Leadership Hausa

Darasin Da Za Mu Koya Daga Shirin Mata A Yau (1)

-

Shafukan sada zumunta, musamman manhajar Facebook da WhatsApp sun cika da muhawara da rubuce-rubuce game da wasu kalamai da ake danganta su da shirin nan na Mata A Yau da tashar talabijin ta Arewa 24 ke gabatarwa, wanda ke tattauna matsalolin da suka shafi rayuwar mata da ta iyali. Jama'a da dama sun yi ta bayyana ra'ayoyi mabambanta game da zargin da suke yi na cewa; manufofin shirin suna karo da koyarwar addinin Musulunci, da al'adar al'ummar Arewa. Haka kuma yadda masu gabatar da shirin suke zaqewa wajen bayyana rashin dacewar wasu abubuwa da suka shafi kare mutuncin mata da shawarwari­n su na neman kawo gyara, ba su dace da zamantakew­ar Malam Bahaushe ba, wanda wasu ma ke ganin sun yi hannun riga da koyarwar addini. Har ma da masu faxar maganganu na aibatawa da cin zarafi ga masu gabatar da shirin, suna musu zargin ana amfani da su ne don ya qi da addini ko rusa tsarin auratayya baki xaya. Waxannan zarge-zarge sun yi muni ainun, duba da kasancewar su mata musulmi, iyaye, kuma 'yan uwa a gare mu. Sannan a matsayin su na 'Yan'adam, suna iya yin kuskure a wani wuri, kuma akwai hanyoyi daban-daban na yin gyara ba sai an kai ga cin mutunci ba.

Kodayake tashar Arewa 24 na da 'yancin fitowa ta kare kanta, ko ta yi magana don daidaita tsakaninta da masu kallonta, ko al'ummar da suke gabatar da shirye-shiryensu gare su. Hakan ba zai hana mu yin sharhi ko tsokaci game da abubuwan da suka faru ba, don qara faxakar da jama'a, da samar da fahimtar juna. Duk da yake a ta bakin xaya daga cikin masu gabatar da shirin Halima Ben Omar, su a karan kansu suna ta qoqarin ganawa da malamai da masu faxa a ji, domin samun fahimtar juna da fayyace abubuwan da shirin yake faxakarwa a kai, don a daina musu gurguwar fahimta. Kuma in sha Allahu nan gaba zan yi qoqarin tattaunawa da wasu daga cikinsu, don kawo muku sakamakon abubuwan da suka biyo baya, daga vangarensu.

Sai dai kafin lokacin zan so mu fahimci cewa; kowacce kafar watsa labarai na da manufofi da dalilan da ya sa ake kafata ko watsa shiryeshir­yenta. Sannan kafin a fara kowanne shiri sai hukumomin da abin ya shafa sun tantance su, sun kuma tabbatar da tsarin ayyukansu bai ci karo da dokokin qasa ko tsarin mulkin Nijeriya ba, wanda a cikinsa an tsare mutuncin kowanne addini da al'ada. Kodayake tun bayan fitowar tashar a shekarar 2014 'Yan Nijeriya da dama sun riqa nuna shakku da kokwanto kan manufofin kafuwar tashar mai amfani da harshen Hausa tsawon awa 24, musamman jin cewa tana da alaqa da qasar Amurka. An yi ta zarge-zarge kan cewa tashar na kawo shirye-shirye masu gurvata al'adu da tarbiyya, musamman shirin nan na waqe-waqen hip hop wanda Aminu Abba Umar Nomis Gee ke gabatarwa, wato Top 10, da wasu shirye-shirye da suka shafi wasan kwaikwayo na Daxin Kowa, Manyan Mata, da kuma shi wannan shiri na Mata A Yau.

Zan so in taqaita bayanai na kan shirin Mata A Yau, wanda a kansa ne wannan dambarwa ta taso, kuma kamar yadda wani fitaccen marubuci, xan kishin Arewa, kuma mai faxa a ji a harkokin ci gaban al'umma, Dr Aliyu Tilde ya rubuta a shafinsa na Facebook, "Wannan yana daga shiryeshir­ye masu amfani ga al’umma, inda mata suke tattauna matsalolin­su kuma suke kiran qwararru don qarin haske. Na kan kalla, kuma na kan qaru sau da yawa." Nima zan iya cewa, ina kallon shirin Mata A Yau, kuma ina bibiyar yadda suke gabatar da tsarin shirin, duk da kasancewar ina da bambancin ra'ayi da su a wasu vangarori. Amma wannan ba zai hana in bayyana muhimmanci­n shirin ga rayuwar mata ba, da kuma kyakkyawan tsarin da aka yi wajen gina tsarin gabatar da shirin. Lura da yanayin bambancin shekaru da gogewar matan da ke gabatar da shirin, kowacce da vangaren da ta fito da kuma gungun matan da take wakilta. Don haka haxin gambizar matan da suke gabatar da shirin, shi ma wani abu ne muhimmi, da yake nuna manufar shirin.

Sai dai duk da qoqarin da tashar ke yi wajen kiyaye koyarwar addini da al'ada, ba a rasa wani lokaci da akan samu kurakurai a wasu maganganu da akan yi amfani da su. Wannan kuma dole ne mu yi musu uzuri kasancewar duk xan'adam tara yake bai cika goma ba. Kamar lafazin da ake qorafin xaya daga cikin masu gabatar da shirin Aisha Umar Jajere ta yi amfani da shi, inda ta nuna cewa idan mata ba ta gaishe da mijinta ba, shi me zai hana ya gaisheta! Wannan a ra'ayin wasu masu tsokaci da kallon shirin ya savawa tarbiyya da zamantakew­ar auren Bahaushe, kuma yanayin kalaman nata za su iya sa mata su riqa raina mazajensu. Kodayake na san ba hakan ne manufarta ba, sai dai qoqarin kawo maslaha tsakanin waxannan ma'aurata da aka ce maigidan ya aika da qorafi a kan matarsa ba ta gaishe shi. Kuma ko nima na goyi bayan ra'ayinta, don bai kamata rashin gaisuwa ya kawo savani ba, musamman tunda ma'auratan suna zaune lafiya da juna.

 ?? ??

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria