Leadership Hausa

Al’ummar Ƙaramar Hukumar Dala Sun Yaba Da Ayyukan Raya Ƙasa Na Gwamnatin Kano

- Daga Ibrahim Muhammad Kano

An yi kira ga al'ummar jihar Kano su dage da addu'a ta miqa al'amuransu ga Allah akan irin zalunci da wasu ke son kitsawa a roqe shi ya kawar da makircinsu dan cigaba da amfanar irin alkhairai da ake ganin Gwamnatin Abba kabir Yusuf ta kawo cikin yan kwanaki a jihar Kano.

Jagoran kwankwasiy­ya na Dala shugaban jam'iyyar NNPP na qaramar hukumar Dala, Alhaji Xayyabu Ahmad Maiturare Galadiman Gado da masun Kano ne ya bayyana hakan.

Ya ce akwai wurare da dama da basa samun ruwan fanfo shekara da shekaru a baya, amma zuwan Gwamnatin nan ana samun ruwan. A cikin wannan xan taqaitacce­n lokacin anga irin wannan alkhairi in aka shekara za'a ga nunkin ba nunkin hakan ne.

Ya yi nuni da yadda ayyukan alkhairai da yawa an xauko ana yi da suka haxa da biyawa ‘yan makaranta kuxin makaranta dana jarabawa wannan za a fitar da wasu ma waje karatu kuma akwai abubuwa da ake aiwatarwa da za'a ga tasirinsu nan take, wasu ma sai bayan shekaru.

Xayyabu Ahmad Maiturare ya kafa musali da cewa kamar waxanda aka kai karatu qasashen waje lokacin Gwamnati Kwankwaso yanzu ana ta ganin alkhairans­u wasu na waje suna aiki wasu na cikin gida suna yi.

Ya ce yanzu kuma irin yanda ake biyan albashi a kan lokaci da masu fansho da aka daina yankar musu kuxi, ya kamata mutane dag su riqa addu'a dan irin waxannan alkhairai su cigaba da wanzuwa a tsakanin al'ummar jihar Kano.

Alhaji Xayyabu Ahmad Maiturare ya ce su a qaramar hukumar su ta Dala a qarqashin wannan Gwamnati ta Abba sun sami gurbin muqamai da yawa da basu tava samun irin wannan tagomashi a jihar Kano a.bays ba kamar wannan.

 ?? ?? •Alhaji Xayyabu Ahmad Maiturare yayin taron addu'a tare da sauran jama'a a wajen addu'ar
•Alhaji Xayyabu Ahmad Maiturare yayin taron addu'a tare da sauran jama'a a wajen addu'ar

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria