Leadership Hausa

Labarin Asadulmulu­uk (84)

- Tare da Rabi’u Ali Indabawa 0806982489­5

Horon da Abdulmajee­d ke bai wa yara ko matasa cikin shekara guda ko biyu su zama jarumai, tuni ta wuce wannan qadamin a cikin watanni uku. Da ta cika watanni shida ta qasaita, ta gawurta, ta fahimci duk abin da ake koyarwa, ya zamto wani abin ma idan ta yi sai dai su zuba ido suna kallon ikon Allah, a wani lokacin ma lamarin har tsoro yake ba su idan ta yi wani abin.

Da yake wasu lokutan akan xan yi gwajin bajinta tsakanin xaliban, a duk lokacin da aka ce za a yi wani gwaji sai Abdussamad ya ce a haxa shi Hamdiyatu’aini. Shi kuma Abdulmajee­d ya san ta fi qarfinsa, sai ya kau da kai ya qi amincewa.

Abdulmajee­d qaqqarfa ne, amma tsufa ya fara kama shi, su kuma yara ne wasu abubuwan ma sai dai ya riqa gaya masu da baki suna gwadawa. Dama kuma suna zuwa ne a ranekun Litinin, Talata, da kuma Laraba, ranar Alhamis kuma rana ce da yake ba su tarihin magabata da gwarazan sadaukan Musulmi da irin gudunmawar da suka bayar.

Wata rana daga ranekun zuwanta koyon yaqi, ta kasance ranar Alhamis ce, suna zaune ya tara su yana yi masu huxuba kamar yadda ya saba, sai suka ji wani motsi babba daga waje kamar ana qoqarin shigowa.

“Ni fa kamar motsi na ke ji daga waje,” in ji Hamdiyatu’aini. Kafin ya buxa baki ya yi magana, sai wani dogon mutum ya shigo jikinsa buzu-buzu da gashi, sumar kansa ta rufe masa idanunsa har ba a iya ganin idanunsa, kamanninsa abin tsoro, a hannunsa a kwai wani mulmulalle­n kulki na baqin qarfe, wanda xaga sai shi kaxai. Sauran yaran suka ruga cikin wani xaki, ya zama daga Abdulmajee­d sai Hamdiyatu’aini ne suka tsaya.

To da yake wurin da suke zaune wuri ne mai girman gaske akwai abubuwa irin na qasaitattu­n sarakunan da can, sai su ga idan wannan mutum ya ja kulkin a qasa kulkin ya ci karo da wani qarfe saboda qarfin mutumin, sai su ga tartsatsin wuta ya tashi sama.

 ?? ??

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria