Leadership Hausa

Gidauniyar Ambasada Munzali Abubakar Dambazau Ta Ɗauki Nauyin Koya Wa Mata 251 Sana'oi

- Daga Ibrahim Muhammad Kano

Xan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar qaramar hukumar Birni, Hon.Sarki Aliyu Daneji ya yaba wa Gidauniyar Ambasada Munzali Abubakar Danbazau bisa irin gudummuwa da take bayarwa ga ci gaban al'ummar jihar Kano.

Xan majalisar ya bayyana haka ne wajen qaddamar koya wa mata guda 100 daga cikin guda 250 da Gidauniyar ta xauki nauyin horar da su sana'oi dogaro da kai da aka gudanar a makarantar firamare ta ‘yan gurasa da ke Jakara.

Sarki Aliyu Danaji ya ce dama Ambasada Munzali ya jima yana baiwa tafiyar kwankwasiy­ya goyon baya ta aiwatar da ayyukan jinqan al'umma na tallafa wa marayu da mabuqata a jihar Kano.

Ya ce shi Munzali mutum ne mai kishin al'umma da mazavarsa yanzu kuma ya xauki nauyin koyawa mata sana'oi ganin wannan kishi nasa tasa shi a matsayinsa na xan majalisa ya tallafa musu da N1,000,000 dan qarfafa musa gwiwa don ya cigaba da wannan abu da yake.

Hon. Sarki Aliyu Daneji ya ce a matayinsa na xan majalisar birni sun fahimci babban matsalarsu shi ne daba da sace-sacen waya shi yasa suka janyo matasa a jiki suka nuna musu suma za su iya zama wani abu waxansa suka ci jarabawa a ciki suka kaisu makarantu dabandaban don su zama nagari akwai waxanda nan gaba kaxan za a basu jari su daina zaman banza wannan za ta taimakai jihar Kano kuma koyi ne da suke ga jagoransu Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf kuma gudummuwar Gwamna na nan tafe data nunka tasu.

Shima a jawabinsa shugaban Gidauniyar Ambasada Munzali Abubakar Danbazau ya ce zama da ya yi da xan majalisar birni wanda yake xinbin aikace-aikace tun bai je majalisa ba har zuwansa ya bashi qarfin gwiwa wajen zaburantar dashi wajen tallafawa al'umma.

 ?? ?? • Xan majalisar jihar Kano mai wakiltar Birni, Sarki Aliyu Daneji da Ambasada Munzali Abubakar Danbazau a yayin taron
• Xan majalisar jihar Kano mai wakiltar Birni, Sarki Aliyu Daneji da Ambasada Munzali Abubakar Danbazau a yayin taron

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria