Leadership Hausa

Dakta Soky Amachree: Ɗan Kishin Ƙasa Jakada Nagari

-

Idan ana maganar ‘yan kishin qasa, Dakta Soky Amechree na da ban ne shi, domin kuwa mutum ne da za a iya suffanta shi a matsayin wani ginshiqi ko jakada na gari, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunqasa harkokin kimiyya da fasaha da kuma masana’antu, tun kusan shekaru talatin da suka gabata a tsakanin Nijeriya, Kanada da sauran qasashe dabandaban a duniya.

Mutum ne wanda ya samu shaida daga wurin aqilan mutane masu ilmi, a matsayin shugaba na gari wanda ya samu qwarewa a fannin ayyuka daban-daban. Kazalika, Daktan ya fito ne daga Jihar Ribas ta yankin Neja Delta, wanda ya bayar da gudunmawa a vangaren da ya shafi qasa bakixaya tare da ci gaba a fannin masana’antu masu zaman kansu da gwamnati da kuma harkar koyarwa a manyan makarantu tun shekaru talatin baya da suka wuce.

Kaxan daga cikin ci gaban da ya kawo sun haxa da samar da kyakkyawar alaqa tsakanin Nijeriya da Kanada, wanda hakan ya yi sanadiyyar samar da Hukumar Kula da Jakadancin Kanada a Abuja da Gwamnatin Alberta da kuma harkokin man fetir da gas a Qasar Kanada tun shekarar 1993.

An samu wannan nasara ce tare da taimakon wasu daga Qasar ta Kanada, Mista Earl Hickok, Shugaban Kamfanin ‘Energy Services Ltd of Calgary’, Alberta da kuma Kanada. Mista Earl Hickok da Dakta Soky Amachree suka jagoranci xaukar wakilan Nijeriya sama da goma zuwa Qasar Kanada, a matsayin yawon buxe ido a vangaren da ya shafi harkokin Ilmin Kimiyya da Fasaha, tun shekaru 20 kafin a samar da alaqar kafa kamfanin harkokin man fetir da gas a Nijeriya.

Mista Earl Hickok, mutum ne jajirtacce wanda ya sha alwashin taimaka wa Nijeriya a wannan vangare. Ya kuma taimaka da aljihunsa, inda ya vatar da sama xaruruwan dubbannin dalar Amurka don ganin ya taimaka wa Nijeriya shekaru 20 da suka gabata. Hankalinsa ya kwanta tare da yarda wajen ganin an qulla harkar kasuwanci da Nijeriya tare da Dakta SOKY Amachree. Kazalika, yana da yaqinin cewa Nijeriya qasa ce mai albarka, shi yasa ya dage wajen bayar da tasa gudunmawar don ganin ta ci gaba ta hanyar kimiyya da fasaha, musamman ma a vangaren da ya shafi harkokin man fetir da kuma gas.

Haka zalika, xaya daga cikin nasarorin da aka samu na ziyarar da aka kai Qasar ta Kanada ya haxa da, kafa Makarantun Gwamnatin Tarayya na man fetir guda biyu da kuma Makarantun Kimiyya da Fasaha a fannin Gas cikin Jihar Ribas (Bonny) da kuma Jihar Bayalsa (Ekowe), tare da haxin guiwar rukunin kamfanonin Kanada ‘Canadian Oil & Gas Polytechni­c’ da kuma Kamfanin ‘Southern Alberta Institute of Technology (SAIT).’

Sannan, an sake samun haxin guiwa tsakanin Kamfanin DPR (Department of Petroleum Resources), ‘Alberta Energy and Utilities Board’ da kuma Jami’ar Calgary Energy da sauran makamantan­su.

Har wa yau, akwai kuma haxin guiwa tsakanin manyan makarantun gaba da sakandire da suka haxa da ‘Southern Alberta Institute of Technology’ da kuma Makarantun Kimiyya da Fasaha guda huxu daga Jihohin Nijeriya da ya haxa da Jihar Bayelsa, Lafia a Jihar Neja, da kuma Jihar Gombe.

Haka nan, idan aka yi la’akari da irin gagarumar gudunmawar da Dakta Amachree ya bayar, musamman a yankunan Neja Delta a matsayinsa na Babban Manajan Daraktan Kamfanin ‘Sigma Technical Agencies Ltd’ a Fatakwal ta Jihar Ribas tare da taimakon Farfesa E. O. Okoro, Shugaban Tsangayar Koyon Karatun Likitanci a Jami’ar Ilorin, sun rubuta wa Ma’aikatar Neja Delta qorafinsu tare da jan hankali, domin samar da hanyar warware rikicin da ke addabar su tare da samar kyakkyawar hanyar zaman lafiya a tsakaninsu.

A takardar da suka rubuta mai xauke da kwanan wata na 17 ga watan Yulin 2009, Amchree da Okoro sun ja hankalin mambobin al’ummar Neja Delta da kuma ‘yan qabilar Ijaw, waxanda aka ciro daga Jihar Ribas da Delta, kan cewa dukkanin banbance-banbance da rashin jituwar da ake samu, kai tsaye ya shafi matsalar tattalin arziqi ne, wato rashin wadata.

Ya qara da cewa, “Babban abin da ke kawo rashin jituwar shi ne, rashin samun isasshen abin kashewa na yau da kullum, duk kuwa da cewa man fetir da gas daga wurinsu ake haqowa, amma sai a baiwa wasu baqin haure dama suna haqa suna sayarwa wasu Kamfanoni na Qasashen Waje, cikin xan qanqanin lokaci suna zama biloniyoyi, su kuma mazauna wajen waxanda ke ganin qasar tasu ce na ci gaba da zama cikin mummunan talauci da quncin rayuwa.

 ?? ??

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria