Leadership Hausa

Babu Abin Da Na Fi So Kamar Faranta Ran Marayu Da Raunana – Adesuwa Udo

-

MADAM ADESUWA OGECHI UDO, matashiya ce wadda ta tashi cikin maraici da rashin gata, amma hakan bai hana ta samun yin karatu har zuwa matakin Jami’a ba. Sannan ta yi gwagwarmay­a a vangarori iri dabandaban, wanda ya kai tag a zama shahararri­yar ‘yar fim na Hausa da kuma Turanci. Bugu da qari kuma, a halin yanzu ita ce Shugabar Gidauniyar ‘Empowermen­t Foundation (ELS)’, wacce har Masallaci ta gina tare da tallafawa marasa galihu ba tare da nuna banbancin addini ko qabila ba, duk kuwa da kasancewar ta na kirista wadda ba musulma ba. Ta samu kyatuka da lambar yabo a qashashen Turai kamar Ingila da Amurka da kuma nan gida Nijeriya. Wakilinmu MUSTPHA IBRAHIM KANO, ya samu zantawa da ita kamar haka:

Za mu so mu jin cikakken sunanki da taqaitacce­n tarihinki a taqaice?

Sunana ADESUWA OGECHI UDO, an haife ni a Kano amma iyayena mutanen Jihar Benin ne, na yi makarantar Firamare a kwakwaci daga nan na wuce Sakandire ta Xanware duk a nan Kano, daga nan kuma sai na tafi Jami’ar Jos, inda na karanta ilmin fannin sana’ar wasan kwaikwayo (Film), bayan kammala Digirin nawa sai na kama hanya Legas, inda na fara fitowa a fina-finan Turanci (Nigerian Film). Daga nan ne kuma sai likkafa ta ci gaba, domi aqalla na yi fina-finai xai-xai har guda 25, na Hausa kuma sun kai 11. Kazalika, daga cikin Fina-finan da na yi akwai; Lafiya uwarjiki, Musa Bakanike da sauran makamantan su, cikin waxanda na fara shirin wasan Hausa da su a matsayinsu na jarumai akwai Baba Ari, Ali Nuhu, Hannatu Bashir da sauran su.

Wane suna aka fi sanin ki da shi a Fina-finanki?

Madam ELS, wanda kuma shi ne sunan Gidauniyar­ta (ELS Empowermen­t Foundation), wadda ke samar da ayyuka da tallafawa Marayu raunana da sauran marasa galihu a fannoni daban-daban.

Me ya jawo hankalinki kika kafa wannan Gidauniya?

To, magana t gaskiya ita ce na ta so cikin matsala ta rayuwa, domin kuwa sai da na yi tallan ruwan sanyi da ake xaurawa a leda, na qwandala qwandala, sai na sayar sannan ni da Kakata za mu samu mu ci abinci, duk sanda aka ce ruwan babu sanyi haka zan yi ta faman kuka, idan na koma gida Kakar tawa sai ta rarrashe ni da ce da ni ka da ki damu Allah zai ba mu abin da za mu ci. Sannan a hakan idan ta yi abinci, sai ta xiba ta rararraba wa waxanda ba su da shi, haka nan idan ta yi miya da nama, shi ma sai ta rarraba wa mabuqata. Kazalika, tallan ruwan nan haka nake xauka tun daga cikin Sabon gari wajen titin Sarkin yaqi har zuwa ‘Yan kura da sauran wasu gurare daban-daban a qasa. Da haka dai cikin ikon Allah aka rayu har aka yi makaranta.

Ko za mu iya sanin tsakanin Marayu da sauran Raunana nawa wannan Gidauniya taki ta tallafawa?

Babbar magana! Gaskiya abin kamar da wuya, dalili kuwa zai yi wuya na san adadin mutanan da suka amfana da wannan Gidauniya, amma dai qiyasin da na yi zi iya kai wa kinanin dubu xari biyu (200,000), domin mu kan fita mu yi sansani, mu tattara mutane masu rauni wasu mu koya musu sana’o’i mu kuma ba su jari, musamman mata iyayen Marayu da sauran su. Mun yi wannan a wasu Unguwanni na Birnin Kano, kamar

Unguwar Sabon gari, Birget, Unguwa Uku da sauran makamantan su tare da raba musu kayan sana’o’i. Ko a shekarar da ta gabata, mun yi irin wannan sansani a Gidan Makama da ke kusa da Fadar Kano, cikin Qaramar Hukumar Birni da kewaye, ta hanyar tara xaruruwan mata muka koya musu sana’o’i iri daban-daban, muka kuma ba su jari da atamfofi da kayan abinci, baya ga xaukar nauyin abincinsu na kwana bakwai, akwai kuma lokacin horar da su sana’o’in kamar yadda na faxa maka a baya.

Har ila yau, bayan Kano wannan Gidauniya ta ta je har wasu jihohin don taimaka wa raunanan. Akwai jihata ta asali Jihar Benin, sai Bayalsa, Ibadan da kuma Jihar Kaduna, duk wannan Gidauniya ta je ta yi aikin bayar da tallafi da kuma koya sana’o’i da bayar da jari ko kayan sana’a da suka haxa da; Injin kitso (drier), Injin Markaxe da sauran makamantan su, domin mata su samu abin dogaro da kawunansu.

Ko akwai wasu ayyuka da wannan Gidauniya ta yi tun bayan kafuwarta?

Kamar wasu watanni da suka shuxe ina Qasar Ingila, na ba da umarnin a gina masallaci a nan cikin Sabon gari, domin amfanin al’ummar musulmi waxanda muke tare da su, sannan na nemi alfarmar mai Martaba Sarkin Kano, a zo a buxe shi. Wannan masallaci yana nan a cikin Sabon gari, titin Sarkin yaqi, sai kuma rumfuna guda takwas da na samar domin anfanin leburori waxanda ke zama a ciki kafun su samu aiki ko bayan sun dawo daga qwadagonsu, musamman saboda maganin rana ko lokacin damuna ko kuma shan iska duk qarqashin wannan Gidauniya.

Haka zalika, akwai kuma tsarin gangami da nake jagoranta na shiga Unguwar Sabon gari tare da haxin guiwar masu ruwa da tsaki, domin wayar da kawuna da kuma yaqar al’adar nan ta sha da ta’ammali da miyagun qwayoyi da kuma sace-sace, musamman na wayoyi da karuwanci da sauran makamantan su.

A irin wannan gangami da muke fita ne na ci karo da wani abin takaici da kuma ban tausayi, inda na haxu da wata mata mai shekara 68 tana karuwanci. Na ce da ita ke ya haka? ta ce da ni yanzu haka ma duka aka yi mata; aka kuma xauke kayanta ciki har da wayarta, bayyan an yi lalata da ita na tsawon awanni 24, aka kuma hana ta kuxinta duk kuwa da cewa a kullum tana baiwa Otal xin da take kwana Naira 1000. A nan ne bayyana min cewa, da zarar ta samu jari za ta koma jiharsu ta

Akwa Ibom ta kama sana’a.

Kafin kammala wannan tattaunawa da ke Ogechi a sana’arki Ta Fim me ya fi faranta miki rai?

Gaskiya abubuwan da suke faranta min rai suna da yawa, amma dai wannan tallafi da Uban giji ya ba ni dama nake yi ya fi faranta min rai. Sa’annan kuma kyatukan yabo da na samu a Qasashen Ingila da Amurka

da kuma nan gida Nijeriya, musamman

Kano ba qaramin abin alfahari ne a wurina ba. Kamar a shekarar 2022, na samu kyauta a matsayin mace wacce ta fi taimako a Afirka baki-xaya (The Best Women Philanthro­py Award) sai kuma kyautar lambar yabo a vangaren Fim ita ma da na samu a Ingila ta (ZAFA ZAFA Award) da kuma wata kyautar daga ‘ICAN’ da sauran qungiyoyi daban daban a Nijeriya da kuma wajenta. Wannan dalili yasa mu ma muka baiwa Ubanmu, uban kuma wannan Gidauniya mai Martaba Sarkin Alhaji Aminu Ado bayero, kyautar girmamawa ta ‘ELS’ dangane da gudunmawa da haxin kan da muke samu daga wurin sa.

Mene ne ba za ki iya mantawa da shi a rayuwarki ba?

Abubuwan da ba zan manta da su ba suna da yawa, amma abin da ya fi damuna nake jin badaxi koda-yaushe shi ne, lokacin da ba ni da halin taimakawa, sai wata mata wadda mijinta ya mutu ya bar ta da ‘ya’ya biyar, ‘yan’uwan mijin nata suka kwashe dukiyarsa suka kama gabansu. Ko shakka babu, wannan mata ta shiga matuqar tashin hankali. A daidai wannan lokaci ta zo wurina na taimaka mata, ba ni da halin d azan taimaka mata, ga shi yanzu kuma ban san a inda zan same ta ba. Don haka, duk lokacin da na tuna wannan yana ba ni tausayi da kuma takaici. Sai kuma wani tsoho da ya zo guna ya ce shi ma na taimaka masa da Naira 1,500, na ce da shi Baba mai za ka yi da shi? ya ce zai je ya yi cefane ne gidansa saboda babu abin da za a ci, sannan ya zo neman aikinsa na gyaran fanfo; bai samu ba.

Me kika fi so ko qauna a rayuwarki?

Abin da na fi so da qauna a rayuwata shi ne, ganin na taimaka wa Marayu da raunana marasa galihu suna cikin farin ciki tare da jindaxi. Idan kuma t akama na shiga cikin su muna rawa, muna nishaxi da murna, kai wannan yana faranta min rai qwarai da gaske a rayuwata.

A qarshe wane saqo kiki da shi ga gwamnatoci da sauran al’umma?

Saqona a nan shi ne, Shugaban Qasa, Gwamnonin Nijeriya da Shugabanin Qananan Hukumomi da sauran Shugabanni­n Addini, su dubi halin da al’umma suke ciki na matsin rayuwa, su taimaka musu ta

hanyar koya musu sana’o’i tare da ba su jari da kuma tallafin kayan Abinci, musamman ga raunana da sauran Marayu. Haka nan, su ma mawadata su yi qoqarin tallafa wa marasa shi da sauran mabuqata. A taqaice wannan shi ne kaxai abin da zance iya cewa.

 ?? ?? •Wasu daga cikin waxanda suka samu tallafin gidauniyar
•Wasu daga cikin waxanda suka samu tallafin gidauniyar
 ?? ?? •Madam Adesuwa na miqa wa Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero Kyautar Karramawa a matsayin Uban qungiya
•Madam Adesuwa na miqa wa Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero Kyautar Karramawa a matsayin Uban qungiya
 ?? ?? •Madam Adesuwa Ogechi Udu
•Madam Adesuwa Ogechi Udu

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria