Leadership Hausa

Yadda Aka Fara Gudanar Da Wasan Ƙwallon Folo A Katsina

- Daga Sagir Abubakar Katsina

Kimanin qungiyoyin qwallon dawaki 30 da suka haxa da wasu ‘yan wasan qwallon dawaki na qasashen waje da aka gayyato domin fafatawa a gasar qwallon dawaki a Jihar Katsina.

Shugaban qungiyar qwallon dawaki na Katsina, Muhammad Usman Sarki ya bay-yana haka a lokacin taron manema labarai da ya gudana a Katsina.

Shugaban ya yi nuni da cewa an fara gudanar da gasar ne a ranar Asabar 26 ga watan Agusta.

A cewarsa, qungiyoyin qwallon dawaki daban-daban daga Legas, Fatakwal, Ka-duna, Kano, Neja da Abuja sun bayyana shirinsu na shiga a fafata da su a lokacin gasar.

Shugaban qungiyar qwallon dawaki na Katsina ya ce a halin yanzu an xaga darajar filin wasan qwallon dawaki na Katsina domin karvar baquncin duk wani nau’i na wasan qwallon dawaki.

Ya ce an samar da masauki, tsaro, kula da lafiya, zirgazirga da kuma kula da walwalar ‘yan wasa domin inganta harkokin gasar wasan a Katsina.

Sai dai, Alhaji Muhammad Usman Sarki ya ce qwararrun ‘yan wasan dawaki za su yi gasar cin manyan kofuna guda 4 da suka haxa da gasar qwallon dawaki ta cin kofin Nijeriya, inda sauran qungiyoyin za su fafata da sauran qungiyoyin qwallon dawaki.

Alhaji Muhammad Usman Sarki ya yaba wa qoqarin gwamatin Jihar Katsina bisa bayar da tallafin kuxaxen ga qungiyar wanda ya taimaka masu wajen aiwayar da shiryeshir­yen ba tare da wata matsala ba.

Ya kuma jinjina wa gwamnatin jihar da mai martaba Sarkin Katsina a kan bayar da shawarwari ga qungiyar don ganin gasar ta samu nasara.

Tsohon Shugaban Qasa Muhammadu Buhari yana xaya daga cikin waxanda suka halarci buxe wasan qwallon a filin wasan qwallon folo da ke cikin birnin Katsina.

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria