 311,000 a faxin duniya.

Binciken da Lancet suka yi ya nuna cewar fiye da mata milyan 44 na iya kamuwa da cutar kansar mahaifa tsakanin shekarar 2020 da 2069.

Hakanan ma ta yi gargaxin cewa ana iya samun qaruwara mutuwa daga kansar mahaifa ada abin zai iya kaiwa kashi 50 nan da shekara ta 2040, bugu daqari mata da yawa al’amarin zai shafar iyalansu da al’umma.

Duk da yake ba a san abinda yake sa ana kamuwa da cutar kansar mahaifa ba sai dai 14 daga cikin 100 na qwayar cutar mai suna Human Papillomav­irus (HPV) an gano cewa sune musabbabin kamuwa da a qalla kashi 99 na waxanda suka kamu da cutar kansa.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce nau’oin qwayar cuta ta,HPV 16 da 18 sune musabbabin a qalla kashi 70 na nau’oin kansar da kuma kafin kamuwa da ita cutar.

Akwai ma sheda da ta haxa qwayar cuta HPV da nau’oin kansa na dubura,wani sashe na farji, farji, azzakari, da oropharynx.

“Allural rigakafin qwayar cutar HPV tace wani cigaban daya shafi al’amarin kula da lafiyar al’umma.Wani abu ne mai nuna haxin kanmu wajen kare mutuncin rayuwa kjamar yadda Shu’aib ya jaddada”.

Gidunmawar Shugabanni­n Addini

Mista Shuaib ya ce yana da yana da kyau a samiu wayar da kan al’umma ko ina suke hakan ta sa gudunmawar Shugabanni­n ta taso.

Sune ke da damar sadar da saqo mai muhimmanci wanda zai yi tasiri kan al’umma da kawar da shakku, su bada qwarin gwiwa na amincewa da saqon da ake son isarwa zuwa gare su,su yarda da tsarin da zamani ya zo da shi ta hanyar gwamnati.

“Ya ce kalamansu suna da matuqar tasiri ga al’umma su amince har ga zuciyar su saboda mutuntawa da girmamawar da suke yi masu.

 ?? ??
 ?? ?? Idris Aliyu Daudawa ayau@leadership.ng
Idris Aliyu Daudawa ayau@leadership.ng

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria