Leadership Hausa

Mene Ne Tsarin 5G?

- Kimiyya Da Fasahar Sadarwa Tare da

Tsarin 5G wani tsari ne na intanet da ke bayar da damar saukewa da xora saqonni cikin matuqar sauri a intanet.

Yana bai wa wayoyi da sauran na'urori da yawa damar amfani da intanet a lokaci guda.

"Duk abin da muke yi da wayoyinmu yanzu, za mu iya yi da tsarin 5G amma cikin sauri kuma cikin sauqi," a cewar Ian Fogg na OpenSignal, wani kamfanin waya.

Ku yi tunanin tarin jirage marasa matuqi sun haxa kai wajen gudanar da aikin bincike da ceto da sa ido kan tarin motoci da ke wuri guda, kuma duk suna aiki tare suna sadar da bayanai ga juna ba tare da amfani da waya ba, kuma dukansu suna amfani ne da tsarin 3G.

Haka kuma, mutane da yawa na ganin cewa tsarin 5G zai taka muhimmiyar rawa kan abubuwan hawa maras matuka wajen musayar bayanai a tsakaninsu.

Yaya tsarin yake aiki?

Wata sabuwar fasaha ce, amma idan aka fara amfani da ita ba lallai ne a fahimci saurin intanet din ba saboda akwai yiwuwar amfani da tsarin 5G ne daga farko wurin inganta tsarin 4G.

Saurin da wayarka za ta yi zai danganta ne da kamfanin sadarwarka da yadda suke amfani da tsarin 5G da kuma irin kayan aikinsu.

Saurin tsarin 4G a halin yanzu na bayar da gudun 45Mbps (duk daqiqa xaya). Amma ana sa rai tsarin 5G na iya samar da sauri sau 10 zuwa 20 fiye da na 4G. Wannan zai ba da damar sauke fim, wato ‘downloadin­g’, cikin minti guda.

Ci gaban da za a samu a sauri da ingancin intanet zai fara aiki ne idan kamfanonin sadarwar suka kafa tsarin 5G mai zaman kansa, inda duka ayyukansu na amfani da fasahar 5G.

Me ya sa za mu buqaci tsarin?

Kusan duka al'amuran duniya sun dogara ne kan wayoyin hannu kuma amfani da data na qaruwa duk shekara, musamman wajen kallon bidiyo ke qaruwa.

Tsare-tsaren da ake da su yanzu suna kara takurewa, shi ya sa ake samun cunkoso ko tsaiko a network musamman idan akwai mutane da yawa a wuri guda suna kokarin amfani da network guda a lokaci guda.

Tsarin 5G ya fi sauqin bai wa dubban na'urori damar amfani da network guda a lokaci guda, kama daga wayoyin hannu zuwa na'urar xaukar hoto da fitilun kan titi masu kunnawa da kashe kansu.

Zan buqaci sabuwar waya kafin na iya amfani da tsarin?

Eh. Amma a lokacin da aka qaddamar da tsarin 4G a shekarar 2009 zuwa 2010, a daidai lokacin ne aka fara sayar da sabbin wayoyi.

Kuma mutane sun yi ta qorafin cewa kuxin data ya qaru yayin da ingancin networ xin bai gyaru ba.

Tsarin zai yi aiki a karkara?

Ana yawan qorafi kan rashin network mai karfi a yankunan karkara. Amma tsarin 5G ba lallai ne ya yi maganin wannan korafin ba.

Tsarin 5G zai fi aiki ne a birane da ke da yawan mutane.

Kamfanonin sadarwa za su fi mayar da hankali ne kan inganta tsarin 4G LTE a yankunan da ke wajen birane yayin da suke kaddamar da 5G a biranen.

Amma wannan na nufin, ga mutanen da ke kauyuka, ingancin network dinsu ba zai gyaru ba har sai gwamnati ta sa manufofin da za su taimaki kamfanonin sadarwa yadda za su ji dadin kafa karafunan sadarwa a karkara.

 ?? ??

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria