Leadership Hausa

Sana'ar Sayar Da Qosai

- SANA’A SA’A

Assalamu alaikum masu bibiyarmu a wannan shafin mai farin jini da albarka na sana'a sa'a barkammu da sake haxuwa daku a wannan makon a cikin shirin namu na sana'a sa'a.

Sana'ar qosai wata sana'a ce wadda take da amfani kuma tanada riba so sai ko bakome qosai de abinci ne mai gyau kuma mai amfani, ana cin qosai lokacin karin kumullo sannan kuma wasu suna cin har da daddare.

Mai sana'ar qosanki: qosai yadda zaki qayata

Dafarko zaki samu wakenki sannan ki surfashi sai ki samu kwando ki wanke yadda ake wankeshi zaki cire masa dosarsa wato bayan shi ake qira da dusa ki zuba ruwa a waken sai kisa hannunki ki xan gauraya zakiga dosar ta yi sama sai ki zuba a kwandon dosar zakiga tana zuba cikin kwandon haka zakiyi har dosar tagama fita sai ki tsince sauran wanda ban fitaba da ya maqale a jikin waken da hannunki idan kingama sai kisa masa albasa da xan tattasai sai ki kai niqa amiki niqa mai laushi saboda yafi daxi idan yayi laushi, idan kika dawo kika haxa wutaki kika xora mai kafin man yayi zafi sai ki zubawa wannan qollun gishiri daidai yadda zai isa wannan qullun sannan ki bugashi wato kisa masa ludayi kiyi ta kaxashi amfanin bugashi shine yanasa qosai yayi laushi sannan kuma yayi daxi so sai fiye da wanda ba'a bugaba zakiga mutane sunasan qosanki sannan kuma idan zaki iya kisa masa qwai yana daxi so sai amma bawe mai yawa ba kamar idan na mudu xaya ne zaki samasa qwai guda biyu ko xaya ma kikasa yayi yana qarawa qosai daxi da laushi.

Suna: Yusuf Murtala Yusuf, ana qirana Khalifa Khalin boy

Shekaru: Goma 10.

Makaranta: Raudatul Qur'an

Academy

Aji: Ajina huxu zan shiga biyar idan mun koma hutu

Aboki: Al'amin Muhammad Sani.

Saboda me: Saboda muna karatu tare.

Abincin da kafi so: Soyayyen dankalin turawa da qwai

Abinsha: Lemon kwali

Kalar da kafi so: Shuxi

Burinka: Injiniya

Fatan Mahaifinsa Allah ya ba shi sa'a a kan duk abinda yake da buri na alkhari a rayuwa duniya da lahira.

Mahaifiyar­sa: Allah ya qaro shekaru masu albarka duniya da lahira.

 ?? ??
 ?? ??

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria