Leadership Hausa

Ƙungiyar Tallafa Wa Marayu Ta Gandun Albasa Ta Yi Walima Karo Na 17 Ga Marayu 100

- Daga Ibrahim Muhammad Kano

Qungiyar tallafa wa marayu da gajiyayyu ta Gandun unguwannin Gandun albasa da kewaye ta gudanar da walimar karo na 17 ga marayudaqu­ngiyartake­shiryawadu­oshekara.

Malam Bashir Muhammad Ingawa magatakard­ar kwamitin ilimi na qungiyar da a qarqashins­a ne ake shirya wakilimar ya ce a qarqashin hadafin qungiyarne taga ya dace ta samarwa marayu wani lokaci da za suyi nishaxi da jin daxi. da walwala shi yasa ake gudanarda walima na walimar na yara marayu 100 kowace shekara da wannan shi ne karo na 17.

Ya yi nuni da cewa shekaru huzu da kafa qungiyar aka soma irin wannan walima ana gayyato yara da iyayensu da iyayen qungiya a taru ayi faxakarwa a yi nishaxi na bana ma ya bambanta dana baya an shigo da abubuwa sababbi da ba'ayi a baya da ya qarawa walimar armashi.

Ya ce bana duba da halinda ake ciki an gabatar da salloli da yara da addu'a ga qasa na neman xaukin Allah ya kawo sasauci kan halin da ake ciki. Sannan an gabatar da musabaqa ta Qur'ani da azkar a tsakanin marayu an zavo yara uku aka zavi gwarzo a ciki guda xaya.

Ya ce an kawo dawaki da raqumi da yara suka riqa dan samun nishaxi da samarda injin alawa da gurguru nan take ana rabawa yara.A baya har yawon buxe ido ma ake kaisu zuwa kantin shoprite su xanyi sayayya da wasanni an tava kaisu wajen shaqatawa da wasanni a dawakin kudu.

Ya ce walimar tana tasiri wajen sa marayun walwala da jin daxi harma iyaye na bibiya yau she za'ayi walimar ,saboda farin ciki da suke samu hatta iyayen qungiyar da suke tallafawa da dukiyoyins­u suna son tsarin saboda taimakawa da suke da son sa nishaxi ga marayu da suke.

Malam Bashir Muhammad Ingawa ya godewa Allah bisa taimako da yake da godewa masu tallafawa da suka fahimci amfanin tallafawa marayu, sannan da yawa masu tallafawa in anje sune ke yin godiya saboda suna jin daxin tallafawar.

Ya godewa marigayi Alhaji Bashir Usman Tofa wanda shine uban qungiyar da yake tallafa mata run daga farkon kafuwarta shine qashin bayanta da ya rungumeta ta kai inda take yanzu ko bayan rasuwarsa suma iyalansa sun xora akai suna kwatanta bada tallafinsu ga qungiyar.

Malam Bashir Muhammad Ingawa sakataren kwamitin na ilimi na qubgiyar tallawa marayu na Gandun Albasa da kewaye ya ce akwai sarkin Kano murabus Alhaji Muhammad Sunusi na Biyu da tsohon akanta janar na qasa da Alhaji Bala Borodo da sauran mutane da dama suna tallafawa qungiyar. Wanda da bazarsu suke rawa.

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria