Leadership Hausa

Ba Mu Hana Sulhu Da 'Yan Ta'adda Ba, Amma A Bar Jami'an Tsaro Su Yi Aikinsu - Bosso

- Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Sakamakon rahotannin da ke yawo na yunqurin wasu gwamnonin arewa na shirin yin sulhu da 'yan ta'addan daji, tsohon shugaban qungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders na qasa, Alhaji Hussaini Yusuf ya ce sulhu alheri ne, domin manzon Allah ya tabbatar da hakan.

Ya qara da cewa ba su hana a yi sulhu da ‘yan ta’adda ba, amma a bar jami’an tsa-ro su yi aikinsu.

Tsohon shugaban ya ci gaba da cewa maganar sulhu da 'yan ta'adda masu xauke da makamai a baya gwamnatin Zamfara da wasu gwamnoni sun yi irin wannan sulhun amma abin bai haifar da xa mai ido.

Ya ce babu tabbas idan an yi sulhun 'yan ta'addan za su ajiye makamansu, to ma ta ya ya za a yi sulhu wanda aka ka wa laifi ne ke neman sulhu ba mai laifin ba.

A cewarsa, idan da gaske su 'yan ta'addan sun amince da cewa sun yi laifi, su ne ya kamata su nemi yin sulhu ba gwamnati ba, idan ma ya zama gwamnatin ta matsa kan maganar sulhu, suna fatar Allah ya sa a yi da kyakkyawar niyya kuma a bar jami'an tsaro su ci gaba da aikinsu.

“Varayin nan na san ba za su ajiye makamansu ba, domin an yi a baya kuma abin bai yi wani tasiri ba, da suka xauki makami ba za su iya faxa maka laifin da aka yi musu da ya sa suke faxa wa talakawa suna kwashe su da lalata abinci da duki-yoyinsu, idan da gaske ne, to su manyansu su fito gwamnati ta ware wuri 'yan ta'addar nan su kawo makamansu a hannun gwamnati.

“Babban matsalar nan, akwai waxanda ke xaukar makamai a matsayin ‘yan banga kuma su ba ‘yan sa kai ba ne. Ka ga maganar 'yan banga da ke aiki da jami'an tsa-ro ban goyon bayan shi ba, domin suna da qwarewa saboda gogayyarsu da jami'an tsaro, amma wasu da amfani da wannan dama su na farmakan jama’a,” in ji shi.

 ?? ?? •Tsohon Shugaban Miyetti Allah Cattle Breeaders na qasa, Alhaji Hussaini Yusuf
•Tsohon Shugaban Miyetti Allah Cattle Breeaders na qasa, Alhaji Hussaini Yusuf

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria