Leadership Hausa

Yaya Hukuncin Amfani Da Motar ‘Office’ A Harkokin Ƙashin-Kai?

-

Assalama alaikum Malam ya halatta mutum ya zuba mai a motar ma'aikatar da yake aiki, ya kai matar-sa unguwa, ko ya je harkokinsa na yau da kullum a ciki?

Wa alaikum assalam. To dan'uwa kwamitin fatawa na din-din na Saudiyya ya ba da fatawa cewa: Bai hal-atta mutum ya yi amfani da motar gwamnati wajan harkokinsa na yau da kullum ba, tun da ba dan haka aka tanaje ta ba, kamar yadda ya zo a fatawa mai lamba ta: 16594.

Sheikh Ibnu Uthaimin yana cewa: "Ko da shugabanka na office ya halatta maka, bai halatta ba, tun da ba huruminsa ba ne, ba kuma mallakinsa ba ne, kamar yadda ya zo a: Lika'u babil maftuh: 238.

Yana daga cikin siffofin muminai kiyaye amanar da aka damka a hannunsu, kamar yadda aya ta: 8 a su-ratul Muminuna ta tabbatar da hakan.

An rawaito cewa Khalifa Umar dan Abdul'aziz ba ya amfani da fitilar gwamnati a harkokinsa na kashin-kai, ko da kuwa bako ya yi bai zai yi hira da shi da fitilar gwamnati ba, in har ba matsalolin da suka shafi jama'a za su tattauna ba, wannan sai ya nuna takatsants­an da dukiyar office yana daga cikin tsentseni.

Duk wanda ya wadatu Allah zai wadatar da shi, wanda ya kame Allah zai kamar da shi, Wadatar zuci taska ce da ba ta karewa.

Allah ne mafi Sani.

Juma'a 15 Safar Asabar 16 Safar Lahadi 17 Safar Litini 18 Safar Talata 19 Safar Laraba 20 Safar Alhamis 21 Safar

Asuba

05:29 05:29 05:29 05:29 05:29 05:29 05:29

F/Rana Azuhur La’asar Magriba Isha’i

06:39 06:39 06:39 06:38 06:38 06:38 06:38 12:47 12:46 12:46 12:46 12:45 12:45 12:45 03:52 03:50 03:49 03:48 03:47 03:46 03:47 06:54 06:54 06:53 06:53 06:52 06:52 06:51 08:00 07:59 07:59 07:58 07:58 07:57 07:56

Majiyarmu: Muslim Pro

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria