Leadership Hausa

Zamfara: Shugabanni­nmu, Ku Yi Hankali Da ‘Yan Kanzagi

- Imam Murtadha Muhammad Gusau 0803828976­1

Da farko zan fara da gaisuwa kamar yadda muka saba, Assalamu alaikum wa rahmatulla­hi Ta’ala wa barakatuhu. Ya 'yan’uwana al’ummar Jihar Zamfara masu albarka (Zamfarawa), ya kamata mu san cewa, da Dauda Lawal da ya zama Gwamnan Jihar Zamfara da kuma Bello Muhammad Matawalle da ya zama Ministan Nijeriya, duk wannan daga Allah ne, a cikin su babu wanda ya ba wa kansa wannan matsayi.

Sannan a cikin nasu babu wanda wayonsa ko dabararsa ta ba shi wannan matsayi. Mun yi imani da Allah a matsayinmu na musulmi cewa, shi kaxai ne ke bayar da mulki da matsayi ga wanda ya so. Don haka, ya zama wajibi mu yi musu addu'a tare da fatan alhairi, Allah ya ba su sa'a da nasara, ya kuma sa a ce gwamma da aka yi. Allah kuma ya sa su zamar wa Jihar Zamfara alhairi da ma Nijeriya baki xaya tare da fitar da su kunya, duniya da ta lahira, amin.

Amma mutum ya koma gefe yana soke-soke da zage-zage da cin mutunci; ko ya kasance yana rubuce-rubucen banza a kafafen sada zumunta, ko shiga rediyo ko talabijin yana vavatun banza, don goyon bayan Gwamna ko Minista, to wallahi duk wannan babu inda zai kai mu, domin kuwa bai dace ba. Sannan a matsayinmu na musulmai, mu sani wannan haramun ne kai tsaye, haramun ne, haramun ne!

Duk mai kishin Jihar Zamfara da Nijeriya da gaske tare da son a samar da tsaro da ci gaba da kwanciyar hankali, to kamata ya yi ya dage da addu'a da roqon Allah (SWT), ya sa waxannan shugabanni su zama alhairi a gare mu baki-xaya.

Don haka, ina sake yin kira ga Zamfarawa da mu ji tsoron Allah, mu yi musu addu'a, mu kuma yi wa jiharmu da qasabaki-xaya addu'a.

Haka zalika, duk siyasar da muke yi, mu riqa tunawa cewa mu musulmi ne. Sannan shi musulmi, yana da dokoki da qa'idojin da suke yi masa jagoranci a cikin dukkanin rayuwarsa, ba haka kawai yake rayuwa sagaga ba. A tare da shi akwai Mala'iku masu rubuta dukkannin abin da ya aikata na alhairi ko sharri.

Sannan, su kuma waxannan shugabanni guda biyu, wato Gwamna Dauda Lawal da kuma Minista Muhammad Bello Matawalle, ina roqon su tare da yin kira da su ji tsoron Allah (SWT). Su kuma sani cewa, su jarabawa ce da Allah ya jarrabi Zamfarawa da su. Don haka, ya zama wajibi su haxa kai domin kawo wa Jihar Zamfara da Nijeriya bakixaya alhairi da ci gaban da zai amfani kowa da kowa.

Har wa yau, ka da su yarda da masu zuga da 'yan bani-na-iya, 'yan kanzagi da banbaxanci, waxanda su a koda-yaushe, faxan shugabanni da rigingimun­su sh ine hanyar cin abincinsu. Irin waxannan mutane wallahi babu wani alhairi a tare da su kwata-kwata illa sharri.

Gwamna Dauda Lawal da Minista Muhammad Bello Matawalle, ku sani cewa a matsayinku na jagororin Zamfarawa, Allah zai tashe ku a gabansa a filin alqiyama, domin yi muku hisabi a kan wannan jagoranci da ya xora muku. A wannan rana wallahi babu wani magoyin bayanku da zai iya fitar da ku, face ayukkanku na alhairi da kuka yi. Don haka, ka da ku tava yarda da zugar wani magoyin baya, wanda a wannan rana ta lahira shi ma ta kansa yake yi, kuma kuma kuna taku ta kan.

Wallahi qaunar da nake yi muku tsakanina da Allah da kuma kishina ga

Gwamna Lawal

jihata da kuma qasa baki-xaya ne yasa na yi wannan rubutu. Domin kuwa, ina kallon duk abin da ke faruwa a faxin wannan jiha tamu, wanda idan wannan lamari ya ci gaba a haka, ko shakka babu jiharmu da al'ummarmu ba za su ji daxi ba.

Ku manta da maganar banbancin jam'iyyar da ke tsakaninku, ku manta da banbancin siyasar da ke tsakaninku, ku ji tsoron mahaliccin­ku, ku kalli al'ummarku, ku yi qoqari ku haxa kai, domin tunkarar rashin tsaro da yunwa da talaucin da ke addabar Jiharmu ta Zamfara mai albarka.

Muhammad Bello Matawalle, a matsayin da Allah ya ba ka na Ministan Tsaro, ya zama tilas in dai har dai kana son tsira a gaban Allah, ka haxa kai da Gwamna Dauda Lawal, ku yi aiki tare, domin samar da kyakkyawar natija.

Haka nan, Gwamna Dauda Lawal, a matsayinka na Gwamnan Jihar Zamfara, wanda Allah ya damqa wa amanar tsaron Jihar Zamfara da ci gabanta, da zaman lafiyarta a hannunka, kai ma ya zama tilas in dai kana son tsira a gaban Allah, ka haxa kai da Minista Muhammad Bello Matawalle, ku yi aiki tare ba tare hangen wani banbaci na jam'iyya ko siyasa ba, domin kawo wa jihar da ma Najeriya baki-xaya ci gaba.

Wannan ita ce gaskiyar magana, wadda duk wani masoyinku na gaskiya zai faxa muku. Duk wanda zai gaya muku akasin haka kuma, miqiyunku ne. Miqiyinku wanda yake so ya jefa ku cikin rami, ya bar ku da jangwam a gaban Allah (SWT).

Bugu da qari, dukkanin manyan 'yan siyasarmu na Jihar Zamfara, su ma ya zamar musu wajibi su mayar da hankali wurin zamar wa jihar da qasa baki-xaya alhairi. Musamman kamar Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura, Tsohon Gwamna Sanata Abdul-Aziz Yari, Tsohon Sanata Marafa, Xan Majalisa Aminu Sani Jaji, Sanata Ikra Aliyu Bilbis, Sanata Sahabi Ya'u Kaura, Xan Majalisa Kabiru Amadu Mai Palace da sauran makamantan­su, ya zama wajibi a gare mu mu ji tsoron Allah, mu kuma zama alhairi ga jiharmu mai albarka.

Gaskiyar magana ita ce, dukkanin ku kuna da magoya baya da masoya, akwai ximbin jama'ar da suke bayanku, don haka wuqa da nama duk a hannunku suke. Idan kun gyara kun sani, idan kuma kuka vata nan ma kun sani.

Sannan duk wanda yayi da kyau, ya sani, Allah zai yaba haka nan kuma al'umma ma za su yaba. Duk kuma wanda ya vata, ya sani cewa zai jawo wa kansa fushin Allah, sannan kuma al'umma za su yi Allah wadai da shi.

Allah ya sa mu dace, ya ganar da mu gaskiya, amin.

 ?? ?? •Minista Matawalle
•Minista Matawalle

Newspapers in Hausa

Newspapers from Nigeria