Leadership Hausa

Sirrin Gaishe Da Miji

-

Akwai sirruka da dama da ya kamata a ce uwargida ta san su ta kuma yi koyi da su; waxannan sirrika sun hada da tsafta, ladabi, biyayya, iya Magana, sai kuma uwa gaisuwa. Za mu fi xaura wannan maudu'i kan gaisuwa ne. Wanda gaisuwar nan fa ta qunshi abu biyu da suka haxa da gaisuwar tambayar ya aka ta shi wato ina kwana, Allah ya tsare a dawo lafiya, sannan akwai gaisuwar sannu da dawowa.

Uwargida ko kinsan cewa sirrin da ke tattare da ina kwan, sannu da dawowa?

Idan ba ki sani ba, to bari ki ji. Idan gari ya waye kika yi sallar Asuba, juya ki ce wa maigidanki ina kwana ko ba ki yi dogon gaisuwa ba, sannan ki sauke nauyin shiga kitcin, ki haxa abun kari. Bayan kin gama, ya ci ya kimtsa, raka shi bakin qofa bi shi da a dawo lafiya Allah ya tsare. Uwargida ke kanki a wannan ranan sai kin ji sauyi a zamantakew­arku. Bayan ya dawo, sannu da zuwa ya zama kalmar farko.

Da yawan mata akwai abun da ba su fahimta ba wajen gaishe da miji wanda yake qara wa mace daraja da kima, sannan hakan na qara sa miji ya sake tabbatar da irin ingantacci­yar tarbiyar da aka ba ki a gidansu.

Haka zalika, gaishe da miji yana sa uwargida ta kasance ko laifi ta yi masa ya kan yi qoqari ya danne zuciyarsa wajen ganin ya xaga miki qafa.

Kalmar sannu da dawowa, in dai kin riqe wannan kalma, to za mu iya kiransa da 'sirrin mallaka', yana dawowa ki kasance bakinki ya zama kalmar sannu da dawowa shi ne abu na farko da zai furta. Amma wasu mata ka fin su ce komai, qora fi ne abun da zai fara fita a bakinsu, wanda hakan ba tarbiyya ba ne.

Ko da dai ana cewa gaisuwa al'ada ce, amma Hausawa na cewa ‘yaba kyauta tuqwici’, idan aka duba komin zafi, ruwa, iska miji zai fita ya nemo abun da za ku ci ke da yara, to ashe in har zai yi muku wannan qoqarin ke kuma matsayinki na uwar al'umma wacce aka fi sani da tausayi da sanin ya kamata, sai ki yi qoqarin nuna tausayawan­ki a kansa. Kalmar sannu da dawowa a gareshi zai qara masa qwarin giwa wajen nemo muku abin sawa a bakin salati. Amma wasu matan miji na shigo za a fara ba shi bayanin maggi ko shiri ko manja ya kare.

Ta vangaren ‘ya’ya kuwa, yi qoqari ki nuna musu tausayin ubansu ta hanyar koya musu gaisuwa da kuma sannu da zuwa. Idan kika yi qoqari kika nuna musu hakan, ko cikin mutane sai kin ji ana yabon 'ya'yanki, kuma shi ma mijin a duk sanda zai fita zai kassnce cikin qwarin gwiwa da annashuwa. Uwargida an san cewa tsakanin harshe da hakori ma ana savawa, saboda haka tsakanin ma'aurata ma ana samun savani, to amma kar ki bari vacin rai ya yi tasiri a zuciyarki, ki yi qoqari ko faxa kuka yi ki kasance mai daxin kalamai ga mai gidanki.

 ?? ??

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria