Leadership Hausa

Za A Yi Dokar Hukunta Masu Qona Alqur'ani A Denmark

-

Gwamnatin qasar Denmark ta xauki aniyar haramta qona Alqur'ani Mai Tsarki a bainar jama'a bayan jerin qone-qonen da suka haddasa yamutsi a qasashen Musulmai.

Ministan shari'ar qasar, Peter Hummelgaar­d ya ce irin wannan mataki na qona Alqur'ani ya cutar da Denmark kuma ya sanya al'ummarta cikin hatsari.

Dokar wadda ake shirin kafawa za ta mayar da duk wani matakin wulaqanta Alqur'ani ko Littafin Bayabul, matsayin laifi da za a iya hukunta mutum, ta hanyar cin tara ko xauri a gidan yari tsawon shekara biyu ko sama da haka.

Gwamnatin qasar mai sassaucin ra'ayi ta ce tana son aika wani saqo ga al'ummar duniya.

Ministan harkokin waje, Lars Lokke Rasmussen ya ce Denmark ta shaida jerin zanga-zanga har 170 cikin 'yan makonnin nan, a ciki har da qona Qur'anai a gaban ofisoshin jakadancin qsashen waje.

Hukumar leqen asirin Denmark ta yi gargaxin cewa al'amuran da suka faru a baya-bayan nan sun tsananta barazanar kai harin ta'addanci.

Ita ma qasar Sweden mai maqwabtaka ta shaida jerin qone-qonen Alqur'ani kuma jami'an tsaronta sun yi gargaxin cewa al'amuran tsaro za su tavarvare. A watan Yuli, masu zanga-zanga sun cinna wuta kan ofishin jakadancin­ta a Iraqi.

Sai dai duka qasashen Denmark da Sweden sun jinkirta xaukar mataki a kan qone-qonen saboda dokokinsu na sassaucin ra'ayi a kan 'yancin faxar albarkacin baki.

A shekarun 1970 ne Sweden ta soke dokarta ta haramta savo. Gwamnatin birnin Copenhagen ta yanke shawarar xaukar mataki bayan qarin qone-qonen Alqur'ani a qarshen watan Yuli cikin Denmark da Sweden.

Qungiyar Qasashen Musulmai ta Duniya (OIC) ta yi kira ga mambobinta su xauki matakan da suka dace a kan qasashen da ake wulaqanta Alqur'ani.

Ministan shari'ar ya dage a kan cewa qudurin canza dokar ba zai shafi furuci ko rubutun bayyana albarkacin baki ko zanen shaguve ba. Sai dai ya ce qona littattafa­n addinai ba su da wata manufa sai haifar da varaka da haddasa gaba.

"Wani ginshiqin al'amari ne ga tsarin dimokraxiy­yarmu cewa mutum na da 'yancin faxar albarkacin bakinsa," a cewar Mataimakin firaminist­a Jakob Ellemann-Jensen. "Kuma ya kamata mutum ya riqa sara, yana duban bakin gatari."

Denmark ba za ta tsaya ta zuba ido kawai ba a lokacin da irin waxannan abubuwa masu naqasu ga tsaron qasar ke faruwa, ya qara da cewa.

Firaminist­an Sweden, Ulf Kristersso­n, ya ce gwamnatin Stockholm ba za ta xauki irin wannan mataki na maqwabciya­rta ba, saboda hakan mai yiwuwa zai buqaci yi wa tsarin mulkin qasar garambawul.

Ministan shari'ar Sweden Gunnar Strommer ya faxa wa manema labarai cewa shawarar sake nazari kan dokar tabbatar da kwanciyar hankalin jama'a, ta yi daidai.

Gwamnatin qasar na son canza dokar domin ta haramta tarukan da za su yi barazana ga tsaron al'ummar Sweden.

Ministoci a Denmark sun quduri aniyar yi wa dokar sauye-sauye ranar 1 ga watan Satumba, sannan su gabatar da sauye-sauyen ga majalisar dokoki don zatarwa kafin qarshen wannan shekara.

Ana sa ran, haramcin za a yi shi ne a sashen kundin aikata laifuka da ke hana 'yan qasar muzanta wata qasar waje, ko tutarta da sauran wani tambarinta.

 ?? ??

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria