Leadership Hausa

...Abubuwa 10 Da Suka Kamata A Sani Game Da Ƙasar

- Daga Sadiq Usman

Gabon, Kasa ce da ke Yammacin gabar tekun Afirka ta Tsakiya, sannan kasa ce da Allah ya albarkace ta da yalwar dazuka da kuma namun daji iri daban-daban, sannan suna da sadaukar da kai don ci gabansu.

Kazalika, Gabon kasa ce da ta ke da burin dorewa a matsayin kasa don samun ci gaba mai dorewa, da nufin kare albarkatun kasa tare da bunkasa tattalin arzikinta.

Har zuwa safiyar ranar Laraba, Gabon ta kasance karkashin mulkin Shugaba Bongo tun shekarar 1967.

Hambararre­n shugaba Ali Bongo Ondimba ya kasance dan marigayi Omar Bongo, wanda shi ne shugaban kasar Gabon na biyu daga shekarar 1967 har zuwa mutuwarsa a shekarar 2009.

Bayan mutuwar mahaifinsa, Ali Bongo ya lashe zaben shugaban kasar Gabon na 2009, inda ya zama shugaban kasar na uku.

An sake zabensa a shekarar 2016, a zabukan da aka yi mai cike da cece-kuce na rashin bin ka’ida, take hakkin dan Adam, da zanga-zangar bayan zabe da tashin hankali.

An kuma ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben 2023 na Gabon mai cike da cece-kuce. A ranar 30 ga watan Agusta, 2023 ne dakarun sojin Gabon suka yi juyin mulki na biyu a tarihin Gabon tun bayan samun ‘yancin kan kasar a shekarar 1960, inda suka yi juyin mulki na farko a shekarar 1964.

Abubuwa 10 na musamman game da Gabon: 1. Yalwar Dazuka: Gabon tana

alfahari da yawan dazuka a kasar, wanda hakan ke taimaka mata wajen bunkasa tattalin arzikinta.

2. Mayar Da Hankali Kan Ci Gaba: Qasar ta himmatu wajen

samar da ci gaba mai dorewa, ta hanyar kebe wani yanki mai yawa na kasart matsayin wuraren shakatawa kamar irin su Loango National Park, wanda ke ba da kariya ga namun daji da sauran wuraren shakatawa da ke bakin teku.

3. Al’adu: 5. Bambance-bambancen

Gabon kasa ce mai kabilu sama da 40, kowannensu yana da al’adunsa da harsuna daban-daban.

4. Manyan Namun Daji: Kasa mai tarin manyan namun daji kamar irin su giwaye, gwaggon biri, macizai da sauransu.

Wuraren Shakatawa:

Wannan ya kunshi muhimman wuraren shakatawa da masu yawon bude ido ke zuwa wanda yawanci dabobbi ke nishadanta­r da masu ziyara.

6. Kare Muhalli:

Gabon ta yi kaurin suna wajen kare muhalli ta hanyar bai wa tsirrai da hallitu kulawa ta musamman.

7. Yawon Bude Ido:

Kasar tana ba da dama don yawon shakatawa da bude ido, wanda baki ke ziyarta don ganin nau’ikan halittu na musamman.

8. Karacin Mutane:

rashin

yawan

Duba da al’ummar kasar,

Gabon tana kiyaye daidaito tsakanin ayyukan dan adam da yanayin kasar.

9. Masana’antar Mai:

Duk da kasancewar­ta kasa mai fitar da mai, Gabon ta dauki matakai don rage tasirin muhalli da saka hannun jari kan tsirrai.

10. Kasa Mai Cike Da Al’adun Gargajiya: Kasar na da tarin

al’adun gargajiya sannan ta samu ci gaban zamani ta hanyar samun abubuwan more rayuwa.

 ?? ??
 ?? ??

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria