Leadership Hausa

Tsokaci Kan Yadda Wata Ƙanwa Ta Zalunci ‘Yar Yayarta Ta Riƙo

-

Ci gaba daga shafi na 24

ta sosai har sai tayi nadamar abin da ta aikata. Shawarata ga masu irin wannan xabi'ar ita ce su tuna cewa duk abin da ka shuka na alkairi ko na sharri babu shakka sai ka girbi kayanka, kuma kar su manta idan hakan akan ya 'yan su ta kasance yaya za su ji a ransu, ubangiji ka bamu ikon iya riqe amana tare da tausayin na qasa da mu.

Sunana Fatima Jameel Yusuf Qofar Na'isa:

Tab-xi-jam! Gaskiya ba ta kyauta ba, amma ayi haquri kar a biye mata, a duba zumuncin da ke tsakaninsu a yafe mata, domin bahaushe ya ce hannunka baya tava ruvewa ka yanke ka yar, a nuna mata kuskurenta domin idan aka barta ai ba za ta tava gyarawa ba, sai ta zaci ko tsoronta take ji ba za ta iya xaukar hukunci akanta ba. gaskiya dai me irin wannan xabi'a ta ji tsoron Allah, domin shi ubangiji baya yafe haqqin wani akan wani, shi me yafiya ne, amma tsakaninsa da bawansa.

Sunana Ibraheem Isma'el Ibraheem daga Jihar Kano Jogana:

Gaskiya a tunani na abin da ya faru da 'yar nan qaddara ce ga 'yar da kuma me 'Yar, gaskiya qanwar ba ta kyauta ba, kuma hausawa sun ce ka gina ramin mugunta daidai da kai dumin watarana kai zaka faxa, kuma ubangiji yana cewa; "innal laha ma assabirin" Allah yana tare da mai haquri, idan aka yafe mata 'may be' ta iya xaukar izina, Allah ya shirye ta ta gyara halayanta. Kuma a yi mata nashiha cewa; "idan kin mutum yayin da ki ka bada riqon waxannan 'ya'yan naki ko ki ka yi tafiya ki ka zo ki ka tarar da su za ki ji daxi", ki yi mata nasiha yin hakan zai sa ta shiryu idan Allah ya yi tana da rabo, Shawara ita ce duk abin da baka so kar ka so ka yi wa wani.

Abba Abubakar Yakubu

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria