Leadership Hausa

Tsokaci Kan Yadda Wata Ƙanwa Ta Zalunci ‘Yar Yayarta Ta Riƙo

- Tare da

Shafin da ke zaqulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al'umma, musamman Zamantakew­ar Aure, Rayuwar Yau da Kullum, Rayuwar Matasa, Soyayya, da dai sauransu. A yau ma shafin na tafe da tattaunawa kan wani saqo da ya ci karo da shi game da cin amana.

Ga saqon: "Na yi tafiya na tsawon shekaru shida, na bar 'Yata me shekaru takwas a wajen qanwata. Ina biya mata kuxin makaranta tare da ‘ya’yan qanwar tawa guda biyu duk da cewa tana da aure. A kowanne wata nakan tura wa qanwata dubu saba'in na ciyarwa da sauran hidimomi, wani lokacin ma har dubu xari dan kawai na tabbatar da 'Yata ba ta rasa komai ba, ita ma qanwata haka. Na buxe wa qanwata wurin sana’a don kawai in tabbatar tana cikin walwala, saboda mu biyu ne kawai muka rage. Haka nan na siya wa kaina filaye guda biyu, sai kuma wani fili mai girman gaske wanda na shirya gina gida biyu daban-daban, xaya na qanwata xaya kuma nawa, kamar dai gidan dangi. Yaran qanwata su ne manya, nakan kira waya ta hoton bidiyo mu yi magana da 'Yata, wanda hakan ya ba ni damar gane cewa 'Yata tana cikin wani hali. Ban sanar da su zan zo ba, don ina son in yi musu ba-zata, kawai na hau jirgi na taho Nijeriya. Kwatsam ina shiga gida sai na tarar da qanwata tana dukan 'Yata da 'belt' wai saboda ta jira ruwan sama ya xauke kafin ta dawo gida. Ni ban sani ba, ashe tuni qanwata da 'ya'yanta sun mayar da yarinyata baiwarsu, suna saka ta duk wani aikin gida, har ta kai ta makaranta mai nisa kuma me arha, duk da irin kuxaxen makarantar da nake turawa, 'Yata ba ta cin abinci mai kyau, duk kayan da na turo mata masu kyau qanwata ta kulle su a akwati tana bai wa 'Yarta ta saka, ya yin da 'Yata kuma take saka tsumma. Duk kuxin da nake tura wa qanwata don kar na wahalar da ita amma sau xaya take ba ta abinci a rana, yanzu da na mutu kuma fa, wane irin riqo za ta yi wa ‘yata? A gaskiya ina ji a raina cewa ba zan iya yafe wa qanwata ba. Hatta mijinta ya sha yin faxa a kan abubuwan da take yi amma ba ta ji. Yanzu haka ina tunanin hukuncin da ya dace na yanke a kan qanwata saboda kamar yadda na faxa mu biyu kawai muka rage uwa xaya uba xaya a duniya? Idona ya rufe, amma don Allah jama’a ku taimake ni da shawara!”

Dalilin hakan shafin Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannn batu, ga kuma ra'ayoyinsu kamar haka:

Sunana (S.Girl) Sadiya Jihar Garba Kano:

Hmm.. Kaico an ci amanar zumunci, ai maganar yafiya ba ta taso ba, saboda ba ta duba zumunci ba ta ci Amana kuma ita ta aikata abubuwa da dama, waxanda Allah ya yi hani da su; Na farko ta ci amanar zumunci, na biyu tayi zambo cikin aminci, na uku an amince mata tayi ha'inci da sauransu. Kawai ta rabu da ita kunya ma ta isheta domin wallahi ko a haka ma ba za ta tava jin daxin rayuwarta ba sai ta tsangwami kanta, dama ai qarshen zalunci nadama ne. Sannan xabi'ar manzon Allah (saw) ma ya yi Allah wadai da masu hali irin nata domin tayi zambo cikin aminci ne, dan haka masu irin wannan xabi'a ku ji tsoron Allah, ku sani azabar me cin Amana daban take musamman ma akan zumunci, duba da yadda ta aminta da ita Amma ta biye wa son zuciya da ruxin shaixan ta aikata abin da zai zo ya zamar mata dana sani. Ya ubangiji Allah kayi mana tsari da cin Amana, da kuma sharrin zuciya.

Sunana Yakubu Bala Gwammaja:

Abin da zan yi mata shi ne; zan gaya mata abin da na gani, gaskiya idan na bar ta a raina zan dinga ganinta da abun a raina ba zan yafe mata ba, idan ni ne zan xauke 'ya ta na bata kulawar da ya kamata ko nayi sauri nayi auren mace mai san yara. Na xan janye tallafin ga qanwata, ko hakan zai sa tayi hankali ta gyara.

Sunana Lawal Isma'il (Lisary) Jihar Kano Rano LGA Yalwa KNARDA:

Shawarata anan matakin da aka xauka yayi tsauri duba da 'yar uwa ce ta jini kuma su kaxai suka rage a duniya wanda suke ciki xaya, amma gaskiya ta ci amana, amma tunda ita ce qarama kuma ba tada hali sosai kawai kamar yadda aka xauke 'yar a yafe mata, amma duk wani batu na taimako sai a janye hannu ko za ta gane gaskiya ta daina cin amana, tunda Allah yana son masu yafiya idan anzalunce su, sannan a nuna wa xiyar abin da ya faru ya wuce kada ta yi wa Antinta da yaranta kallon sun zalunce ta, amma a qarshe dai ina mai bata shawara da a yafe mata hakan ma zai sa ta cikin tunani, wanda za ta daina koma ba akan 'yar uwar ta ta ba, anan gaba. A kira ta su zauna ayi mata nasiha ta ji tsoron Allah a duk inda take da ma sauran mutane maciya amana irinta. Shawarata anan ita ce mu rinqa jin tsoron Allah a duk inda muke, sannan ita fa amana ba wai ta kuxi ko ta kadara ce ba, balle idan muka tabbata za mu gane cewa mun ci amana. Hatta yaran da muka haifa na cikinmu Allah ma ya ce amana ya ba mu to ina ga wanda zai yarda da mu har ya ba mu amanar abin da aka ba mu, musamman ita da aka bata amanar 'ya mace wanda yake ita ma xiya mace ce, kuma ko da asirin ire-irensu bai tonuba to wallahi akwai lokacin da kowa zai gani kuma ya sani Allah ya sa mu gane kuma mu gyara mu kawar da son zuciya.

SunanaMasa'udSalehDok­adawa:

Shawarar anan ita ce gaskiya koda za a yafe mata sai an gama yi mata kyakyawan gargaxi da kuma jan hankali akan abin da tayi ita ma ta san ba ta kyauta ba, sannan zan janye duk wani tallafi ko bada taimako na Jin qai wanda nake mata na tsawon lokaci don ita ma ta gane amfani na. Zan kira wo ta da mijinta da 'ya'yanta, da sauran danginmu na shaida musu irin zalinci da cin amanar da suka yi min. Don kada wani ya zarge ni nan gaba. Ita kuma a san abin da ta yi min a rayuwa. Shawarar ita ce su ji tsoron Allah su daina su sani cewa Amana abar tambaya ce ranar hisabi, sannan cin amana laifi ne babba, yana kawo fushin Allah, don haka ta kiyayi gaba ta gyara halinta.

Sunana Faridat Hussain Mshelia, Suleja Jihar Neja:

Haquri da yafiya su ne kan gaba, tunda Allah yana son bayinsa masu yafiya, ba wayon mutum bane kuma ba dabara ba ce ya sa aka fahimci 'yar tana cikin wani hali, rashin haqqi ne ya sa Allah ya nuna hakan, tunda har Allah ya kuvutar da 'yar a gode wa Allah. Shawarar da zan baiwa masu irin wannan halin ita ce su ji tsoron Allah su sani ko dabba ka ke kiwo bai kamata ka ci amanar shi ba balle mutum sukutum.

Sunana Muhammad Sunana Sunana Abdullahi Musbahu Gorondutse Kano:

Ya kamata a yafe mata domin duk wanda ya yafe wa wani to shi ma sai Allah ya yafe masa kurakurans­a, a rabu da ita aa xauke 'yar, kuma a fita daga harkarta, hakan zai sa ta gane. Ta yi babban laifi a rayuwarta kuma akwai yiwuwar ta gyara halinta. Masu irin wannan halin su ji tsoron Allah su sani cewa duk abin da kayi za a yi maka irinsa, kuma dole mutum ya girbi abin da ya shuka.

Sunana Abba Rano Unguwar liman Muktar Habiba (Dr. Gada Gada:

Gaskiya qanwar tayi kuskure babba kada a qi yafe mata, dan Allah yana son masu yafiya kuma Manzon Allah (s.a.w) Ya ce; Idan aka vata muku ku nuna, idan aka nemi ku yafe, ku yafe. A yafe mata a fita daga harkokinta gaba xaya. Ma su irin xabi'ar su ji tsoron Allah su daina Allah ya yi hani da zalunci.

Sunana Maryam Hussain Zariya:

Shawarata shi ne a yafe mata Allah yana san mai yafiya. A rage yi mata alkhairi saboda rowa babu kyau. Masu irin halin su ji tsoran Allah su san cewa kamatudinu Tudan.

Adakawa:

Haquri ya kamata a yi domin jini xaya ya fi qarfin wasa, dole nan gaba za ta gane gaskiya, Ita yarinyar ta ta wanne mataki za a xauka akanta. Ya kamata a yafe mata, amma a janye jiki da ita har sai ta gane kurenta.

Mustapha Haibat):

A gaskiya wannan 'yar uwa ta shiga hakkin 'yan uwantaka, sannan za ta ja wa kanta zagi bakin mutane ire-iren wannan matsala ko hali, ba shi da amfani duk wanda ya taimake ka ya gama yi maka komai a rayuwa, ballantana kuma a ce jininka na 'yar uwata, Allah ya sa mu dace ya kamata a yafe mata ko ba komai uwa xaya ta fi qarfin wasa, idon mutanen duniya ma kaxai ya ishe ta tunani, sannan idan akwai ra'ayin ci gaba da taimaka mata dan Allah a ci gaba ba dan halinta ba, sai dan iyayensu, sannan kuma duk mai irin wannan hali to ta gyara ko dan gobenta ya yi kyau, duk wadda ya taimaki wani shi ma Allah zai taimake shi, mijinta kuma Allah ya ba shi haqurin zama da ita ko dan yaransu.

Sunana Sunana iliyasu Sunana Nasara Jihar Yahya Majidaxi Abdullahi Salisu:

A ganina a yafe mata tunda 'yar uwa ce, a janye duk wani tallafi/ gudunmawa da ake bata tunda ba ta da amana. duk mai irin wannan halin ya ji tsoron Allah ya daina domin har a wajen Allah laifi ne kuma cin amana ne.

Usman Kano:

Duk da an kasance mai ikon xaukar mataki a yafe mata tunda Allah ya sa an gane kafin lokaci ya qure, Zumunci abu ne mai muhimmanci. A karve 'yar a kuma ci gaba da kulawa da yaranta ai qanwar ce ta yi laifi ba su ba, matuqar don Allah ake yi ai ba za ta fasa ba. Duk mai irin wannan halin farkon da kansa ya san bai da kwanciyar hankali ko asirinsa bai tonu yau ba ranar lahira zai iya tonuwa don haka ya ji tsoron Allah amana abu ne mai girma.

Mai

Kano Nassarawa LGA Birgade Gama-C:

Ah to! ni dai shawarar da zan iya bayarwa ita ce; tunda har ta kasance qanwa ce to bai kamata a ce an watsar da ita ba, kawai dai a xauke 'yar daga wajanta, kuma a janye mata dukkan wani tallafi da take yi mata, amma har sai ta gano kuskurenta, kuma ta nemi gafarar abin da ta aikata mata amma du da haka kar a sake xaukar amana a damqa mata har abada. Abin da ya kamata a yi mata shi ne; a janye dukkan wata hurxa da ita, amma vangaren tallafawa kuma a nesance

CI GABA A sHAfi nA 25

 ?? ?? •Faridat Hussain Mshelia
•Faridat Hussain Mshelia
 ?? ?? •Fatima Jameel Yusuf
•Fatima Jameel Yusuf
 ?? ?? •Sadiya Garba (S.Girl)
•Sadiya Garba (S.Girl)
 ?? ?? •Habibah Mustapha Abdullahi (Dr. Haibat)
•Habibah Mustapha Abdullahi (Dr. Haibat)
 ?? ?? •Maryam Hussain
•Maryam Hussain
 ?? ?? •Abdullahi Mai Nasara
•Abdullahi Mai Nasara
 ?? ?? •Lawal Isma'il (Lisary)
•Lawal Isma'il (Lisary)
 ?? ?? •Abbah Gada Rano
•Abbah Gada Rano
 ?? ?? •Isma'eel Ibraheem Isma'eel
•Isma'eel Ibraheem Isma'eel
 ?? ?? •Mas'ud Saleh Dokatawa
•Mas'ud Saleh Dokatawa
 ?? ?? Rabi’at Sidi B. • 0906383603­3 • rabiatsidi­88@gmail.com
Rabi’at Sidi B. • 0906383603­3 • rabiatsidi­88@gmail.com
 ?? ?? •Yakubu Bala Gwammaja
•Yakubu Bala Gwammaja
 ?? ?? •Usman iliyasu Majidaxi
•Usman iliyasu Majidaxi
 ?? ?? •Mukhtar Adakawa
•Mukhtar Adakawa
 ?? ?? •Musbahu Muhammad
•Musbahu Muhammad
 ?? ?? •Yahaya Salisu
•Yahaya Salisu

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria