Leadership Hausa

Luis Rubiales: Daga Murnar Lashe Kofin Duniya Zuwa Rasa Muƙami

- Tare da Abba Ibrahim Wada

Masu horar da tawagar qwallon qafa ta mata ta Sifaniya da suka je gasar cin kofin duniya sun yi murabus in ban da babban mai koyarwa, Jorge Vilda kuma hakan ya biyo bayan taqaddamar da ta vullo, bayan da shugaban hukumar qwallon qafar qasar, Luis Rubiales ya sunbanci 'yar wasa, Jenni Hermoso.

Tawagar mata ta Sifaniya ce ta ci Ingila 1-0 sannan ta lashe kofin duniya na mata a gasar da aka yi a qasashen Australia da New Zealand, wasan da aka fafata a cikin wannan watan.

Mataimakin kociyan tawagar, Montse Tome da Javier Lerga da Eugenio Gonzalo Martin da mai kula da lafiyar 'yan wasa, Blanca Romero Moraleda da mai horar da masu tsaron raga, Carlos Sanchez, duk sun bar aikin.

Haka kuma wasu da suka shafi tawagar ta mata ta Sifaniya da suka shafi shekaru daban-daban suma sun ajiye aikin kuma duk saboda zargin da ake yi wa shugaba Luis Rubiales. A satin da ya gabata ne hukumar qwallon qafar ta duniya ta dakatar da shugaban hukumar qwallon qafar Sifaniya, Rubiale, bayan da ya sumbanci Hermoso a leve, bayan cin kofin duniya.

A wani jawabi da kociyoyin suka fitar sun ce dukkan masu horar da tawagar Sifaniya ta mata sun yi tir da xabi'ar da shugaban hukumar qwallon qafar qasar ya nuna kuma suna fatali da halayyar tasa.

Mai koyarwa Luis de la Fuente, wanda ya yi wa shugaban tafi, bayan da ya ce ba zai sauka daga muqaminsa ba a ranar Juma'a, ya kuma caccaki Rubiales ranar Asabar xin da ta wuce.

Shi dai Rubiales bai yadda ya yi murabus ba kan lamarin, amma hukumar qwallon qafar Sifaniya ta ce za ta xauki mataki a kansa idan ta kammala binciken da ta fara akan lamarin.

Mahaifiyar Luis Rubiales Ta Fara Yajin Aikin Cin Abinci

Mahaifiyar shugaban hukumar qwallon ta Sifaniya, Luis Rubiales ta shiga yajin qin cin abinci saboda ceceku-ce da ake yi dangane da sumbar 'yar wasa da ya yi bayan da ake ci gaba da sukar Rubiales xin, mai shekaru 46 a duniya, bayan ya sumbaci 'yar wasan gaba Jenni Hermoso a leve, bayan wasan qarshe a gasar cin kofin duniya na mata a birnin Sydney.

Mahaifiyar­sa, Angeles Bejar, yanzu ta kulle kanta a wani coci a qauyen Motril sannan ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Sifaniya EFE cewa yajin qin cin abincin zai ci gaba ''dare da rana”.

Hermoso, mai shekaru 33, ta ce ba ta amince da sumbar da Rubiales ya yi mata a lokacin bikin gabatar da su a Sydney a ranar 20 ga Agusta ba sai dai Rubiales ya sha alwashin ba zai yi murabus ba amma hukumar qwallon qafa ta duniya Fifa ta dakatar da shi.

 ?? ??

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria