Leadership Hausa

Harin 'Yan Bindiga A Qauyen Dan-Umaru: 'Yansanda Sun Ƙwato Roka A Kebbi

- Daga Umar Faruk Birnin Kebbi

Rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi, ta qwato wani makamin roka guda xaya da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi watsi da su a qauyen Dan-Umaru da ke gundumar Bena a Qaramar Hukumar Danko-Wasagu ta jihar.

Bayan samun wannan bayanin ne tawagar ‘yansanda daga sashen ‘yansanda na DanUmaru, suka ma-yar da martani cikin gaggawa da ruwan harsashi.

Kwamishina­n ‘yansandan jihar, CP Samuel Titus Musa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Birnin Kebbi, yayin da yake gabatar da waxanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a shalkwatar rundu-nar jihar.

Kwamishina­n ya ce "Tawagar 'yansandan sun yi nasarar daqile harin tare da gano makamin roka guda xaya, da 'yan bindigar da ake zargin sun tsere da raunukan harbin bindiga daban-daban.

Haka kuma ya qara da cewa, wani Aminu Bello dake Unguwar Almasira a cikin garin Jega, ya karvo bash-in Naira 485,000 daga abokinsa Abdulmajid Nasiru. Wanda ake zargin, Aminu Bello ya yaudari wanda abin ya shafa ya ja shi zuwa cikin wani daji da ke kusa da su inda ya daba masa wuqa a wuya.

Sakamakon haka, wanda aka dava wa wuqar ya faxi a sume kuma aka garzaya da shi babban asibitin Aisha Muhammadu Buhari da ke Jega inda wani likita da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa. Daga nan sai jami’an ‘yansanda suka kama wanda ake zargin wanda ke shirin tserewa.

A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa. A cewar kwamishina­n ‘yansanda, bayan an kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Hakazalika, an kama wata mata Mai suna Hauwa Sulieman dake kauyen Babbar Dogo dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, tana rike da harsashi harsashi guda dari biyar da sittin da shida (566) 7. 62×39mm. Ana gudanar da bincike kan lamarin. Da yake jaddada cewa an kama ta ne a yankin na kara-mar hukumar DankoWasag­u a ranar 24 ga Yuli, 2023.

A wata hira da ta yi ‘yar jarida a shalkwatar ‘yansanda da ke Birnin Kebbi, ta ce “Wata mata ce ta nemi in taimaka mata na karvo musu saqo a madadinta, daga nan na buve jakar da na ga harsashi, na isa wajen jami’an tsaron soji da ke bakin aiki a Qaramar Hukumar Danko-Wasagu, sai na sauka kan mota inda na same su daga nan na yi musu bayani kuma na miqa musu harsashi, in ji ta".

A cewarta, bai dace in bari a yi amfani da wannan harsashi wajen kashe xan’Adam ba, domin a matsay-ina na Musulma ta gari me zan faxa wa Allah Maxaukakin Sarki ranar haxuwata da shi. "Ban da wani zavi ban da in bayar da rahoto game da harsashin," in ji ta.

"Bayan sun yi min tambayoyi su jami'an soji suka yi mani, sun kama ni, daga baya suka miqa ni ga 'yan-sanda, a cewar Hauwa Sulieman." Sai dai ta ce, "Na san cewa mallakar harsashi laifi ne, shi ya sa na kai rahoto ga jami'an soji da ke bakin aiki a wurin da na ambata a sama," in ji ta.

Kwamishina­n, ya bayyana jin daxinsa ga muqaddashi­n

Sufeto Janar na ‘yansanda Kayode Adeolu Egbe-tokun da ya ga ya dace da a turo shi Jihar kebbi a matsayin Kwamishina­n ‘yansanda na 35.

A yayin da yake tabbatar wa IGP da gwamnatin Jihar kebbi da xaukacin al’ummar jihar cewa jami’an rundunar da ke qarqashins­a ba za su yi qasa a gwiwa ba wajen ganin Jihar Kebbi da kewaye ta samu ‘yanci daga duk wani nau’i na aikata laifuka.

Bisa ga hakan ya yi kira ga jama'a a faxin jihar da su taimaka wa 'yansanda da sauran hukumomin tsaro wajen ba da muhimman bayanai na duk wani motsi ko aiki da ake zargin laifi ne. Domin ta hanyar bayar da bayanai ne za mu iya yin aikin namu kamar yadda doka ta tana da na daqile duk wani laifi, in ji shi.

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria