Leadership Hausa

Yadda Sojoji Suka Yi Juyin Mulki A Gabon

-

Sojoji sun bayyana a gidan Talabijin na Qasar Gabon, inda suka bayyana cewa sun qwace mulki.

Sun ce sun soke zaven da aka yi na ranar Asabar da aka bayyana Shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaven.

Hukumar zave ta bayyana Mista Bongo a matsayin wanda ya lashe zave da kashi biyu cikin uku na quri’un da aka kaxa amma ‘yan adawa sun ce an tafka maguxi.

Wannan matakin ya kawo qarshen shekara 53 da aka shafe iyalan gidan Bongo na mulki a qasar Gabon.

Sojoji 12 sun bayyana a Talabijin inda suka sanar da soke zaven tare da rushe “duk cibiyoyin gwamnati”.

Xaya daga cikin sojojin ya sanar a gidan Talabijin na Gabon 24 cewa “Mun yanke shawarar tabbatar zaman lafiya da kuma kawo qarshen wannan gwamnatin.”

Mista Bongo ya hau kan mulki ne bayan rasuwar mahaifinsa a shekara ta 2009.

Wane ne Ali Bongo?

Wasu na kallonsa a matsayin sangartacc­en xa, wanda ke kallon mulkin qasar Gabon a matsayin haqqinsa na gado.

Ya tava zama mawaqi, inda daga baya ya gaji mahaifinsa a matsayin shugaban qasar, ya xora a kan shekara 50 da iyalansa suka kwashe suna mulkin qasar.

Wasu kuwa na yi masa kallon mai kawo sauyi, kuma sun ce talakawa ne suka zave shi bisa tsari na demokuraxi­yya.

Sai dai rashin lafiyar da ya yi fama da ita a shekarun baya sun haifar da tantama a qasar mai yawan al’umma sama da miliyan biyu.

A ranar 7 ga Janairun 2019 wasu gungun sojoji sun yi yunqurin yi masa juyin Mulki, lamarin da bai yi nasara ba.

Sojojin sun ce dalilin yunqurin nasu shi ne domin su mayar da mulkin demokuraxi­yya a qasar bayan zaven shekara ta 2016, inda Mista Bongo ya yi nasara da kyar duk da zarge-zargen cewa an tafka maguxi.

Gabon na xaya daga cikin manyan qasashen Afirka da ke samar da man fetur, inda kusan kashi 90 cikin 100 na qasar dazuka ne.

Idan juyin-mulkin ya tabbata, to za ta kasance qasar Afirka ta takwas, reinon Faransa da aka yi wa juyin-mulki a cikin shekaru uku da suka gabata.

Sai dai, sauran qasashen da suka fuskanci wannan yanayi a yankin Arewa su ke na Sahel inda mayaqan jihadi suka ba da kafar qorafi ko amfani da su wajen kifar da gwamnatin dimokuraxi­yya.

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria