Leadership Hausa

An Raba Jadawalin Gasar Firimiyar Nijeriya

-

Hukumar da ke gudanar da gasar Firimiyar Nijeriya ta fitar da jadawalin wasannin kakar wasa ta bana ta 2023 zuwa 2024 inda a karon farko qungiyar qwallon qafa ta Kano Pillars za ta buga wasa tun bayan faxuwarta daga gasar a shekarar da ta gabata. An raba jadawalin wasannin bana a Babban Birnin Tarayya Abuja da za a fara gasa ta 53 ranar 9 ga watan Satumbar wannan shekarar ta 2023 kamar yadda aka tsara lokacin fitar da jadawalin.

Qungiyar qwallon qafa ta Enyimba ce mai riqe da kofin bara kuma na tara jimilla, wadda take fatan ta farko da za ta lashe babban gasar tamaula ta Nijeria karo na 10 a tarihin qasar nan.

Daman dai qungiyoyi 20 ne za su kece raini a bana da suka haxa da 16 da suka fafata a bara da kuma huxun da suka samu buga gurbin kakar wasan bana ta 2023 zuwa 2024.

Qungiyoyin da suka hauro gasar bana sun haxa da Heartland da Sporting Lagos, da Kano Pillars da kuma Katsina United kuma wannan shi ne karon farko da Sporting Lagos za ta fafata a gasar Firimiya ta Nijeria a tarihi. Qungiyoyi huxun da suka bar gasar bara sun haxa da Wikki Tourists da

Nasarawa United da El-Kanemi Warriors da kuma Dakkada da za su buga Nigeria National League.

Jadawalin wasannin farko na bana; Enyimba da Bendel Insurance. Heartland da Lobi Stars. Sunshine Stars da Kano Pillars.

Katsina United da Kwara United. Abia Warriors da Niger Tornadoes. Ranagers Internatio­nal da Doma United. Rivers United da Remo Stars. Bayelsa United da Akwa United. Sporting Lagos da Gombe United. Shooting Stars da Plateu United.

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria